Part One

11 2 0
                                    

JANNATUL FIRDAUS 🦚🦚🦚

Story and written by
Mss Fah tee mah Yousrah Wali
Wattpad @TeerahWali
Facebook @Fah tee mah wali
Instagram @Yusrah_wali

🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin k'ungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma nishadantar da masoyana.🤙🏽'''
____________________________

This book is entirely a work of fiction, any duplicate/resemblance of character or lifestyle should please be considered as a coincidence 🙂.

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai...
Ina mai roqon Allah ya bani ikon fara littafin nan a sa'a, ya kiyaye hannuna da rubuta haram. Allah ya azurta ni da rubutu mai ma'ana.

Wannan littafin kyauta ne wato book 1, book 2 zai zama na kudi in sha Allahu. Ina fatan labarin ya qayatar daku sannan kuma ku dauki darasi aciki. Ga mai buqatar siyan book 2 tun yanxu zai iya turo katin #200 ta wannan layin
09034275112 sai a turo shaidar biya ta wannan layin 08107129242.

Ga mai buqatar tuntuba ta via WhatsApp sai yayi min magana ta wannan number 08107129242. Ga masu transfer ta account zasu turo ta wannan number 2281365157 UBA
Fatima Kabir Wali.

Akwai Opay ga masu buqatar turawa tanan
8107129242 Fatima Kabir Wali.

Part one
Page 1

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM .....

Idanu ta qurawa invitation card din dake hannunta tana jin quna sosai a zuciyarta, hawaye ne kawai ke zuba a fuskarta wani na bin wani. Tuna cewa Idrissa baya sonta shine yafi komai yi mata ciwo, burin da taci na zuwan bakinta da Idrissa ya rushe tunda gashi yaune ake daurin aurensu da Anty Surayya. Sai da tayi kuka sosai har taji kanta na mata ciwo sannan tayi shiru, dama kullum haka takeyi tunda tasan da zancen auren.

Motsin bude qofa taji hakan yasa ta saurin boye IV din tana rufe ido kamar mai barci, Amaryar ce da kanta ta shigo tana murmushi tana fadin
"Toh ai gani nazo davkaina yanxu tunda kinqi fitowa kina jira nazo."

Shiru taji hakan yasa ta qaraso ciki sosai, kallo daya tayi mata ta fahimci ba barci take ba don ta santa sarai fiye da kowa ma a gidan, hakan yasa ta qarasa ta zauna kusa da ita tana fadin

"Ba barci kike ba.?"

Yanayin yanda tayi maganar kamar tayi tambaya kamar kuma tana tabbatarwa, tashi zaune kawai tayi tana qoqarin kautar da idanunta ga barin kallon Antyn nata. Duk da hakan ta fahimci tana cikin wani hali duk da rashin wadatar haske a dakin kasancewar ma'abociyar zaman dakin bata cika son haske ba. Cikin sanyin murya tace

"Jannah! Meya sakaki kuka haka fuskarki ta kumbura?"

Shiru tayi kawai bata ce komai ba don ta fahimci duk abinda zatayi bazata gujewa Antyn nata ba, hannu tasa ta dafa kafadar ta tace

"Jannah tell me... Meyake faruwa? Meya same ki? Meyasa ki kuka?"

Jijjiga kai tayi tana jin hawayen na qara tsinke mata don ta kasa riqe su kuma tunda taga lokacin daurin auren baifi mintuna goma sha biyar ba yanxu, cikin rawar murya ta fara magana

"Yanxu Anty murna kike ma zaki tafi ki bar Babynki? Kinsan tun yaushe na fara kukan kewarki? Amma kinganki nishadin ki kawai kike?"

Shiru kawai Anty tayi tana kallonta kafin itama yanayin fuskarta ya canza tace

"Ba haka bane Baby ba haka bane wallahi, tun daga ranar da na tabbatar auren nan akwai shi na fara kewarku, wani abin saboda jama'a kake sakewa ka nuna komai ba komai bane. Don Allah ki daina kuka kar nima ki saka ni kukan, haba mana Babyn Antynta."

JANNATUL FIRDAUSWhere stories live. Discover now