*Z E E Y A D*
'''(The Abandoned Prince)'''*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD**MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*Note:*
_Banyi alƙawarin Posting kullum ba😁, sannan kuma labari na ƙagagge, ne banyi shi dan cin zarafin wani koh wata ba, kowa dai yasan da cewa ɗan Adam ajizi ne, dan haka duk wani kuskure da aka samu cikin labarin nan toh a bisa rashin sani ne, ba zan kar6i cin mutunci koh wasu ƙananun maganganu ba, MHIZZ JIDDHERR batada abokin faɗa, kowa nawa ne, dan haka idan kin zage ni koh a 6oye ne na yafe miki😁__Bismillahi_Rahmanin_Rahim_
_*YAA WAHHABU,KAMAR YADDA NA FARA WANNAN LITTAFI LAFIYA,KASA NAGA ƘARSHEN SA LAFIYA BA TARE DA AN SAMU WATA MATSALA BA,Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum🤲🏽*_
*001...*
*Cairo [Egypt]*
..............."My life my rules, nobody has the audacity to interfere in my life, and nobody has the gut to decide what is good or better for me...this is my life so let me live it the way i want it, Your highness ni ba yaro bane why then duk abinda zanyi sai wani ne zai yanke hukuncin hakan,why ba za'a barni nayi rayuwa ta cike da ƴanci ba kamar yadda akasan kowane cikakken ɗan sarki mai ragamar mulki a ƙasa ba?, am tired, am fed up with all this shit, so let me be, i need freedom...so freed me from all this...Please" ya ƙarashe cikin cize haƙora yana kallon farin dattijon dake kishingiɗe kan kujerar alfarma inda fuskar sa ke fitar da tsantsar 6acin rai.
A fusace ya juya ya fara tafiya, daidai isowar sa bakin ƙofa ya tsinkayo muryar dattijon nan.
"ZEEYAD!" ya ƙira shi cikin kakkausar murya.
Runtse idanu yayi yana dakatawa ba tare da ya juyo ba.
Miƙewa dattijon nan yayi daga kan Kujerar sa yayin da fadawan da suka zagaye shi suka shiga gyara masa doguwar alkyabar dake jikin sa.
"How dare you hun?, babu wani mahaluƙi da ya ta6a karya koh ƙetare dokar da na gindaya a wannan masarautar, yau kai ɗan da na haifa baka isa ka karya min doka kuma na kyaleka ba, dan kana gudan jini na ba hakan na nufin zakayi dukkanin abinda kaga dama kuma na barka ba, dole ne kabi doka kamar yadda kowane mahaluƙi keyi a masarautar nan, idan kuwa ba haka ba lallai zaka fuskanci hukunci mai tsanani."
A fusace ya juyo yana fuskantar Uban nasa yace "I know it,I know you will never change,your mind has already been poisoned, but sooner or later zaka gane cewa what you're doing is totally wrong Father, am your Son your own flesh and blood, but you never gave me a Fathers love..."
"ZEEYAD!, Enough of this Nonsense...."
"You better keep your mouth shut,save your words it maybe useful for you next time, this is between me and my Father, so you better not interfere in it, understand?" ya faɗa cikin katse ta yana aika mata da mugun kallo.
"ZEEYAD!" ya Faɗa yana mai wanke sa da wani irin zazzafan mari.
"Ashe bakada kunƴa har haka bansaniba?, a matsayin uwa take a wurin ka."
"Ba uwata bace, Mahaifiya ta ta daɗe da mutuwa kowa yasan da hakan,wannan matar ba mahaifiya ta bace, this selfish and disgusting woman here is nothing but a mess to our Family" ya faɗa yana nuna ta da yatsa,inda kuma idanun sa suke daɗa canza launi zuwa jaa.
"ZEEYAD!" ya faɗa a zafafe yana sake ɗaukesa da wani marin.
Hannun mahaifin nasa ya ruƙo kafin ya shiga dukan kansa dashi yana faɗin "Beat me, beat me as hard as you can, you enjoyed it right, you enjoyed beating your Only lovely son don't you, ka tsane ni koh, then why don't you just kill me Dad?."
Sosai ran Mahaifin nasa yayi mugun 6aci,wanda kallo ɗaya zakayi masa ka firgice tsabar zallar kwarjini dama kuma jinin sarautar dake yawo a jijiyoyin jikin sa.
Wani marin ya sake ɗauke ɗan nasa dashi kafin yace "Kuje ku ɗauke sa,sannan ku tabbatar da kunyi masa hukunci mai tsanani wanda koh da kuɗi aka basa nangaba ba zai sake sha'awar aikata abinda yayi ba yanzun" ya ƙarashe faɗa yana kauda kansa daga kallon da ɗan nasa keyi masa.
Da umarnin Sarki suka ƙaraso wurin tare da kamasa sukayi waje dashi,ba tare da yayi gardama ba yabi su,kasancewar hakan ya rigada ya zame masa jiki.
Kallon Juna itada ɗan saurayin dake kusada ita sukayi kafin duk su saki wani irin murmushi mai cikeda zallar ma'anoni iri-iri.
Wani irin ɗaki da ya kasance kamar Kurkutu aka jefa sa kafin a garƙame kwaɗo a ƙofar sukayi gaba suka barsa.
