Hangota Khalil yayi ta doshi hanyar waje yabi bayanta da sauri kamarta sani ta qarawa tafiyarta sauri, cikin sassarfa ya bita ganin har ta kusa isa gate din Asibitin ya daga murya yana kiran sunanta amma bata juya ba jefa qafunta kawai take tana tafiya, ji take ina ma data rufe ido ta bude zata ganta a gida tsabar yanda ta tsani Asibitin da Duk wadanda suke ciki sa.
"Umaimah meye haka ne kina ji ina kiranki ina zakije ko jikin ne ya tashin miki?" Khalil ya fada bayandaya tararda ita yasha gabanta. Wani shegen kallo ta watsa masa, yanda ya ke washe baki yana riqe da hannun wannnan matar ya dawo mata seta kauce shi taci gaba da tafiyarta ya qara tare ta cikin fada fada yace
"Wai ke meyasa kike haka, ina miki magana shine zaki wuce kici gaba da tafiya ina zakije? Idan wani abun ne ya faru ki gaya mun mana se muje na kaiki"
"Allah ya kiyeye na sake shiga motar ka kaje dai kaci gaba da diban wadancan jakan marasa kamun kai da kake kulawa, tsabar rashin kunya a gaban uwar data haife ka da sauran mutane kake kama hannun wata qatuwa kuna dariya"
"Jamilar ce baki sani ba? Meyasa idan wulaqancinki ya tashi se kin nemi abinda zaki cimun mutunchi ko yan uwana?" Ya fada yana kallonta cikin ido saboda yanda kalmar Jaka data alaqanta da yar uwarsa. Seda ta harare shi kafin tace
"Toh dan Jamila ce se aka ce ku tsaya kuna iskanci a gaban mutane"
"Iskanci Umaimah, nine nake iskancin?" Ya sake katseta yana nuna kansa da yatsa.Dauke kanta gefe tayi tana qunquni qasa qasa wanda tsaf ya jita "toh idab ba iskanci ba menene zaka wani kama mata hannu a tsakiyar mutane ita kuma se wani murmushi take tana yaqe haqora" ta fada. Seda Khalil ya hadiye malolon baqin cikin daya taso masa zuciyarsa tana ayyana masa rashin dacewarsa da wannan mara kunyar yarinyar qarara.
Dakyar ya iya bude baki yace "ki jira na yiwa Nuratu magana ta fito na mayar daku gida" dan ko babu komai shi ya dakko su daga qofar gidansu kuma seda Abba ya jaddada akan su dawo da wuri dan haka dole ya mayar dasu daga baya ze zauna ya yankewa kansa hukunnci akan ta, dan ya fara hango dalilan da suka saka har mutum uku fasa auranta, sannan yaga tasa wautar qarara da yake qoqarin daukar ta ya kaita nasa gidan.
"Ni? Ai wallahi bazan shiga motar ka ba ita dai da bata da zuciya taje ta zauna seka maida ita amma ni kaga tafiyata, kuma ka qaddara daga nan gurin babu ni babu kai kaje can cikin yan uwan naka ka auri daya idan zaka iya" Umaimah ta fada cikin tsananin rashin kunya kafin ta murguda masa baki tareda baza Hijabinta da yake har qasa ta tafi ta barshi a gurin kamar wanda aka dasa.
Dakyar ya iya jan qafafunsa da sukayi sanyi ya koma dakin, yana shiga suka hau tambayarsa ina take lafiya dai? Ya rasa me zece musu ga tunanin maganar data fada masa da ke neman ruguzashi haka ya daure ya tattaro yawun bakin sa yace "Amai ne ya taso mata, gata can A mota Nuratu muje na mayar daku gida tace akwai sauran magungunanta da bata gama shanyewa ba".
Nuratu da duk ta tsargu dan tun fitar sa wata daga cikin matan ta fara qananun maganganu akan taga wani kallon wulaqanci da Umaiman ta watsa musu kafin ta fita, aka samu wata ta goyi ganin zasu tada hayaniya Hajiya ta tsawatar musu, ita dai tayi tsuru, Jamilan ta zauna kusa da ita tana janta da magana amma ta kasa amsawa se murmushin yaqe kawai take tasan Allah kadai yasan yanda zasu kwashe a wajen nan, Allah yasa kar tayi rashin hankalin nata data saba ta tarawa kanta mutane har magana ta dawo dakin su samu nayi shigowar da Khalil yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya dukda a kallo daya da tayi masa ta gane akwai matsala Umaimah tayi tsiyar, yana cewa ta tashi kuwa ta miqe tana qara yiwa Hajiya Addu'ar samun sauqi ta fice.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
HALIN KISHI (NADAMAR UMAIMAH)
Художественная прозаLabarin Umaimah mace me tsananin kishi wanda ya kaita ga gamuwa da qaddarar da ta sanya ta a dana sani na har abada