Part 2

5 2 0
                                    

JANNATUL FIRDAUS 🦚🦚🦚

Story and written by
Mss Fah tee mah Yousrah Wali
Wattpad @TeerahWali
Facebook @Fah tee mah wali
Instagram @Yusrah_wali

🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin k'ungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishadantar da masoyana.🤙🏽'''
____________________________

This book is entirely a work of fiction, any duplicate/resemblance of character or lifestyle should please be considered as a coincidence 🙂.

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai...
Ina mai roqon Allah ya bani ikon fara littafin nan a sa'a, ya kiyaye hannuna da rubuta haram. Allah ya azurta ni da rubutu mai ma'ana.

Wannan littafin kyauta ne wato book 1, book 2 zai zama na kudi in sha Allahu. Ina fatan labarin ya qayatar daku sannan kuma ku dauki darasi aciki. Ga mai buqatar siyan book 2 tun yanxu zai iya turo katin #200000800 ta wannan layin
09034275112 MTN sai a turo shaidar biya ta wannan layin 08107129242.

Ga mai buqatar tuntuba ta via WhatsApp sai yayi min magana ta wannan number 08107129242. Ga masu transfer ta account zasu turo ta wannan number 2281365157 UBA
Fatima Kabir Wali.
Akwai opay ga mai bukata
8107129242 Fatima Kabir Wali.

Part one : Page 2

Kwance take tana tunane tunane wanda ita ma kanta bata san abinda take tunanin ba, tayi nisa sosai sai taji ƙarar ringing din wayarta, firgigit ta dawo hayyacinta tana kallon wayar. Sai dai kafin ta ɗauki wayar ma kiran ya katse, idanunta ne suka sauka akan lokaci, 12:57 am. Toh waye wannan ? Wani kiran ne ya qara shigowa, wayar ta qurawa idanu tana kallo da mamaki fal a fuskar ta ganin Anty Surayya ce take kiranta a wayar.
Ta daure ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnenta bata ce komai ba, muryar Anty Surayya taji tace
"Hello Baby kina ji na kuwa?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Eh Anty ina jinki, lafiya?"

Tana jiyo numfashin da Anty Surayya ta sauke sannan tace "Na kasa barci Baby, ina cikin matsala wallahi wadda take son gurguɗa aurena , pls ki taimaka gobe kizo gidana."

Shiru Jannah tayi na dan wani lokaci har taji Anty Surayya tana fadin "Hello are you online Jannah?"

Ajiye zuciya ta sauke tace " Yea ina jinki Anty Surayya, zanzo amma ba gidanki ba sai dai ki fito mu hadu a wani waje."

"Meyasa toh? Gidan nawa ne bazaki zo ba? Please help me Baby kinga ko Riya ban fadawa ba saboda nasan kin fita hankali."

Girgiza kai tayi kamar Antyn na kallonta tace "I'm so sorry Anty amma I can't come to ur house, nayi wa kaina promise shiyasa."

Ajiyar zuciya Antyn ta sauke tace "Shikenan kizo mu hadu a clinic dina by 10:00am."

Da haka sukayi sallama ta kwanta tana ta tunanin abinda har zai sa aurenta yayi rawa, ita dai tasan Idrissa yana son Antynta tun ranar da ya ganta. Tasan bazai taba yarda ya sake ta kawai sati daya dayin aure ba. Da wannan tunanin barci ya dauke ta.

9:30am sharp ta fito daga dakinta ta nufi dakin Mami, a zaune ta ganta a gefen gadonta tana dudduba wasu takardu, tsuguna wa tayi ta gaishe ta sannan tace mata Anty Surayya tana nemanta ynx zata je. Mami tayi mata Allah ya kiyaye hanya ta fice daga gidan, lokacin data qarasa clinic din goma da minti sha biyar sakamakon cinkoson ababen hawa kasancewar safiya ce.

Direct office ɗinta ta wuce, tayi knocking kafin ta sauke hannunta Anty Surayya ta bude mata, saurin jawo ta ciki tayi ta rufe qofar, kallonta kawai Jannah keyi ganin yanda take abubuwa strangely. Zaunar da ita Anty tayi ta riqe hannunta gam a cikin nata sai kuma hawaye ya zubo mata, sosai Jannah ta rude saboda tasan ba abu mai sauki bane yake saka Anty Surry tayi kuka daga dukkan alamu wannan ya wuce yanda take zato. Gabanta na faduwa tace
"Anty lafiya kike kuka? Wai menene ya faru haka naga duk kin rasa sukuni? Don Allah Anty ki fada min duk kin saka hankalina ya tashi."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 17, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

JANNATUL FIRDAUSWhere stories live. Discover now