17&18

28 3 0
                                    

*DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE*
( _DSP ALIYU HAIDAR👨🏻‍✈️_)

BY
*ZAHRA ABDUL*
( MOMYN AHLAN)

SAHIBAR KAINUWA👸🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

Dedicated to brosmie ALIYU💓

Special gift to my heartbeats bloodies fam💞💕
❤️💘❤️💘❤️💘
===========
Follow me on my wattpad @Fateemah0.
==============
*MARUBUCIYAR.*
1-HALITTA DAGA ALLAH NE.
2-GUDU A JEJI.
3-SHUHADA.
4-NIDA ƘANNEN MIJINA.
5-WA'YA KASHE ZAHRA'U? #200.
6-COLONEL UBAIDULLAH.
7-ITA CE ZUCIYATA #200.
8-SAMIMA (MACIJIYA CE).
9-DA NA SANI NA.
10-GAWURTACCEN SOJA #300.
11-BADAWIYYAH.
12-AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE) #300.
13- AHLAN #200.

    NOW
Typing.....
*DSP ALIYU HAIDAR.*✍

🅿️....1️⃣7️⃣▶1️⃣8️⃣

 
Sosai Aliyu ya duƙufa bincike akan mai wannan sunan Crus'danger. ya yi bincike har na tsawon wata daya wanda a wannan wata dayan bai san iyakar adadin tsagerun da ya kama ba wanda kaf cikinsu ba Crus'danger, sosai jikinsa ya fara sanyi a case din.

A yau ma kamar kullum yaje gidansu gaishe da Abba da Hajiya Dalah wanda kafin ya kama Faisal idan ya gaisheta tana amsawa sabida kwarjinin da Aliyu ke yi mata yana cika ido akasin yanzu da bata amsawa burinta kawai ta kashe shi.

Ya zo fitowa kenan Faisal na waya a handsfree ya ji an ambaci wannan sunan da yake tsumayin kamewa, tunani ya hau yi ba dai shima Faisal yana yiwa Crus'danger aiki bane? A ranar ko bacci bai yi ba sabida tashin hankali yana ta fargaban kar zarginsa ya tabbata Yayansa uba ɗaya yana tare da ɗan ta'adda.
Tun daga ranar ya sanyawa Faisal idanu ya fara bin diddigin Faisal da duk wani motsinsa kuma shi da kansa yake aikin bai ma saka wani ba bare a samu matsala.

Wata ranar laraba da Aliyu ba zai manta ba da safe ya zo gaishe da Abbansa da Hajiya Dalah, zai shiga ciki suka yi karo da Faisal wanda ya fito a fujajan, ganin yanayin da Faisal ya fita sam hankalin Aliyu bai kwanta ba haka nan yasa ya fasa shiga gaida Abba da Hajiya Dalah ya bi bayan Faisal wanda kwata-kwata basu san ana bin su a baya ba, anyi tafiya mai tsayin gaske har aka iso madakatar da za a dakata inda Aliyu yake bin gurin da kallo wajan shi ba kango ba ba fili ba, da shike yayi parking daga nesa a hankali ya lallabo yana leke a sadda Faisal ya fito a mota ya tinkari cikin wani sashe daga cikin kangon duk excort dinsa na biye da shi wanda hakan ya bai wa Aliyu damar shigewa shima.

