CHAPTER 20

55 6 0
                                    

   Nagama registration na fara lectures sai dai baa fara serious ba karatun dan wasu har yanzu ma basu gama registration din su ba.

      Ban hadu da ko wace kawa ba dan daga an gama lectures gida na ke wuce wa ko dan shirye shiryen rubuta jarabawan ss3 dakhiliyya da kharijiyya wato mock da  kuma na NBAIS ,ina alfahari dan kam yanzu na iya larabci kuma na iya rubutawa daidai gwargwado ga kuma manyan littattafai da aka mana.
   Inna zo gida karatu nakeyi because exam is starting on Saturday,wani lokaci kuma sai in zauna inta tunanin halin da masoyi na ya ke ciki yanzu dan ko waya mun daina yi.yau alhamis naje lecture din safe 8-10 ana tashi gida nadawo nazo ne akan yau dama zanje in duba shi a asibitin dan tunda mukaje da mama last week ban koma ba sai dai da yaya khalifa ya koma yace min jikin nasa da sauki,inaso inje amma kunya nakeji maman sa da yan uwan sa,ga kuma na kasa tambayar mama ince mata inaso inje.
  Nayi sallar azahar na tattaro courage na samu mama,cewa nayi mama yau baki kallo ne naga ko kunna tv bakiyi ba dagowa tayi ta kalleni sai tayi shiru,tv na nufa na kunna sannan tace toh gashi kin kunna,tsit nayi na samu wuri na zauna
     Shiru mu ke zaune mama na danna wayarta abinta tace ko zaki zuba mana abinci mufara ci kafin siyama ta dawo sch naga dadan sauran time tohm nace ban tashi ba dai
  mama ta kallo ni tace me kikeson fada min ne ?dariya na kyalkyale dashi nace yauwa mama so nakeyi ince miki in siyama ta dawo ta rakani in duba jikin tanimu,cewa tayi oh ni nabani shi ne kika tsaya kinata min kame kame ,ku je mana ni dama inata jira inga kince zaki koma,wata ajiyar zuciya nayi sannan kuma mama tahada da tanimu ai yaron kirki ne ga iyayen sa ma duk mutanen arziki.Kinga rannan na manta bamu kai fruits din ba da nasiya yau sai ku siya wani kutafi dashi da khalifa yana nan sai kuje tare amma ku din ma ba laifi ama karku dade.Inta dawo sai ku wuce tunda yau ba islamiyya Allah ta bashi lafiya.Amin nafada ina nufan kofar kitchen na shiga najiyo muryan siyama da surutun nan nata tashigo.
   Doguwar riga nasa da hijab dina,ko powder ban shafa ba siyama kuma abaya ta sa ta yafa gelen ta,ni na tuka motar sai da muka siya drinks da fruits sannan muka isa asibitin inata rokon Allah yasa ba mutane a dakin avin mamaki kuwa mun shiga ba kowa sai wani mai kama da tanimu da alama shi ne kanin sa khalil da yake fada min,ba zai wuce ace saa na ba gaisheni yayi na amsa masa nace khalil ko da mamaki a fuskan sa yace eh,ji mukayi yace kai durkusawa zakayi kagaida  ta aunty ka ce  asiya. Yace laa sannu da zuwa alaman ya gane ni,juyawa  yayi yagaida siyama dariya tafara yi tace kaga ni yarinya da ni karka maida ni wata babba dariya mukayi duk a tare.
    Daga nan gefe na samu wuri na zauna ina gaida shi siyama kam chan wurin gadon ta matsa sunata magana banjin  me suke cewa ,cewa yayi ita wacchan ko ba wiri na ta zo ba ne naga ko kallona batayi,siyama tace duk fa ta kosa mu iso ta ganka har roko takeyi Allah sa ba mutane gashi munzo babu kuma ta makale kinga yaya asiya matso jawoni tayi na zauna kan kujeran kusa da gadon kokarin tashi ya zauna yakeyi na hana sa nace haba dai ka kwanta,pillow dinsa na dan gyara masa yace yauwa yar baba nagode .
  Ina wuni nace masa yace bazaa amsa ba,kinzo kin makale a gefe haba yan mata na yar university naso ace ina da lafiya na rakaki registration din school and lot's more,ya makarantar i hope yana miki dadi ko,hawaye naji yataho min ganin halin da yake ciki duk ya rame ido daya ya rufe amma duk da haka bai dena wasan shi ba kukan na shanye,nace makaranta lafiya kalau nafara ashe da dadi dariya yayi yace not soo soon queen kibari a kai karshen semester ko wani 200 level sai muji ko da dadi ko babu dariya nayi nace toh zamu gani,ki maida hankali sosai kiyi karatu nasan bakida wasa amma ki dage kinga in GP dinki yayi kyau yanzu shikenan kin huta nan gaba.

  Naji dadin da kika zo kika sameni mama bata nan saboda muyi magana sosai duk da dai ni ko tana nan zanyi fira da ke amma ke nasanki da kunyan tsiya yar baba, yanzun nan ta fita da kyar kullum bata son tafiya ta bar kusa da ni amma yau kinga addua ki taci ta fita shi ne aka bar khalil.
   Ka cika surutu kaki bari in ma yi ma magana,to nayi shiru yi magana cewa nayi to to kana cin abinci yace eh ina ci,nafi shan drinks haka dai abu mara nauyi,tohm kadinga ci dayawa kaji toh yace, shiru na danyi yace toh shikenan maganar naki ya kare ai ni nasani ,dariya nayi nace toh ban gama ba ya jikin naka?
   Cewa  yayi da sauki ina jiran lokaci Asiya naji dadi da kika zo kafin dayan ido na ya rufe kaman yanda nafada miki wanchan zuwan a waya inaso ki kula duk wanda yazo gurinki kiyi auren ki kar ki tsaya bata lokaci ko tunani inna mutu nidai kawai kiyita min adduaa.
   Kina da kyau da hali me kyau,ke mace ce ko wani namiji keda burin samun kalarta,i thought na samu mata ashe ke ba tawa ba ce you are going to be a very shining star 🌟,you are already shining saboda duk wanda kika zauna da shi sai ya dandana alkairin ki,ki cigaba da zama mai mutuncinki,Allah ya miki albarka.
   Duk maganan nan da yakeyi ina kallon sa na rike hannun sa ya na daga kwance ina zaune amma na daure naki inyi kuka,ki cigaba da min adduaa,kadaina surutun nan zaka tashi lafiya insha Allahu ciwo ba mutuwa ba,murmushi yayi sai baice komai ba kuma.
    Na dan jima a zaunen sannan yace kizo ku tafi gida kin zauna kin tsureni da ido ko jira kike sai na mutu zaki wuce dariya na yi sosai shima yana yin dariyan sosai yace kinga na dade banyi dariya haka ba ,i love you nafada masa ba tare da na furta ba amma motsin baki na ya nuna masa haka shima hakan ya amaa min yace i love you more, nace zaka tashi insha Allah kuma zamuyi aure,and i will never let you go.
     Tashi nayi naga hawaye a idon siyama da khalil,da sauri kowa ya goge hawayen sa ni kam nawuce ido na a bushe ba ko kuka amma ni kadai nasan me nakeji a zuciya ta gwara ma a ce kukan nayi
   Har muka koma gida ba wanda yayi magana,ina shiga gida daki kawai na wice ina kan gado naji hawaye nata zubomin a hankali na ke sharewa tun ina sharewa har na kyalesu su kayi ta zuba.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now