Sanadin
Labarina
Free Page ( 3)©®Hafsat Rano
***
***Kiran farko akan kunnen ta, saboda yadda jikinta ya saba da tashin wuri, dan tun bata iya tashi ba har ya zame mata jiki, ko bata ji kira ba zata mike, wataran ko sallah Lami bata barin ta tayi zata fara sakata aiki, itace dauko itace, itace debo ruwa da sharar gidan baki daya dan duk sai tayi su kafin ta tafi makaranta wadda take da yar tafiya tsakanin su, haka ta saba ta goge tun shekarun ta basu kai haka ba, babu wani aiki da yake bata wahala sai dai idan ba sunan sa aiki ba. Zama tayi jugum tana kallon yanayin dakin, ta kalli Usman da yake bacci a gefenta, tana matukar son yara, haka take ko a gida bata da aiki sai jajibo yaran makota kafin Lami ta hanata. Turo kofar akayi, Anty ta shigo sanye da Hijabi, ganin ta a zaune ya bata maki
"Har kin tashi Jiddah?" Tace tana karasowa cikin dakin
"Tun dazu na tashi."
"Toh maza tashi kije kiyi alwala muyi sallah, Usman be yi kuka ba ko?"
"A ah be yi ba."
"Toh yi alwalar maza kizo muyi sallah."
"Toh." Tace ta sakko, taje tayo alwala suka fara yin raka'atanil fajr sannan sukayi subh. Al'kurani ta dauko suka fara daga Falak da Nasi, zuwa in da Jiddan ta tsaya a karatun, ta yaba sosai da yadda take karatun dan batayi tunanin hakan ba duk da baffa ba daga nan ba wajen riko da addini. Suna zaune tare har garin yayi sha, tace mata ta koma ta kwanta, ita kuma ta fita zuwa shashen Baban dan tasan zuwa lokacin ya dawo daga masallaci. Tana fita ta fito itama ta je kitchen ta dauko tsintsiya da faka dan ko ta kwanta ba wai iya baccin zatayi ba, bata saba ba, ta share falon tas ta gyara kitchen ta wanke kwanukan da suka bata jiya da daddare sannan ta wanke toilet, bayan ta gama usman ya tashi, ta rakashi bandakin tayi masa alwala da brush sannan tace yayi sallah, be iya ba tunda karami ne haka yayi tana kallon sa.
Wajen takwas Antyn ta dawo shashen sai dai tsananin mamaki ya kamata, ganin yadda ta gyara ko ina kamar ba ita ba, murmushi kawai ta dinga yi tana wa Allah godiya da ya duba ta ya bata 'ya me taimaka mata. Kunun da Abu ta dama tazo kawo wa kawai taga yadda ta gyara ko ina, albarka ta dinga saka mata sannan tace taje tayi wanka zata je ta gaida Baba idan sun gama karyawa.
A babban falon suke karyawa gaba dayan su, har Baban dan yace cin abinci a tare yana kara shakuwa, shiyasa suke zama kowa yaci da dan uwansa musamman weekend da baya fita da wuri sai rana ta daga. Fitowar ta kenan daga wanka ta gama saka kayanta tana goge ruwan da yake akan fuskar ta Amira da ta sato hanya ta leko dakin fuskarta a sake,"Kawata." Tace tana sako jikinta cikin dakin
"Amira." Ta kira sunan ta da taji Antyn ta fada jiya, hakan yayi ma Amiran dadi
"Jiddah ko?" Kai ta daga Mata
"Kizo muje mu karya, kinsan gaba daya muke yin breakfast har Baba."
"Hadda ni?"
"Eh, kema kin zama yar gidan nan ai, taho muje."
Ta ja hannun ta suka fito, bata so ba dan tana da jin kunya sosai da rashin saurin sabo, bata kuma saba da mutane da yawa ba daga ita sai baffanta sai Inna Lami. Sun firfito dukkan su kowa na zaune wasu a kasa wasu a saman kujera, su biyu ne mata a zaune Maryam, sai Safiyya wajen su Amiran ta jasu, tace
"Ya Sofy, Mero, ga Jiddah."
"Sannun ta."
Safiyyan tace tana danna wayarta, babba ce dan da alama duk ta girme su, murmushi sauran sukayi mata hakan ya sakata sakin jikinta kadan ta zauna a gefen Amiran ta makale. Maman su ce ta fito ta wata kofa taci ado sosai, kamar wadda zata tafi gasar kyau, babba ce dan akalla shekarun ta zasu kai arba'in da biyar amma ba zaka taba cewa ta kai ba saboda gyara da kyawun jiki. Duk suka gaishe ta ta amsa idon ta akan Jiddan, da sauri tace