Faisal yana shiga ya fara dauke su da mari a lokacin da Aliyu ya sawo kansa dan ganin meke faruwa me Faisal zai yi a wannan gurin? tunaninsa bai katse ba ya tsinkayi muryar Faisal da abinda yake faɗi wanda ya kusan haukata shi dan kwakwalwarsa sai da ta tsaya na wucin gadi.
"Ta ya za ku ce min yara goma sha shidda sun mutu, hauka ku ke yi kun san yara 16 din nan kudinsu ya kai nawa?"
"Ka yi hakuri Crus'danger akasi aka samu, goman sun mutu ne ta sanadin gwajin maganin da ka haɗa wato biyar ta sanadin maganin yara uku wajan operation da aka sanya musu kwayoyi a ciki wanda za a tsallake border dasu, ana saka musu kwayar suka mutu, biyun kuma wannan allurar ne tayi sanadinsu ana yi musu suka hau buge-buge har suka mutu" cikin 6acin rai Faisal yace
"Okay naji goman sun mutu ne ta sanadin gwaji wannan ba komai bane, su kuma 6 din fa?" jiki na rawa wanda aka tsare shi da tambayoyi sai zufa yake yi ya juya ya kalli abokan aikinsa mutum shidda da jikinsu sai rawa yake yi murya na rawa yace.
"Su Antorny ne suka yi musu fyaɗe har suka mutu" wani waigowa Faisal yayi ya zuba musu idanunsa na tsageru tuni suka zube guiwowinsu a ƙasa suka sa kuka
  "Kayi hakuri Crus'danger mun tuba ba zamu sake ba karka kashe mu" jinjina kai Faisal ke yi kana daga bisani yace
"Zan yi muku afuwa ne kawai idan ku ka fita farauto min madadinsu dan ni bana wasa da harkallah, munyi magana da Alex Devid ya ce 'yan matan nan kwantena biyar yake so dan haka a nemo goma sha shiddan da aka rasa kuna dai gani yanzu yaran ma ba a cika samun su ba ina ga zamu fara shiga jaha-jaha kame" Aliyu dake tsaye tamkar mutum-mutumin haka ya zama idanunsa sun kada sunyi jajur duk wata jijiya dake gudana a jikinsa ba wanda bai fito raɗau ba kamar an zanesu barin ma jijiyar tsakiyar goshinsa da jijiyar wuya,
Kenan zarginsa ya tabbata? Kenan Faisal ba wa ɗan ta'adda yake yiwa aiki ba shine ma crus'dangern da kansa? Tamkar anyi 6arin wuta haka idanun Aliyu Haidar suka koma, tunaninsa ne ya dawo jin Faisal na tambaya ina gawan yaran? Antorny yace
"Gasu can" ɗago ido Aliyu yayi ya ga yadda aka ci zarafin yara gasu nan a shinfiɗe a wulakanci babu suturar arziki a jikinsu
"Ku kwashe su kuje ku watsar da su!" ya fada cikin rashin imani, wato da ace Aliyu mai saurin kuka ne wannan abu da ya gani yaci ace furkarsa ya jiƙe da ruwan hawaye amma hawaye ko digo bai digowa Aliyu ba sai idanunsa da suka yi jaa kamar jan wuta, a hankali ya daga kafafunsa ya fara kokarin bayyana a garesu dan ya bi mutanen gurin kaf da kallo ba wanda zai iya buguwa a hannunsa a gurin karya ne ba ayi sa ba, sautin takalmi kawai suka ji domin yana sanye ne da kakinsa da zai bayyanar maka da shi din wanene, saurin kallon wurin shigowar sukayi suna mamakin waye haka da har ya samu karfin guiwar yi musu bin diddigi ya shigo musu wajan harkallansu? Lallai koma waye dama a rubuce yake yau kwanansa ya kare.
    Aliyu na shigowa da sauri duk yaran Faisal suka ɗaga bindiga suka saita shi, Faisal ya zaro idanu yana fadin
"Haidar!" ɗagowa Aliyu ya yi duk yana binsu da kallo, firgita Faisal ya yi yana ja da baya ganin yadda fuskar Aliyu ya sauya jijiyoyi suka bayyana a fuskarsa ga idanunsa jajur, harbi suke son yi ya daka musu tsawa da fadin
"Stop! He's my brother" wani ɗaci Aliyu ya ji a ransa jin Faisal ya ambaceshi da sunan ɗan uwansa, wayarsa ya ɗaga ya kira policestation dinsu ya gaya musu inda yake akan su zo yanzun nan za a kama yan ta'adda, cikin kiɗima Faisal ya fara magana.
"Are u out of ur sense? Ni zaka kira ka ce a kama?" jin haka yasa yaran Faisal kokarin dukan Aliyu duk da Faisal na hanasu, amma ina ance mai rabon cin duka bari bata aiki, nan Aliyu ya samu ƙasusuwarsu ya hau ragargaza yana karya musu ƙashi yana kallon Faisal wanda zuwa yanzu shima ransa ya fara 6aci da dukan yaransa da Aliyu ke yi, ganin haka yasa wasu kokarin son su gudu amma ina tuni Aliyu ya fara janyosu yana dukkansu idanunsa akan Faisal da gawan yaran mutane a kwance a wulakance, wani ne da ya kai masa duka ya bugi wani kofa sai da kofar ta buɗe, kofar na buɗewa yara ne birjik a ciki suna ta kuka, Aliyu ji yayi wutar kansa ta dauke, ganin haka yasa Faisal shako Aliyu yana fadin
"U have to stop this Haidar! me kake shirin yi? 6ata min harkallata da kasuwancina ko miye?" duk yadda hawaye yaso zubowa a idanunsa inaa abin ya faskara ya kasa hawaye, juyowar da zaiyi ya kai wa Faisal naushi a baki tuni hanci da bakin Faisal ya hau fidda jini, nan faɗa ya tashi aka hau musayar karfi da shike Faisal criminal ne yana da karfi nan suka hau dambatuwa da Aliyu wanda tuni ya manta da waye Faisal a gurinsa, suna cikin damben ne motar policestation din su Aliyu ta iso kasantuwar sunyi amfani da na'ura wajan bibiyar layin Aliyu, ai kuwa suna shigowa Aliyu ya bada umarnin a kwashe yaran Faisal da ya karya dik ayi dasu station, shi da hannunsa ya damki Faisal ya sanya shi a mota 'yan matan da gudu da kuka suka fito suna komawa bayan Aliyu, sai da aka kuma kawo babban mota aka dauki gawan yaran da suka mutu daga can mafakan Faisal asibiti aka wuce dasu wanda aka yi bincike aka tabbatar sun mutu ne sabida gur6ataccen sinadarin magani,wasu kuma ta hanyar raping kamar dai yadda yaran Faisal suka gaya masa, a ranar da yamma aka hau watsa labarin, a asibiti aka bar yaran bayan an dauki hotunansu kowacce ta faɗi unguwar da take.
