Part 1

733 32 6
                                    


"Mama qarfe uku zamu tafi gidan Kamun fa, kinga unguwar su da nisa kuma Abba yace mu dena yin dare a waje" Umaimah dake tsaye daga bakin qofar daki ta fada tana kallon Babbar Macen dake tsinke danyan zogale tana jefawa a cikin babar robar dake gaban ta.
Banza tayi mata taci gaba da aikinta, se kuwa ta takwarkwashe fuska kana ganinta kasan tana fama da tsiwa da shagwaba tace

"Mama kina jina fa kikayi shiru, se kuma an jima na gama shiryawa kice ban gaya miki ba"
"Idan baki matsamun daga nan ba UMAIMAH sena bata miki rai a gidan nan, na gaya miki babu inda zaki je wallahi idan bakiyi wankin nan ba, ke ko kunya bakyaji a shiga dakinku wai sunan dakin Yanmata kin hargitsa muku ko ina da shirgin dattinki qazamar banza qazamar wofi" Maman ta dago a fusace tana fada tana kallonta.

Wata Fara doguwar mace ta fito daga Kitchen tana cewa
"Maman yara kenan, ki barta mana bana ji dazu tana cewa Nazifi gobe yazo ya mata wanki ba naga fa kayan da yawa idan kika ce seta wanke ai seta makara zuwa gidan bikin ko"

"Ai Antyn su Ko shekara zatayi wallahi seta wanke su kuwa na gaji da iskancin ta, shekara goma sha tara ai ba wata sha tara bace da kullum ita tana girma tana cin qasa, in ba haka ba ko dakin su Saddiqa ka shiga ai baka tarar da bolar da UMAIMAH take tarawa, ni wallahi ma baiken Nuratu nake gani da har ta iya hada daki da qazamar banza bayan ita komai nata tsaf tsaf yake" Maman ta sake fada tana Harara Umaimah dake ta faman tura baki.

"Haba, ai bazaki hada ba, da zama da mutum yana saka ka koyi halinsa ai da Umaimah batayi qazanta ba dan duk gidan nan babu wanda yakai Nuratu tsafta, su Umaimah kuwa ba'a magana" Antyn ta Fada tana zama a kusada Mama dan tayata qarasa gyaran zogalen.

"Munafuka kawai, kece qazama bani ba dai" Umaimah ta fada qasa qasa tana juyawa cikin dakinsu, Mama dake kallon Bakinta tsaf ta fahimci abinda ta fada dan daman tasan za'a rina, Umaimah se gyara da shiriyar Allah kawai. Daga cikin dakin ta ringa watso kayan wankin tsakar gida babu wanda ya tanka mata daga maman har Anty har ta gama iskancinta ta fito ta tattara su zuwa gaban fanfo ta tara ruwa a bokitai ta hau wanki.

Cikin qanqanin lokaci kuwa se gashi ta gama yanda kasan wacce ake tayawa, ta zagaya bayan gidan inda igiya take ta shanya kayanta tas ta dawo ta dauraye gurin da tayi wankin lokacin har Anty ta sauke dambun da suka girka a matsayin abincin rana. Tana dacin rai dan tunda ta fara wankin tafi ku mutu bata ce musu ba har ta gama ta shige dakinsu, can ma bata zauna ba, gadonta dake nana hargitse ta gyara bayan data saka sabon zanin gado dan ta wanke na kai yanzu nan da nan ta share dakin ta hado ruwa ta goge ko ina kafin ta fada wanka ganin har qarfe biyu ta gota dan tun kusan goma take aikin.

Tana bandakin ta jiyo sallamar Anty Laure, qanwar Mamansu ce da suke uwa daya uba daya ta tabe baki dan tasan yanzu zasu qara haduwa su sakata a gaba da magana dan ma Allah yaso bata tarar da ita tana wankin ba amma tasan se munafukar Antyn can ta gaya mata ma, haka tayo wankan ta tareda alwala ta fito tana ta sauri, dukda qarfe biyar aka saka a katin kamun amma so take ta tafi da wuri dan seta biya ta inda Amarya taje kwalliya dan itace babbar qawarta. Daren da sukayi jiya a gurin Bridal shower ya saka Abba hanata tafiya tun sassafe dan da gaba daya ma hanata yayi seda Anty ta saka baki kafin ya kafa mata sharadin karya wuce qarfe shida yau amma dukda haka bata mata gwani ta ba.

Tana cikin yin sallah qawarta Rumasa'u Murtala tayi sallama, kamar ta sallame ta dakatar da ita karya shiga falon inda take jiyo muryoyin su Maman dan tabbas seta rusa mata shirin da tayi amma ba hali haka ta shiga karatun sallar sauri sauri tana jiyo ta suna gaisawa tana kuwa sallame wa ta fice falon da sauri har Hijab na neman tadeta ta kwalawa Ruman kira.

"Ke kuma fa kamar wadda aka biyo?" Anty Laure ta fada tana kallonta, seta saki murmushin da yake qara mata kyau tace
"Babu komai Momy ina wuni? Yasu Bintu? Ruma shigo mana kin ganni na kusa qarasawa ma" ta fada tana kama hannun Rumasa'un.

HALIN KISHI (NADAMAR UMAIMAH)Where stories live. Discover now