Shafi Na biyu

15 5 0
                                    

"Ni bana so na haihu, Sabida ina tsoron kar yara na su shiga wani hali a dalilin qaddarar rayuwata, na fi so in zauna ni ka'dai sabida nasan ra'da'din da uwa take ji in ta rasa yadda zata yi wurin bama yaran ta kariya, soyayya da kulawa..." NanaKhadija

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Ba mu isa Kaduna ba se gab da magriba kasancewar bayan la'asar muka baro Zaria sannan kuma da yanayin hanya, kai tsaye gidan Kawu da ke Malali muka wuce inda a nan Amaryar sa take wato Anty Bilki. Muna isowa dai dai qofar gidan Kawu ya danna qarar motar sa, shi kuwa me gadi kaman jira yake ya rugo da sauri daga inda yake zaune tare da wasu 'yan unguwa da suke qoqarin yin alwala anan qofar gidan Kawun, gidan Kawu gida ne me madaidacin girma amma a hakan ya samu wani 'bangare daga waje ya fitar da massallaci inda anan yawancin 'yan unguwan suke gabatar da sallolin su guda biyar, duk wanda ya ga massallacin se yayi sha'awan shi  sabida duk da baya da girma ya tsaru daidai ga kuma tsafta wanda hakan ya sa masallatan ke samun duk wata nutsuwa wurin gabatar da sallolin su.

Kawu na shigar da mota Anty Bilki ta fito wurin tarbar abun qaunar nata, madaidaiciya ce me matsakaicin tsayi da kuma farar fata, kallo 'daya zaka mata ka gano tsantsar kyaun ta da kuma hutu da ya zauna a jikin ta, zagayawa tayi saitin da Kawu yake tare da fa'da'da murmushin ta, shima murmushin yayi mata sannan yace mata

"Bilki mun same ku lafia?"

"Lafia lau Dear" ta fa'di sannan ta bu'de mashi qofar na shi, fitowa yayi sannan ya umurce mu da mu fito muma, muna fitowa muka duqa gaba 'daya muka gaida Anty Bilki, a tsarin gidan ba'a gaida Babba a tsaye, duqawa ake yi har qasa sannan a miqa gaisuwa, amsawa tayi a taqaice sannan muka miqe dukan mu, bu'de muna bayan motar Kawu yayi muka kwaso wasu daga cikin kayan mu sabida ba zamu iya 'dauka duka ba dole se munje kai wasu mun dawo, gaba 'daya abunda muka mallaka ne  aka ha'do mu da su inji Mama.

Tunda muka fara fitowa da kayan muna ajiye su Anty Bilki ta tsare mu da ido tana kallon mu, kana kallon fuskanta za ka san irin tsantsar 'bacin ran da ke tattare a fuskan ta, shi ko Kawu ya lura da hakan amma ya qi kula ta ko ka'dan se ma wucewa da yayi kawai ya qarasa cikin gidan, ganin ya wuce ne ita ma ta bi bayan shi amma se da ta tabbatar ta watsa muna harara me sa fa'din gaba, irin wannan kallon da mugaye ka'dai ke yin shi, kallon Jamila nayi na ga ita ma ni take kallo se dai amma ita nata kallon da take mun akwai rashin nuna damuwan hakan da Anty Bilkin tayi muna, ta dai kalle ni ne sabida ta san hali na na gudun tashin hankali, ganin kallon kallon yayi yawa ne ya sa na ce mata

"Mu kai kayan mu dawo mu 'dauki wasu"

Bata ce mun komai ba ta ja akwatin ta da wani jakan nima na ja nawa akwatin muka shiga ciki, tun daga falo ake jiyo muryar Anty Bilki tana ma Kawu magana, maganan da take yi be yi kama da fa'da ba amma akwai tsantsar 'bacin rai da damuwa a muryar ta, tsuru tsuru mukayi a tsakiyan falon sabida rashin sanin inda zamu kai kayan, a tsaye muke babu wadda ta zauna a cikin mu se dai kawai rarraba idon da muke ta yi muna kallon falon, rabon mu da gidan Anty Bilki ya kai kusan shekara uku tun sanda Baba ke raye sabida ba mu cika fita ba kuma in Mama zata zo Kaduna bayan rasuwar Baba da muka koma Zaria ita ka'dai take zuwa, ko da munzo Kadunan ma wurin Uwargidan Kawu Maman Husna ake kai mu sabida anan ne akwai tsarar mu wato 'yar ta Husna.

Fitowa Kawu yayi yana gyara hannun rigar shi da ya 'daga sabida alwalan da yayi, tsayuwar da ya ga munyi ne ya sa yace

"Ahh, wai dama baku shigar da kayan ciki ba? Kar dai tun 'dazu a tsaye kuke"

"Bilki? Bilki? " ya fara kiran ta sannan ya sake komawa cikin 'dakin da ya fito, se da ya kai kusan minti uku sannan ya fito shi ka'dai, Umarni ya muna da mu kwaso kayan sannan ya nuna muna 'dakin da zamu aje su. A haka mukayi ta kwaso kayan namu muna shigo da su har muka gama sannan muka sake dawowa falon muka zauna a qasa, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mun nayi saurin share su sannan na dake, mun kai kusan minti 30 a zaune a haka, Kawu be dawo ba sannan ita ma Anty Bilkin bata fito ba.

Komai  Tsananin Duhu.... (ON GOING)Where stories live. Discover now