Koda Aliyu ya bar policestation gidan su mahaifiyarsa ya wuce yana shiga Innani nayi masa sababi da shike ita ta bude masa kofa, bai bi ta kanta ba ga wuce wajan Ammy dake zaune a falo suna kallon tafsir, yana zuwa ya zube guiwowinsa a kasa ya kifa kansa a kafarta jikinsa sai 6ari yake yi ga shi jikinsa yayi mugun zafi, hankali tashe Ammy ke shafa kan Aliyu tana tambayarsa meya faru? ganin bazai yi magana ba yasa da sauri ta miƙe ta je kitchen ta dauko ruwan sanyi ta shafa masa a fuska ya hau sauke ajiyar zuciya bakinsa har na hayaki, yafi mintuna talatin kan ya kalli Ammy yace.
"Na yi mugun bakinciki da ya kasance Faisal dan uwana ne Ammy! Da fari ina tsoro ina fargaba ace Faisal yana yiwa ɗan ta'adda aiki ashe shine cikakken dan ta'addan" ya faɗa da karfi yana dukan ƙaramin stool din dake gefen kujera wanda nan take ta tarwatse, sosai Ammy da Innani suka girgiza da Labari da Aliyu ya basu a yau akan Faisal inda tsoro da fargaban yadda za a ƙarƙe da wannan sabuwar chakwakiyar da ta 6allo kai Ammy ke yi, inda Innani anan take ta ba wa Aliyu ƙwarin guiwar dik wani mai laifi ya zartar da hukunci bisa gaskiya da adalci koda Khamis ne ya je ya sarƙame shi bama Faisal ba, sosai Ammy ta dinga dannarsa har wajan goman dare kafin tace masa yaje gida Basmah ita kadaice kar hankalinta ya tashi ciwonta ya tashi tinda yace baiyi mata waya ba, sallama ya musu ya nufi gida jikinsa duk a sanyaye.
A falo ya samu Basma zaune tayi shuru da alaman damuwa, jin sallamarsa yasa ta tashi da sauri taje ta shige jikinsa, yana jinta a jikinsa ya lumshe ido cikin kashi dari na damuwarsa yaji kashi arba'in ya gudu
"Yaya Haidar yau ina ka shiga haka? Ba waya ba sako hankalina ya tashi wlh dik da ina tunanin ko aiki ne ya maka yawa amma naji na kasa samun natsuwa"
"Sorry" ya faɗa a gajarce, sakinsa tayi tana kallon fuskarsa tasa hannu ta karbi jakar system dinsa, sama ya haura ta bi shi, wanka ya yi ya shirya cikin jallabiyya ya zauna a bakin gado ya riƙe kai yana sake tariyo abinda ya faru yanaji kamar a mafarki, yau rana ce mai muni a garesa, Basma da ta kasa fahintar meke damunsa yasa ta matso kusa da shi ta kama hannunsa a sanyaye tace
"Ina fata ba ni bace silar wannan damuwa da na ganta akan fuskarka ba mijina, idan kuwa ni ce bazan gushe anan ba face nai ta kuka ina neman afuwa da yafiyarka har sai ka yafe min" ta faɗa idanunta na tara ruwan hawaye duk da tasan bai son kuka ya tsani kuka, saurin rungumeta ya yi dan yasan halinta tana iya saka mi shi kuka, cikin kunar rai ya hau bata labari wanda ita ma Basmah sosai ta girgiza da lamarin, a ranar Aliyu bai rintsa ba. Da washe hari sai da ya fara biyawa gurin AIG bai boye masa komai ba ya sanar da shi komai duk ya nuna masa hujjarsa sannan ya shaida masa Yayansa ne Ubansu daya, zare idanu AIG yayi yana fadin.
"Yayanka dai Aliyu Haidar? Anya zaka iya da case din nan ko dai a ba wa wani to?"
"Sir! Ko da sunan mahaifina ne ya fito a 6ata gari sai inda karfina ya kare nayi rantsuwa akan aikina zanyi gaskiya da adalci, a yayinda na sanya kaki al'umma nake dubawa ba sanayya ba, ka yarda dani sir" jinjina kai AIG yayi yana fadin.
"Na jima da yarda da kai Aliyu kaje kayi aikinka yadda ka saba bisa gaskiya Allah yana tare da kai sannan kana da goyon bayana duk abinda ya kamata kayi da sa hannuna,ga wannan takardan shaidar, zanyi magana da DIG a waya anjima" sara masa Aliyu yayi yana karban takardan iko da AIG ya ba shi kana ya fita daga nan ya wuce asibiti a can ya samu Iyayen yara sunzo domin kuwa tin a jiyan aka sanar da wasu, wasu kuma sai a yau da safe, har ta da wanda suka rasu iyayensu sunzo sabida duk yaran gari daya ne ga kuma hotuna da labaran da ake ta yaɗawa kuma dama iyayen jira suke yi su ji sanarwan an samu 'ya'yansu sun bayyana dan adduarsu kenan ba dare ba rana.
   Asibiti ta ruɗe ta hargitse ga koke-koke dake tashi, koda Aliyu ya iso yake tambayar kukan me ake yi haka? dan kukan yayi yawa da alama kuma ya zarce ta farincikin bayyanar yara haka kuma ya zarce na bakincikin waɗanda suka rasu, IP Muttaƙa ke gayawa Aliyu da cewan ai anzo anyi bealin Yayansa dazu, wani zaro ido Aliyu yayi yana jin ba'asin waye yazo yayi bealin Faisal? Inda IP Muttaƙa ya shaida masa da cewa ai Hajiya Dalah ce, wa ya bada bealin? IP Muttaka ya ce.
"SP Sale A Wanzam ne"  kasa shiga cikin asibitin Aliyu yayi ga kuma 'yan jarida a gurin, juyawa Aliyu yayi zai koma ya ji magana kamar daga sama tsayawa ya yi cak gami da juyowa ya ɗora idanunsa akan wata mata kana ganinta ka ga kwayar idanunta zaka ga tsantsar ciwon dake zuciyarta.
