30

155 20 0
                                    

🦎 *K'ADANGARUWA*🦎

  *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
  ( *Home of expert and perfect writers*)

       *NA:* *SLIMZY*✍🏻
      wattpad@slimzy33

*EID MUBARAK MASOYANA ALLAH YA MAIMAITA MANA*❤️🥰

                       *30*
Jikinsa ne ya kama rawa sosai saboda tsananin tsoronta da furgici Daya shigeshi ya daga Kai ya kalli girgije yadda yayi bakinkirin gabas da yamma kudu da arewa a tankamemem fili suke Wanda besan a duniyar da Suke ba tsoro ya cikasa ya daga Kai yayi tozali da ita Rabi mutum Rabi K'ADANGARUWA ya hadiyi wani miyau yace yau shine tsaye a gaban aljana?gumi ya sake lullubesa muryarta yaji a dashe wanan Karon ba kalar muryar da tayi masa magana dashi ba a farko tace "nasan tarihin Amina da yadda akayi na Zama uwarta yanzun Zan Baka abinda nasani daga ciki sanadin baffahta na kauye"shidai gaba Daya harshensa da hakoran bakinsa rawa yakeyi fatansa ya fita daga cikin wanan balain Daya tunkarosa....

Tace "kauyen Kura....wata Rana,....Yana cikin gonarsa yanata aiki sakamakon lokaci ne nadamuna lokaci ne da Suke noma a kauyen daga Kai yayi yaga har magriba ta rufa Dan alamun yadda gari yayi ma ya Nuna anyi sallah,ya dauki jakarsa ya rinkajin nishi da kuka sosai ya juya ko ina bega kowa ba sanan ya Kara tafiya ya sakejin abinda yaji yadan tsaya ya Kasa kunnensa Yana bin ko ina da kallo ta cikin Gona ya hangi inuwa wadda kamar ta mutum kamar bata mutum ba ya juya da sauri dikda yadan tsorata Amma mutanen kauye haka ya tsaya Yana kallon mace rungume da jaririya cikin jini yaji tsoro yace "mutum ko aljan?"matashiyar mace kyakkyawar gaske ya kalli suturar jikinta Sam batayi kama da cewar itadin yar kauyen bace jikinta ke tsananin rawa dakyar ta furta "mutumm....Dan Dan Allah Ka taimakeni"tana Fadi tana Mika masa jaririyar hannunta data soma tsala ihu yace "baiwar Allah kince ke mutum ce meyasa kike mikamun jaririyar hannunki?"ta girgiza Kai tace "Ka tallafi jaririyar nan Ka kulamun da ita nidin tawa ta kare domin faraurar rayuwata akeyi"jikin baffa yayi sanyi ya tsaya Yana kallonta cikin rashin fahimta tace "ehh Ka karbeta ita idan ta girma Allah zai kwatar Mata hakkinta domin an kashe mahaifinta yanzun haka farautar rayuwata akeyi Saboda mijina Mai Tarin dukiya ne gudowa nayi nasamu mafaka a nan sun rigada sun kwace Komi a hannuna Dan Allah Ka karbeta suna cikin gonar nan suna nemana"yasa hannu ya karbi Amina itama yace "kizo muje gidana ki fadamun tarihinki ni Zan rikeki Zan taimakeki"jini ne ya balle Mata ta Fadi Kasa hakoranta suka Fara Karo da juna nan da nan ta sankame dafara ta Fara fitowa daga bakinta ganin haka yasa yaji tsoro ya tsugunna a gabanta cikin minti uku tace GA garinku nan,take jaririyar ta Fara tsala ihu haka yake kallon mahaifiyarta Yana kuka....Yana tafe Yana waige gashi Yana jiyo motsi ya tsorata ya boye a jikin bishiyar da muke rayuwa.....nan na fado a Kan jikinta Wanda dik abinda ya faru a gabana akayi tausayinta ya kamani dikda Niba biladama bace yasa hannu ya cireni ya yarfar Dani gefe ya boye a bayan bishiyar,

Wadanda suka biyota ne suna ganinta haka farin ciki ya lullubesu Daya daga ciki yace"shikenan ya hutar Dani shikenan ta mutu dukiya ta dawo hannuna kamar yadda nake muradi sanan ina kyautata zaton ta haihu karnukan farauta sun cinye abinda ke cikinta"dik baffanta na rungume da ita ikon Allah ta tsagaita da kukan gari yayi duhu haka ya shigo kauye cikin sauri ya Shiga gida Yana isa innah ta tarbesa ganinsa da jaririya cikin jini ta kidime tace "daga ina Malam?nasan halinka nasan waye Kai"ya jinjina Mata Kai ya bata labarin Komi tausayin Amina ya kamata tasa hannu ta karbi jaririyar sanan tace "Ka koma tunda gari yayi duhu Ka nemi yakubu Ku dauko gawar baiwar Allah nan batare da kowa ya ganku ba da safe sai ayi Mata Sutura a birneta in yaso ni kuma zance yar uwata ce ta kawomin ziyara ta haihu ta rasu a hannuna"ajiyar zuciya ya saukw yace"Allah yayi Miki albarka"ya juya da sauri ta Karbi jaririyar ina makale a jikin bango ta juya taga giftawar Abu tace "nikam wace irin K'ADANGARUWA ce daddare kamar ba mutum ba kadangaru sun shige makwancinsu"ta dau takalmi ta jefeni na bace bata Lura da hakan ba ta hada wuta tasa ruwa nan da nan tayiwa Amina wanka ana haka saiga baffa ya dawo runngume da gawar mahaifiyar Amina ya shimfide ta dukkansu suka fashe da kuka yadda sukaga Rana haka sukaga dare da safe yaje gidan Mai gari kamar yadda matarsa tabada shawara haka akayi babu Wanda yayi zargin Komi akai Sutura a sunan kanwar matarsa ce aka birneta akaita zuwa gaisuwa da masu kawo kayan jinjira gudun mawa.....

