1.
"A sayi ruwa mai sanyi." Matashin saurayin ɗan shekaru ashirin da uku yake faɗi cikin tashar garin nasu, wanda yake cike da jama'a, cike da dukkan ƙarfin muryar shi da Allah ya ba shi ya ke fadin haka.
Hannu da ya ga ake ɗago daga wani mota yasa da sauri ya nufi wajen motar, yana isa ya sauƙar da babban robar ruwa da yake kansa a cike, yana cewa. "Hajiya na nawa kike so?""Ba mu na hamsin ya ishe mu." Matar da ya ƙira da Hajiya ta faɗa mishi, ta buɗe jakarta ta ciro naira ɗari biyu ta miƙa mishi. Ta sake cewa. "Wannan zafin cikin motar ai sai ya gasa mutum kafin ya isa. Hadiri ne a garin nan, ni dai fatana kar ruwa ya tare mu a hanya ya mana mugun bugu."
Murmushi kawai ya yi, ya kwashi pure water na daidai kudinta ya miƙa mata. Harara ta buga mishi ta ce. "Kai me haka? Haka zan riƙe a hannu ba ka da leda."
"Yi haƙuri Tsohuwa." Ya ce yana ɗaukar leda ya miƙa mata, ta karɓa tana gunguni ta miƙa mishi dari biyun, sai da ya miƙa mata canjinta sannan ya karɓa.
Ya ɗauki robar shi yabar wajen yana buga tsaki, don kawai daurewa yayi da halin da tsohuwar da nuna mishi.
Guri ya samu ya zauna, ya ciro kuɗin aljihunsa na gaban kodaddiyar rigar shi ya kirga, nan yaga ya yi ɗari takwas da hamsin, sauran pure water nashi na ɗari da hamsin.
Hamdala ya yi a ranshi don ganin ya samu abin da yake so, ya miƙe ya ɗauki robar shi ya nufi hanyar cikin gari, yasan masu tafiya zasu iya gani su saya kafin ya ƙarasa gida zai ɗan rage.
Turus ya tsaya ganinta, ta dumfaro shi saman kanta ɗauke da faranti mai cike da gyada soyayye, ido kawai ya zuba mata musamman yadda fuskartan nan tasha kwalliya caba-caba.
Yana tsaye har ƙaraso kusa da shi ta tsaya fuskarta cike da murmushi, shi ma murmushin yake mata sannan ya ce. "Sai yanzu ki ka fito?""Eh, ba ta gama da wuri ba ne." Ta faɗa mishi tana ci gaba da kallon fuskar shi ido cikin ido.
Shi ma cikin nata idanuwan yake kallo ya ce. "Ni kuma ga shi zan koma gida, ko na jira ki."Da sauri ta ce. "A'a nasan tun safe ka fito, ka je gida kawai."
"Na zo hira anjima." Ya tambayeta yana ɗaga mata gira ɗaya.
Da sauri ta ɗauke idanuwanta cikin nashi, ta yi gaba ta rabu da shi cike da kunya. Duk kallon da masu wucewa suke musu bai dameta ba domin tasan abin da zai biyo baya, wanda shi yake hanata ba shi ƙarfin guiwar zuwa wajenta hira kamar yadda samarin k'auyen suke zuwa hira wajen budurwa ƙofar gidan su.
...
Hayatu yana gani ta tafi ta bar shi ya juya ya ci gaba da tafiyar shi ya nufi gida. Ya rasa me yasa take ƙin hana shi zuwa wajenta hira, yasan irin zaman da take a gidan su amma tsakanin su bai shafi rayuwar ƴan gidan ba. Don shi kam ba zai canza ba, kuma ba zai daina sonta ba kamar yadda take son shi, kuma burin shi ya aureta.
...
Islam bayan shigarta cikin kasuwa yawo tayi sosai inda ta sayar da gyadarta kusan rabi da kwata, har ƙarfe biyar saura sannan ta nufi gidan su.
Da sallama ta shiga, nan ta yi arba da Uwale amaryar babanta tana surfe. Ciki ta ƙarasa zuwa ɗaya daga cikin ɗakunan da suke jere cikin gidan, a ƙofa ta tsaya ta doka sallama da ƙarfi.
Daga ciki aka amsa da ƙarfi kafin a fito babbar mace wacce ta kusa shekaru arba'in, amma tsufa da wahala ya mayar da ita tsohuwar dole don yadda ta zazzage.
Ihunta bai damu Islam ba, ta ciro kuɗin cikin dankwalinta ta miƙa mata ta ce. "Na sayar da na dubu biyu da naira ɗari, saura na ɗari huɗu.""To don ubanki me ya hanaki tsayawa ki sayar sauran, asara za ki saka ni?" Faɗin matar cikin faɗa kamar ta maketa don haushi.
Islam baya taja tana gunguni ta dangwarar mata farantin gyadar ta bar wajen.
Baba Babba ashar ta kundumawa Islam tana zaginta tana cewa. "Shegiya marasa kunya. To yau ba ki da kuɗin sallama."Islam dai bata kulata ba, ta ɗauki buta ta wuce ban gida. Fitsari ta yi ta fito, ta yi alwala wanda duk a kwabe tayi ta gama ta miƙe ta wuce ɗakin ƙarshe cikin sauran ɗakunan.
Tsohuwa ce zaune tana linkin kaya, Islam ta kawar kanta ta kalla gabar ta fara rafka sallolinta da ake binta ta yi ta gama.
Tsohuwar tana gani ta yi sallama ta juya tana kallonta ta ce. "Ke kam kamar ba kya zuwa islamiyya Islama, ki yi ta sallah kamar jahilar cikin kusurgumin daji."

ESTÁS LEYENDO
HAYATUL-ISLAM
RomanceBayan ƙaddarar soyayya ta haɗa su da juna tafiyar ba ta yi nisa ba ƙaddarar rabo ta nemi raba su. Rabo abu ne mai zafi, wanda yake tarwatsa dukkan buri. Stay tuned!!! Coming soon!!!