"Ba abinda za ayi akan wannan abun! Cuta ne dai an riga da an cucemu! Bamu da karfin shari'a da ku sabida mu talakawa ne amma ku sani muna da bakin da zamu daga murya mu yi Allah ya isa kuma bazamu gushe ba muna adduar Allah ya mana sakayya da gaggawa, daga fita zata je islamiyya muka nemeta muka rasa, sai yanzu da na ga gawarta an keta mata mutuncinta har sai da ta bar duniya! ita kaɗaice Allah ya bamu, mahaifinta ya rasu watanni shidda da suka wuce, marainiya ce! wa hakan kadai Allah bazai bar ku ba, ba abinda 'yan sanda zasu yi akai na sani!" ta karasa cikin wani kuka da yasa Aliyu ya rintse ido, nan wata tsohuwa ma ta hau gaggayawa 'yan sanda magana tana zagin Aliyu ita ma jikarta tana cikin sha shiddan da suka rasu, wadanda dai yaransu suka dawo sun tsallake rijiya da baya sai hamdala suke yiwa Ubangiji, sautin kukansu har karkashin zuciyarsa a yake ji, da karfi ya ce
"Na rantse da wanda raina yake hannunsa ni nan zan tabbatar sai anyi muku adalci koda kuwa hakan zaiyi sanadiyyar rasa rayuwata, koda duk abinda na mallaka zai kare zan yi shari'a da Yayana! ban san adadin yara nawa bane ya salwantar amma alhamdulillah su waɗannan sun kubuta, zanyi iyakar yina naga ba wata uwa ko uba ko yan uwa da zasu sake zubar da hawaye akan Faisal Khamis, yaran nan ƙannena ne, saina tabbatar da sun samu adalci sabida cika alkawarina da na dauka ku yarda dani" jin abinda Aliyu ya fada yasa suka yi shuru suna kallonsa wata tsohuwa tukuf ne ta kalli Aliyu tace.
"Zaka yi albarka a rayuwarka"
"Nagode Kaka" Aliyu ya faɗa yana juyawa ya kalli IP Muttaka yace.
"A sa a maida su gida cikin aminci sannan ayiwa SM Rukayya magana zanyi aike, yaran kuma wasu daga jami'anmu su halarci jana'izarsu ,SC Bara muje station" daga nan Aliyu ya shige mota basu tsaya ko ina ba sai a policestation yana isa office din SP Sale A Wanzam ya nufa, sallama kawai yayi dan ko neman izinin shiga bai tsaya yi ba, SP Sale na ganinsa ya hau murmushi gami da faɗin
"DSP AKA mai gaskiya, ko a tarihin ban taba jin wanda ya kama Yayansa Uba daya ba, ka ga wannan maslaha ce ta cikin gida ka je ku daidaita ba wani matsala bane da abin da ya aikata rayuwarce tazo da haka sabida...." wani gigitaccen naushi Aliyu ya saukewa bakin SP Sale, wanda ya dago a hargitse cikin magagin son nuna masa shi gaba yake da shi, kan ya yi wani yunkuri Aliyu ya zaro masa idanu ya daga masa babbar yatsa yana fadin
"Bangaren aiki ba ruwana da sanayya! Anzo an cika maka kudi an baka cin hanci ka saki mai laifi,wasu daga cikin manyanmu duk abinda yake faruwa da saka hannunsu kamar dai kai din nan! Ina mai maka albishir da cewa zanje na kamo Faisal Khamis wanda zai girbi daidai abinda ya shuka, kai kuma a matsayina na ƙasanka na dakatar da kai na tsawon wata shidda bisa laifin ka saki mai laifi, AIG ne ya bani cikakken iko ga takardan nan" Aliyu ya nuna wa SP Sale da sai zaro idanu yake yi
"Idan baka so mutuncinka ya zube kafin naje na taho da Faisal Khamis ka koma gida dan kayan 'yan sanda ma bata kama ce ka ba" yana gama fadi ya fice.
Mota uku na shi shine a gaba ya nufi gidansu, a lokacin Hajiya Dalah na hakimce a falo ita da Faisal wanda take kara jaddada masa indai da kudi ba wanda ya isa ya kulle shi ko a zartar da hukunci a kansa bare ma ita bata ga aibun laifinsa ba, kuma zata bi duk iyayen da aka haska ta basu 1m tunda ta ga kaf talakawa ne akan cewa su janye kudirinsu na son ganin adalci dan ba samu zasu yi ba, Abba ne ya sauko daga sama yana yiwa Faisal faɗa akan abinda ya aikata inda nan take Hajiya Dalah ta rufe Abba da fada kamar ɗan cikinta wanda yi take yi har bakinta na kumfa ana cikin hakan ne suka ji jiniyar motar 'yan sanda na tashi kamar ana yaƙi wanda yasa duk suka yo waje babu shiri nan kuwa suka tadda Aliyu tsaye a gaba hannunsa a goye a bayansa fuskarsa ba rahma, Abba na ganinsa ya taho da sauri yana fadin.
"Babana..." Abba bai idasa batunsa ba Aliyu ya ce.
"Alhaji munzo kama ɗan ka bisa kamasa da muka yi da manyan laifuka, hakika da zamu kama har wanda yayi bealin shi amma sai dai wanda yayi ba laifinsa bane laifin wanda ya bada bealin sa ne, ka yi min izinin na shige" jin abinda Aliyu ya fada yasa Abba matsawa gefe inda jikin Hajiya Dalah ya dauki rawa, har gaban Faisal Haidar yaje ya daga masa handcuff a fuskarsa yace.
"U are under arrest Faisal Khamis" wani cije baki Faisal ya yi cikin bakinciki idanunsa suna ƙanƙancewa Haidar ya damki hannunsa ya sanya mi shi handcuff yay gaba da shi Hajiya Dalah ta ruɗe ta hauka ce tana bin Aliyu tana fadin
"Dan uwanka ne fa Aliyu Haidar" sai da Aliyu ya sanya Faisal a mota ya dubi Hajiya Dalah yace.
"Ba Aliyu Haidar bane a gabanki, DSP A'K'A ne, ki bar nai aiki ne" yana fadi ya shige mota ashe 'yan jarida suna biye, nan Aliyu ya maida Faisal cell wanda hakan shine mafarin tsana da Hajiya Dalah ta buɗewa Aliyu Haidar.

