*Sanadin*
*Labarina*
Free Page (4)
©®_Hafsat Rano_
** Tariq ne yake tuka motar Fauwaz na gefen sa,Baba a baya yana duba labarai a wayar sa jefi jefi suna hira da Fauwaz wanda shima rabin hankalin sa yana kan wayar sa yana duba wani pdf. Be fi sau biyu Tariq ya saka musu baki a hirar da suke ba har suka isa garin su Baban in da zasu dauko Hajiya Yaya
A kasan wata bishiya yayi faking kannen Baban dake zazzaune suna shan inuwa suka mike dukka suka yo wajen motar. Fauwaz ne ya bude ma Baba kofa ya matsa baya ya fito, ya shiga mika musu hannu suna gaisawa, kananan kuma suka russuna suna gaishe shi.
Cikin gidan suka dunguma suka shiga gaba daya, zuwa tsohon shashen Yayan kafin ta koma birni tun daga zuwa wani asibiti da tayi Baban yace tazo kenan, bata son birni sam amma babu yadda ta iya haka dai ta hakura bayan ya samu wasu daga cikin yan uwanta sun saka baki, duk da haka bata son zaman ta a cikin gidan sa dan ba wani shiri suke da Mama ba, ita Yaya dama bakin ta baya shiru bata gani bata tanka ba shiyasa tasu sam bata zo daya da Maman ba, tace Maman ta fiya isa da izza dan iyayenta wasu ne, shiyasa da Baba yazo mata da maganar auren Halima ta bada goyon baya dari bisa dari dan a ganin ta a lokacin ne zai auri daidai dashi.
Hayaniyar Yayan suka fara ji tana ta fada da sababi, muryar ta a sama sosai ta dage tana fada bilhakki da gaskiya, murmushi Baba yayi, ya girgiza kansa yayi sallama a tsakar gidan, muryar sa ta sakata yin shiru ta amsa sallamar tana jefar da sandar da yake hannun ta. Fuskar Tariq a hade dan shi ba kasafai ya fiya son hayaniya da shiga cikin mutane ba duk da Baba yana tirsasa masa shiga cikin yan uwan sa dan suna da matukar yawa, yanayin sa ne a hakan kamar Safiyya, su suko yo Mama dan itama bata cika son mutane ba sai wanda tayi mugun sabo dashi.
Shima kamar Maman ba shiri suke da Yayah ba, dan kullum yi masa korafi take bashi da sakin fuska, surutun ta shi yafi komai damun sa, dan idan ta fara magana baya jin ko hadiyar yawu tana yi. Fauwaz ne dan dakin ta da Amira, sune suka yo ta a surutu da kwashe kwashen mutane kowa nasu ne.
Tabarma ta dauko zata shinfida musu fauwaz ya karba ya tayata, ta zauna a gefen gadon ta suka gaisa da Baban sannan su Fauwaz din suka gaishe ta ta amsa tana ficewa taje ta kawo musu ruwa ta ajiye sannan tace"Ashe zaku zo, na dauka fa sai wani satin wallahi, ban gama abubuwan da nake anan din ba."
"Menene baki gama ba Yaya?"
"Em.. em akwai wani biki na yar Hajara nan kasa damu, babu dadi ace ban tsaya an yi bikin dani ba."
"Ayya, sai a basu hakuri Yaya, kinga fa lokacin komawar ki wajen likita yayi har yana neman wucewa."
"A ah gaskia ba zaa basu hakuri ba, sai dai a bani gudunmawa me tsoka na bata, sai kuma ka aiko matar ka itama tazo ranar bikin da gudunmawar ta."
Tace tana yin kicin-kicin da fuska, murmushi Baba yayi yace
"An gama Yaya, sai kuma me?"
"Shikenan, sai mu tafi tun da kayi niyya, ni wallahi dan ba yadda zan ne, a kai mutum a ajiye shi waje daya haba!"
"Kiyi hakuri Yaya."
"Idan ban hakuri ba ya zanyi toh? Fatan dayafi karfin ka ai sai ka mayar dashi wasa."
Har Kawu Rabi'u ya kawo madara da kwan zabin da ya tafi karbo wa Baba bata daina sababi ba, magaanar ta kadai kake ji a dakin sai dai Baba yayi murmushi lokaci zuwa lokaci ya amsa mata, shi kam Tariq ji yake kamar ya fice amma yasan idan yayi haka zai gamu da fishin Baba, shiyasa ya hakura ya zauna kawai yana sauraron surutun ta wanda baki daya babu magaanar da za'a kama.
Fita Baba yayi yace zai je waje ya zauna da yan uwan sa kafin Yayan ta gama shiryawa, yana fita Tariq da ya tabbatar ya kule yaja tsaki yana dafe kansa.