7

39 1 0
                                    

*BAƘAR DAULA*

      ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
 
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

              Free page 7

  🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥

Muna da bridal package

Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k

Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)

Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k

Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852

   Girma da siffar Badakaren ne suka sake hargitse lissafin rayuwata, a hankali na sake ja da baya ya yin da yake sake tunkaro mu gadan-gadan hannunsa ɗauke da wani mummunan ƙarfe wanda aka naɗe jikinsa da manyan ƙusoshi, a zafafe ya ɗaga da niyyar buga min a tsakar ka cikin shammata mahaifina ya kai masa duka a wuyansa. Take suka fara kokawa ganin haka ya sa mahaifina ya yi mini alama da mugudu ni da Kandala, gudu muke kamar ranmu zai fita don na gama tsorota da yanayin azzaluman mutanen da suka fito daga baƙar daula. A yadda na bar mahaifina da Badakaren ina jimamin halin da mahaifina yake ciki don na tabbata zai yi wuya idan bai yi wa mahaifina taron dangi sun hallaka shi ba, sai da muka yi tafiya mai nisan gaske sannan muka raɓa cikin wata bishiyar ɗorawa mai duhu muka zauna muna hutawa, waige-waige nake yi don ganin hanyar da zan samu ruwan da zan ɗebo mana musha saboda zafin ranar da ya busar da maƙogaronmu. A wahalce Kandala ta kalle ni idonta na zubda ƙwallah tana faɗin, "Kyauta ƙishirwa za ta kashe ni maƙoshina ya bushe." Jijjiga jaririn nake saboda kukan da yake ta tsalawa wanda na tabbata kukan wahala ne sannan na furta mata, "Riƙe min shi ki kula da kyau zan duba mana ko da ƙorama a kusa idan muka sha sai na duba ko zan samu wani naman dawan na gasa mana." Karɓarsa Kandala ta yi na miƙa cikin dajin ina duba hagu da dama ko zan samu ƙaramar ƙoramar da zan ɗebo mana ruwan, ko kaɗan ban yi tunanin wurin da zan ɗebi ruwan ba babban burina bai wuce mu samu ruwa kowanne iri ba ne. Daga can nesa na hango wani bafulatani yana tafe da shanunsa wanda hakan ne ya tabbatar min da kiwo yake, gudu-gudu sauri-sauri haka na rinƙa tafiya don na ƙarasa na cimma masa koda zai sa ya taimaka min, yana ganina ya fara bina da kallon tuhuma don ko bai faɗa ba na san suturar jikina yake kallo wacce ta bambamta da irin ta shi, kallon kaina na yi daga ni sai guntuwar fatar da ta rufe min ƙirjina da wacce na suturta al'aurata, sannan na ɗago na kalle shi yana sanye da farar rigar saƙi ta kala-kalan zarurruka, sandar hannunsa ya ɗaga na ji yana yin yaren da nake tsammanin fullaci ne sannan ya yo kaina da sauri zai sauke min ita. A razane na ja da baya cikin hakki ina faɗin, "Abar bauta bata wanzar da zalinci a doron ƙasa ba don haka kada ka cutar da ni."  