Bin Son Zuciya Complete

19 1 0
                                    


KARIN HASKE DA TSOKACI

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Dukkan yabo su tabbata ga Allah Ubangijin dukkan duniya da halittu, Ubangijin sammai bakwai da kassai bakwai da abin dake tsakaninsu. Dukkan yabo ya tabbata ga wanda ya tsayar da sararin samaniya kyam ba tare da wani abu ya tokareta ba. Dukkan yabo ya tabbata ga Ubangijin da ya shiryar da mu ba tare da dabara ko karfinmu ba, hakika dukkan wanda Allah ya shiryar to fa wannan rahama ne daga Allah kuma ga Allah dukkan godiya ta ke, amma dukkan ran da ta kawai da kanta daga hanyar gaskiya, to kar wannan rai ta zargi kowa face kanta. Tsarki ya tabba ga Allah mai shiryar da wanda ya so.

Wannan ne labarina na farko a rayuwata da na rubuta. Da farko dai na faro shine a tsarin rubutun littafin zube, daga baya kuma na mayar da shi tsarin rubutun was an kwaikwayo har aka fara yunkurin mayar da shi zuwa Film a shekara 2015, daga baya kuma aka dakatar saboda wasu dalilai har ya zuwa wannan shekarar ta 2022 da mu ka mayar da tsarinsa rubutun wasan kwaikwayo mai dogon zango. A dalilin na tsawon dadewarsa sai na yanke shawarar sakinsa ga masu karatu domin su karanta kalubalena na farko, kuskurena na farko, jarumtata ta farko da kokarina na farko. Duk da na tabbatar jiya ba yau bace, amma tabbas ina alfahari da wannan labarin, domin anan ne dukkan komai ya samo asali da tushe. Kuma domin na sakewa masu karatu shi ba komai ba ne, domin wancan rubutun da mu kai na wasan kwaikwayo mai dogon zango sam bai yi kama da wannan ba, domin salo da tsari da zamanin ya sauya. Na faro wannan rubutun a shagon mahaifina da ke Azare, Jahar Bauchi, a Najeriya ranar 27th Satumba, 2013, na kuma kammalashi a Famagusta, Tsibirin Cyprus Ta Arewa, a Turkiya ranar 8th Mayu, 2014.

Da farko dai sunan labarin "A Dalilin Bin Son Zuciya" amma bayan da na nunawa Aminina Abubakar S Muhammad sai yace sunan bai yi ba a canjashi zuwa "Hassada" sai na amince da shawararsa na sauya masa suna zuwa hakan a cikin shekarar 2014. Amma a cikin shekarar 2022 bisa shawarata ni kadai, sai na canjawa labarin suna na dindindin zuwa "Dalilin Son Zuciya" kuma wannan shine sunan da labarin zai fita a matsayin ainihin sunan labarin.

Allah yasa mu dace, Amin Summa Amin.

Izzuddeen Muhammad Sani,

27th September, 2013.

SYNAPSES OF THE SCRIPT

Dukkan damuwa mai saukice, dukkan takaici mai saukine, dukkan kewa mai saukice, idan har an shirya musu ko an san da yiyuwar faruwarsu. Rana daya tak a wayi gari an nesantaka da iyalanka, sana'arka da al'umma, an kuma kebeka cikin kulawa ta musamman a wajen da kai ma kanka ba zaka iya cewa ga gabashinsa balle yammansa ba, watakila a wannan shekarar ta 2022 masu garkuwa da mutane ne suka sace ka, watakila kuma masu son yin tsafine da kai. Fatan jiran tsammanin ganin menene dalilin wannan killacewar da akai maka, ba ita ce babbar damuwa, takaici da kewar da ke addabar zuciyarka ba. Yaya iyalanka da 'yan'uwanka da makusantanka suke ciki? 'Dan hakuri kadan za ka kara a killace, har ka fahimci shin zaka rayu ne ko kuwa wannan shine karshenka; wato zaman jiran tsammanin rayuwa ko mutuwa, cike da dumbin damuwa, takaici da kewa.

Izzuddeen Muhammad Sani,

27th September, 2013.

BEGINNING OF THE SCRIPT

EXT. HARABAR ASIBITI - DAY

Mutumin yaci gaba da tafiya a hankali kuma da dingishi yana dafe da kafadarsa wani dake taimaka masa wajen tafiyar, yana kuma din gi sa kaf ar sa guda daya wac ce ak a nan na de da bandeji,wadda hakan ke nuna alamar karaya ya samu a kafar. Suka ci gaba da tafiya a cikin doguwar barandar asibitin a bayan su wata macece dauke da karamin akwati na sa kayan marar lafiya.tana binsu amma afuskarta tamkar duk takun da marar lafiyar yayi ciwon a cikin zuciyarta ne. Tana tafiya itama a hankali,a gefenta wani mutum sanye da riga ta likitoci shima fuskarsa cike fal da tausayawa ga marar lafiyan. Suka iso jikin wata mota su duka suka dakata marar lafiyan ya juyo a hankali ya dubi likitan.

Bin Son ZuciyaWhere stories live. Discover now