Tun da Aliyu ya kama Faisal lamari suke jagule masa, bayan kwana biyu da kama Faisal hujjojin da yake dasu na wayoyinsa duk aka goge masa wanda bai san wanda ya aikata masa hakan ba, ba abinda Hajiya Dalah bata yi ba bisa shawarin kawarta Hajiya Basira suka je suka rabawa iyayen yaran kudin akan su janye su ka ce sam su suna tare da Aliyu Haidar, Daga nan suka fara fafutukar sabauta shi amma inaa shima kamar mahaifiyarsa sihiri bai kama shi wanda a sannan ne suka samu nasarar aikinsu akan Basmah wacce lokaci guda dabi'unta ya sauya daga kyawawa zuwa munana daga mai tsafta zuwa ƙazama, daga mai kunya zuwa marar kunya wanda Aliyu ya kasa gane mata wanda wani lokaci ya gwammaci yay zamansa a office akan ya dawo gida, ga matsalolin da suke kunno masa kai a gurin aiki idan ya dawo gida Basmah ta kara da nata, a lokacin ne ake turo da files domin ya cike akai Faisal kotu amma sai a nema a rasa sabida munafukai na kusa da shi.
Wanda har wa yanzu Faisal bai samu beali ba amma Hajiya Dalah ta lashe takwabin salwantar da Rayuwar Aliyu kuma sai ta fito da ɗanta Faisal ta ko wani hali.

   ☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

   _CI GABAN LABARI._

ko da ambulace tazo aka kai Zee duniya asibiti tuni aka shaida mutuwarta, Aliyu kamar zai yi hauka haka ya ji, ransa a mugun bace ya bar asibitin ya koma office yana ta tunanin mafita,wayar ce ta hau ringing da kamar ba zai duba ba sai kuma ya jawo wayar, sunan Dady ne ya bayyana a screen dinsa, rike kai ya yi ya ma rasa idan ya daga me zai cewa Dady? Da alama AIG ya sanar da shi, cikin dauriya ya daga kiran, kan yayi magana Dady yay sallama Aliyu ya amsa a sanyaye, daga can bangaren tausayin Aliyu ne manne a zuciyar Dady inda cikin karfin guiwa da dauriya Dady yace
"Haidar ashe abinda ya faru kenan? Allah ya kiyaye na gaba Allah ya tsare, Allah ya bata lafiya in sha Allah zamu taho gobe amma don Allah karka gayawa Yayarta Sauda, ka yi hakuri ka ji Allah yana tare da mai gaskiya" idanunsa ne suka yi ja, Dady yay masa komai a rayuwa,jin Aliyu ya kasa magana yasa Dady yay masa sallama ya ajiye wayar dan daurewa kawai yayi amma baya tunanin a wannan lokacin Basmah zata rayu....

#COMMENTS
#SHARE
#MomAhan🪄

DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)Where stories live. Discover now