5

964 10 0
                                    

*_Typing📲_*



         *_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
                  _{Gara rana dake}_


           *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

________________
*_Episode 5_*

..........Bada son ran ɗan-azumi ba aka kwashi Raudha zuwa asibiti. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso, inda aka amshi Raudha dake a jigace har batasan inama kanta yake ba zuwa yanzun. Ko sisi Fatima bata da shi, tayi ƙarya ne kawai dan Abbansu ya bari a kawo Raudha asibiti. Tana ganin an amshi Raudha ɗin ta fito ta nufi ofishin Doctor Rufa'i, sai dai anyi rashin sa'a wai baya nan yamaje Ɗillo tun jiya. Dawowa tai inda Mommy da Abban ke tsaye a ƙofar ɗakin da aka shiga da Raudha ɗin. Zama tai itama tabi ayarin ƴan tagumi, a haka har doctor ɗin ya fito yana mai kwantar musu da hankali akan karsu damu komai zai dai-daita, dan zai rubuta musu wasu allurai da zasu sayo, da zaran anma Raudha ɗin inssa ALLAH zata samu nutsuwa. Cikin gamsuwa da rashin damuwa aljihunsa zaiyi tsuwwa ya miƙe yabi doctor ɗin, har yaje ya dawo mommy da Fatisa da Fatima bakinsu bai saɓa ba. Sai da ya dawo da takardar ya mikama Fatisa ɗinne ta ce, “Abba ya zaka bani kuma? Ba cayay a sayo ba?”.
        Wani shegen kallo ya watsa mata ita da Fatima fuska a ƙwaɓe. “Kunci bu*a'ubaku, ƴan bu*a'uban yara da basa ko ganin mutuncina. Ni kikema magana haka kamar kina a gaban tsohon kwarto”.
      Fuska Fatisa ta ƙwaɓe tana ƙunƙuni, zai sake magana Asabe ta katsesu.
       “Wai nikam maganin zaku sayo a cetomin yarinya ko tazubar ɗinne ya motsa muku a bainar nasi?. Kai kullum bazaka ja girmanka ga yaran nan ba balle tauna harshenka da baiko da linzami wajen sakin magana”.
        “Kar yayi linzamin mana. Banda shegantaka irin tata ba itace tace tanada kuɗi ba shine zata wani tsareni da idanu na rashin ta'ido. ai sai da nace ku bata ɗan libiya amma tace tanada kuɗi ko......”
      “Ni dai ya isa da ALLAH. Ke Fatisa anshi kije ki sayo”.
    “Mommy nifa wlhy banda ko sisi anan. Nace inada sune danya yarda akawota asibiti. Dan haka sai yaje ya nemo inma baida su, dansu dai likitocin nan bawai batun lamuni suka sani b.....”
    Hannu yakai zai kwaɗa mata mari ta tashi ta fita a guje Fatima na take mata baya. Babu ko kunya ya rufa musu baya shima duk da kuwa tsufa ta fara kamashi, ga sigari duk ta gama cinyesa a tsayee....
       “Subahanalillahi! Malam ɗan-azumi lafiya kuwa?”.    
     Cak yaja ya tsaya yana huci saboda jin an ambaci sunansa. Sai kuma duk ya diririce ganin Falalu mai shago tare da Alhaji Maude Dallatu, ya ɗan tura hularsa baya yana ƙaƙaro murmushi. “A'a Falalu kune anan? Ince dai lafiya ko?”.
        “Ai kai ya kamata mu tambaya ko lafiya kuwa baba?”.
    Cewar Alhaji Maude duk da kuwa zai iya girmar ɗan-azumin ko suyi sa'anni.
            Fuska ya marairaice kamar zaiyi kuka, saboda hangen damar dake garesa ta ƙarshe da mafita kenan. “Alhaji wlhy Raudha ce babu lafiya muka kawo asibiti. Shine waccan ja'irar na bata ta sayo magani take shirin min ƙyuya irin nasu na yaran zamani”.
       Fatisa tai saurin waro ido waje suna kallon juna ita da Fatima da gumtse bakunan su jin dariya nason kufce musu.
     “Ai sai dai haƙuri baba. Inga takardar”.
      Alhaji Maude ya sake faɗa a ladabce yana miƙa hannu ya amshi takardar hannun Abban. Kamar bazai bashi ba dai yana ɗan nannoƙewa sai kuma ya miƙa masa. Koda Alhaji Maude ya amsa bai wani tsaya dubawa ba ya kalli Falalu dake ɗauke da kaya niƙi-niƙi alamar duba wani mara lafiyan sukazo ko makamancin hakan. “Falalu ƙarasa ciki ina zuwa”.
      “To ranka ya daɗe, amma daka kawo ni sai naje zai fi”.
      “No karka damu jeka ciki kawai zanzo yanzun”.
      “To a shigo lafiya”.
Falalu ya faɗa cikin girmamawa yana ɗan murmushi.
       “Baba ka jirani nan kaima ina zuwa”. Alhaji Maude ya sake faɗa yana tafiya da kallon mal. Ɗan-azumi. Kafinma yace masa wani abu har yayi nisa. Hannu ɗan-azumi ya ɗaga sama yana godema ALLAH daya kawo masa Alhaji Maude a lokacin daya dace, sai dai a ransa kuma ya ƙudira dolene kuɗin da duk zai biya na maganin sai Fatisa tayi kashinsu. Yana nan tsaye ko mintuna goma ba'aiba sai ga Alhaji ya dawo, da taimakon sa sukaje inda aka kwantar da Raudha ɗin. Babu ɓata lokaci doctor ya amsa dan dama su kawai yake jira.

BAƘAR INUWA....!!Where stories live. Discover now