Cikin ikon Allah bayan sati biyu da haihuwar Amina tayi bulbul jinjira baffa Yana matukar Sonta dik Inda zashi zai rungumeta yaje da ita ciki kuwa harda Gona sanan haka yake tattara Dan abinda ya Tara ya Siya mata madara wata Rana yazo da Amina yanata kalle kalle Inda zai ajiyeta ya hangi katuwar bishiyar dalbejiya da sanyin inuwa wajen yasan koda yaushe bishiyar akwai inuwa ya shimfida tabarmar da yazo da ita ya shimfide ta wajen Yana Mata waka Yana kokarin Fara aikin Gona Amina yarinya ce jinjira Mai hakuri Yana ajiyeta nake saukowa daga Saman bishiya in rikida in koma karamar yarinya Rabi mutum yabi K'ADANGARUWA inyita Mata Wasa Yana cikin Gona Yana aiki idan tayi kuka bayaji haka Zan daukar kofin ruwa da madararta in bata inyita shafa Mata fuska da wadanan hannuwan nawa.....ta daga hannuwanta zako zako yatsunta Zara Zara irin na kadangaru da kumbuna,haka zanyita Wasa da ita inyita renomta har daukarta nakeyi mubar wajen da naji alamar zai dawo in Maza in bayyana a wajen in ajiye masa ita ranan haka ya dauketa yayi gida da ita haka Zanbi bayansu dik Inda sukayi har mu isa gidan tare saboda tsananin kaunar Amina da nakeyi....

Ana kiraye kirayen magriba baffa ya Shiga gida rungume da Amina Nima nashiga gidan innah ta girgiza Kai tace "kana tafe da Amina ga kuma K'ADANGARUWA jangwalagwada na biye daku nibansan wanan K'ADANGARUWAR daga inaba baffa yayi dariya yace "ba tare mike ba bangon gidan nan inkin Lura kadangaru naso"....Innah tace "nidai Malam kadaina fita da yarinyar nan Gona na tabbatar indai ba ajiyeta kakeba to yaya kake aikin gonar?"nan ya fada Mata yadda yakeyi da ita tace "banaso Ka Kara tafiya da ita"ta nufi daki da ita ta shimfide tayi bacci nan naji innah nakokarin rabani da Amina wadda na shaku da ita nakejin nice uwarta a wata duniyar ta daban hakan yasa na shige dakin innah cikin Kaya daddare suna bacci na dauki Amina na hura Mata koriyar iskar dake bakina ta rinka Shiga jikinta nan da nan ta bude idanuwa idonta suka koma green nayi murmushi nasan na rigada na maidata kalata nasan bazamu taba rabuwa ba......ta dubi abbah tace "Kai a tunaninka Raba d'a da mahaifi abune Mai sauki"gaba Daya abbah ya jike da gumi.....kallonta yakeyi take yaji wani Abu game da Amina ya shigesa tayi juyi iska GA guguwa ta taso tana kokarin lullubesa tace "bangama maka tarihin Amina ba".....ya hadiye miyau a wanan lokacin besan karfe nawa bane gashi yasani yanzun ummahnsa na can tana bulayin nemansa burinsa be wuce ya Bude Ido ya gansa a gida cikin mutane Yan uwansa ba gashi tsudum a duniyar aljanu.......

*******
Karfe dayan dare ummah a gigice take tanata Kiran layin abbah Baya Shiga nan da nan ta tada hankalin mutanen dake cikin gidan Suna zaune cirko cirko Amina ta fito daga dakinta ta jike sharkaf da gumi dik abinda ke faruwa da abbah tanaji daga Inda take kunnuwanta a Bude suke dik yadda taso ta isa wajen ta Kasa sakamakon karfinta be Kai hakan ba,

Idonta cike da kwalla ta tsaya ji takeyi kamar ta sanarwa da ummah abinda ke faruwa saidai dukkansu bazasu yarda ba saboda hankali bazai dauka ba haka ta juya ta nufi dakinta ta mike hannuwanta suka rikide ta daga hannunta Sama ta bude ta gagara ta Fadi Kasa sakamakon iskanta be Kai ta isa wajen ba sanan tunda take da ita bata taba zuwa duniyar aljanu ba hawaye ya wanke Mata Ido ya zaayi dani a sanar musu cewar abbah Yana wata duniyar ta daban a sanadinta?......

Guguwa ce ta tsaya dik ya galabaita ta dubesa tana Kada katon bindinta tace "akwai abubuwan al'ajabi a rayuwar Amina gashi na dauko maka ba tarihinta turyan turyan kanaso muncigaba ko inbarka?"tana yawo cikin iska tana zagayesa ya dake yace "inaso insan sauran labarinta "ta daga Kai ta kalli Sama ta juyo tasa hannu ta bude yatsunta nan da nan haske ya karade wajen tamkar Rana tace mu cigaba......

*SLIMZY*✍🏻

K'ADANGARUWAWhere stories live. Discover now