Bakin ƙofar ya matso yana kama ƙarafunan ƙofar, kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci irin tsantsar 6acin ran dayake ciki.
Kansa ya ɗaga sama yana kallon yadda hadari ya haɗu wanda ƙiris take ruwa ya sauƙo.
Sam bai damu ba,sai ma samun ƴar ƙarfen gadon dake ajiye a ɗakin da yayi ya kwanta fuskar sa na fuskantar sama.
Sama da shekaru goma na cikin rayuwar sa yana tafiyar da ita ne cike da ƙunci da wahala tun bayan mutuwar mahaifiyar sa,inda ya kasance bashida kowa face mahaifin nasa wanda yake tunanin zai zame masa gatan sa,sai dai kash! akasin hakan ta kasance wanda tun bayan mutuwar mahaifiyar tasa ya rasa gane kan mahaifin nasa kwata-kwata,balle ma dayake ƙarƙashin kishiyoyin uwa har uku wanda tunda ya taso bai ta6a samun wata kulawa ta musamman daga gare su ba sa6anin ƴaƴan cikin su da suka haifa.
ZEEYAD,matashin yaro mai kwazo da kaifin basira,Dukda mulki da ƙarfin iko irinta mahaifin sa hakan bai sanƴa shi fita daga cikin ƙangin rayuwa mai cike da ƙunci da rashin ƴanci ba.
A kaf cikin yara Shida da mahaifin sa ya mallaka babu marar gata kamar sa,Makaranta mai tsada,Tsadaddun sutura irinta ƴaƴan manƴan sarakuna,tsantsar ƙauna daga wurin mahaifa,rayuwa mai cike da jindaɗi da ababen more rayuwa iri daban-daban kowane yaro dama kuma ƴaƴan ruƙon gidan sun mallake sa sa6anin shi da koh almajirin cikin gida ya fisa gata.
ZEEYAD yaro ne mai ƙoƙari sosai dukda kasancewar yana cikin ɗaya daga cikin makarantu masu sauƙin kuɗi a ƙasar hakan bai sanƴa guiwar sa ta sace ya kasa yin abinda zai fice shi a rayuwa ba.
Dukda cewa dukkanin yaran gidan ba a ƙasar suke karatu ba hakan bai sanƴa shi jin baƙin cikin da zai hana sa cigaba ba,burin sa shine ya samu ya jona makarantar gaba tunda ya kammala karatun secondary ɗinsa,ya jona Jami'a kasancewar sa na son zama hamshaƙin ɗan kasuwar da duniya keji dasu.
ZEEYAD yaro ne mai tarin baiwa,6oyayyiyar baiwar da babu wani mahaluƙi da yasan sa dashi.
Dukda kasancewar sa ɗa namiji babba a wurin mahaifin nasa hakan bai hana sa nuna masa *TSANTSAR ƘIYAYYA* da warayya a tsakanin sauran ƴaƴan nasa ba.
Koh dan ya kasance mai rauni ne a cikin su wanda ba komai bane ya dame sa,bai kuma damu da shiga harkar da bata shafe sa ba yasa hakan ke faruwa dashi kokuwa tsantsar son zuciya ce kawai dama kuma makirci irin ta kishiyoyin mahaifiyar sa yasa hakan ke faruwa dashi.
Ya taso ne a rayuwa ba tare da yasan mecece soyayya ba sai akasin ta wato tsantsar ƙiyayya.
Tun bayan mutuwar mahaifiyar sa bai sake dariyar farin ciki ba,yau shekaru goma kenan,laifi kaɗan ne zaiyiwa mahaifin sa ya sanƴa a hukunta shi,hukunci mai tsanani,wanda koh a cikin bayi sai wanda ya aikata babban laifi akeyiwa hakan.
Dayawa daga cikin bayi sun fisa gata,wanda hakan yawancin su ke ɗaukar alhaƙin hakan wurin yi masa dukkanin abinda suka so domin kuwa dasu dashi ɗin babu wani bambamci tsakanin su,kamar yadda suke faɗa.
A yau yanada shekaru Ashirin a duniya sai dai koh da da wasa bai baryin addu'a wurin neman taimako daga wurin wanda ya dace kuma maji roƙon bayin sa ba.
Da akwai lokacin da ya gindaya wa kansa na zama cikin wannan ƙunci da wahalar da zaran lokacin nan ta cika kuwa,tabbas ba zai saurarawa koma waye ba,kama daga kan Mahaifin nasa dama kowa dake cikin Masarautar nan,amma kafin burin sa ya cika dole ne ya samu damar tseratar da rayuwar sa daga wannan kangin wuyar da yake ciki,ta haka ne kaɗai burin sa dama kuma mafarkin sa zai zamto gaskiya,da zaran kuma hakan ta faruwa toh tabbas kowa zaiji *A JIKIN SA..............*
*Share Fisabillah👏🏽*
*MHIZZ JIDDHERR........✍🏽*
YOU ARE READING
ZEEYAD
Historical Fiction*Z E E Y A D!!!* '''(The Abandoned Prince)''' *Ever heard of an Abandoned Prince, a Prince who has been abandoned by his own legitimate Father, a Prince that has been treated like a piece of a rotten fruit in his own Kingdom, a Prince who is being t...