Sauke sandar ya yi ƙasa sannan ya furta, "Hai meye abar bauta kuma? Ke kam aljani ne ko mutum?" Dafe kaina na yi saboda matsanancin ciwon da yake min sannan na furta, "Ni mutum ce tare nake da ƙanwata ka taimaka mana ka ba mu ruwa mu sha." Kallon da yake min ne na tabbatar min da har lokacin bai gama aminta da ni ba, don haka na ga ya runtse ido yana ci gaba da fulatanci sannan ya kara sandar hannunsa a saitin kaina. Ya ɗan jima a haka sannan ya buɗe idonsa ya ce, "Zan taimaka maka ina ƙanwar taka?" Hanyar da na baro su Kandala na nuna masa, ya ƙurawa wurin idanu sannan ya ciro kurtunsa ya miƙo min. Har na ɗaga kai zan sha na tuna halin da na baro su Kandala, da sauri na sauke shi na ce masa. "Ka taimaka ka cika ladanka ka bar ni na kaiwa ƙannena su sha. Idan ka yi haka abar bauta za ta albarka ci kiwonka." Ɓata fuska na ga ya yi don haka gabana ya faɗi, ina shirin roƙonsa na riski muryarsa yana faɗin, "Kada ki sake danganta ni da abin bautarku domin Yesi Almasihu zai yi fushi da ni saboda na haɗa bautarsa da waninsa." Shiru na yi ina mamakin maganarsa domin a iya sanina bayan abar bauta babu wani abu da ake bauta wa a faɗin duniya. Da yake ina cike da son biyan buƙatar kaina sai na gyaɗa masa kai cike da godiya, har na juya zan nufi hanyar na ji yana faɗin, "Ki bar hanyar ɓata ki dawo kan shiriya ko za ki samu gidan daɗi wato aljanna domin mu mabiya Yesu Almasihu mun kasance masu karamci da taimakawa saboda Allah." Ko kaɗan ban gane abin da yake nufi ba don haka ban amsa masa ba, sai na kawar da maganar cikin amsar da na bashi da cewar, "Zan gaggauta kai wa ƴan uwana akwai jariri ina tsoron kada ya mutu." A hargitse ya fura, "Jariri kuma?" Na gyaɗa masa kai, jin haka ya sa ya kaɗo shannunsa ya rufa min baya muka tunkari wurin da su Kandala suke. A galabaice muka same su don haka cikin hanzari na karɓi jaririn na fara bashi a lokacin tuni ya gaji da kuka ya sake yin bacci, sai da ya sha ya ƙoshi sannan na miƙa wa Kandala ita ma ta sha ta rage mini. Tausayin Jaririn ne ya kama shi ya dube ni yana faɗin, "Idan ba za ki damu ba ko na tatso masa nonon Naggen can ya sha." Ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min ba na furta masa, "Na gode sosai da taimakonka." Nonon saniyar ya tatsa da ɗuminsa ya miƙo mini na ɗan riƙa bashi kaɗan-kaɗan yana sha. Sai da na lura ya ƙoshi sannan na miƙa wa Kandala ta shanye sauran, miƙe wa na yi na yi na yi masa godiya muna shirin tafiya ya furta min, "Yanzu ina za ku tafi ke da kika ce baki da kowa?" Idanuna ne suka ciko da ƙwalla na furta masa, "A da ni ƴar gata ce gaba da baya, sai dai a yanzu ba ni da kowa ban san inda za mu tafi ba." Tambaya ya sake jefo min nan take ya bashi labarin abin da ya baro mu daga yankinmu, ya tausaya mana sosai don haka ya yi alƙawarin kai mu rugarsu domin ya taimaka mana, duk da ya gargaɗe ni a kan na ɓoye addinina idan kuwa na bayyana shi a rugarsu za su iya korata daga garin. A yadda ya ba ni labari tun tasowarsu iyaye da kakanni babu wani addini da suka sani face Kiristanci, a kan shi suka kafu Yesu Almasihu suke bautawa don haka ba su yadda akai musu kowanne irin addini saɓanin nasu ba. Ba ni da zaɓi don a lokacin burina bai wuce mu samu mutsuguni ba duba da ɗanyan goyon da muke tare da shi, a yadda na ayyana da ace daga ni sai Kandala ne za mu ci gaba da tafiya har mu nufi wani yankin da ba sa tsauwala wa game da addinin da ni kaina na gaje shi tun iyaye da Kakanni. Jiki babu ƙwari na sake rungume jaririn muka fara tafiya, ya wuce gaba shi da shannunsa muna biye.

BAƘAR DAULAWhere stories live. Discover now