Ah yau Thursday, Ilhaam ta shirya tsaf domin zuwa gaishe da Ummi, saidai taqi cin abinci hakan yasa suka zauna suka sha tadi sosai, sai chan Ummi ta yanke shawaran fada mata game da auren Anwaar da Teemerh dan kuwa tasan Anwaar bai fada mata ba "Aya dama nace inaso muyi magana" dan shiru Ilhaam tayi tana tunanin wani magane haka, tasan mey muhimmanci ne duba da yanda tayi maganan "Ummi ae bakomai zamu iya yi" nan Ilhaam ta gyara zama "Inaso kisa a ranki wannan ba shawaran Anwaar bane kuma bazai yi haka dan ci miki mutunci tunda nima bazan barsa ba" kallonta Ilhaam tayi tana tunanin miye kuma ya faru "Na yanke shawaran Anwaar zai kara aure in ya dawo, kuma Fatima 'yar gidan Alhaji Aliyu Shettima nakeso ya aura" sai da Ilhaam takai 2mins kafin maganan ya shigeta, kasacewa komai tayi sai kallonta takeyi kaman statue, wasu zafafan hawaye ne suka sauko mata, still ta kasa yarda da abunda kunnenta sukaji "Teemerh?" Ta maimaita, Ummi ta sauko tazo kusa da ita, sai jin hanun Ummi ah kafadanta kawae tayi amma batasan lokacin da tazo ba "Aya 'yata kiyi haquri ba kuka ya kamata kiyi ah wannan lokacin ba addu'a zakiyi" sai yanzu ta kara tabbatar da abunda kunnenta suka jiye mata "Addu'a?" Ta juyo ta tambayi Ummi hawayen na zuba, gyada mata kai Ummi tayi alamun eh, Ilhaam girgiza kai takeyi cikeda takaici, tunani kawae takeyi dan yanzu ta tabbatar da how worthless she is, banda haka yaushe tayi aure da Anwaar zai mata haka "Nayi nadaman auren Ummi, I know he loves her" ta fada tare da mikewa tsaye zata bar wajen kukanta na kara tsananta "Ilhaam ki tsaya please" Ummi ta tsaida ta, ba musu ta tsaya jin yanda Ummi tayi maganan saidai kukan nata bai tsaya ba "Aya im happy ku kunyi aure, na dade inasan hakan ya faru" kallonta kawai Ilhaam keyi ga wani dizziness from nowhere "Baki tab'a ba" Ilhaam exclaiming without knowing when "Ilhaam karki tsaya kina jayayya da Mamanki, kinsan bazan yi abunda zai cutar da ke ba, Fatima is a good girl nasan zakuyi zaman lafiya" ta fada dan ta kwantar ma Ilhaam da hankali, girgiza kai Ilhaam ta fara sai gata luuu ah kasa, dasauri Ummi tayi kanta taga bata motsi, ah daburce ta fara girgiza ta, Aya, Mamana, saidai ba response, da sauri ta tashi taje fridge ta dauko bottle water nan ta yayyafa mata, ah hankali ta fara bude ido har ta saukesu kan Ummi, sannu Mamana dan Allah ki yafe mun, ta dagota ta rungume, saidai kafin ace mey Ilhaam ta sake sulalewa, hankalin Ummi duk yabi ya tashi, wayan dake a kusa da ita ta dauka da sauri ta shiga kiran Farouq domin yazo ya duba mata Ilhaam, saidai bai dauka ba, he might be busy tasa ah ranta kawae tayi kokarin d'aga Ilhaam suka fita tayi asibitin su Anwaar da ita dan yafi kusa da gidanta "Shareef duba mun yarinyan nan, suman ta uku" kallon Ilhaam yayi dake kwance jikin Ummi "Ina yini Ummi" amsawa tayi sama-sama "Shareef yi sauri, daga fad'a mata kan cewa nace Anwaar ya kara aure fa" kallon Ilhaam in yayi da saurin jin abunda ya sata suman yace ta bisa consultation room "Ilhaam kinasa damuwa a ranki, banda haka wannan issue duk ah hankali za'a samo solution basai ya kai ga haka ba" ya mata bayani "I don't how I ended up passing out Shareef, but no blames I was standing that time" itama tayi nata bayanin "Kinci abinci?" Girgiza kai tayi meaning No "Toh meyasa?" Girgiza kai ta sake "Actually Shareef yanzu ban iya cin abinci, I've no appetite. And if am to force myself I will end up throwing" ta fad'a masa "And you sure you had never suffered from gastroenteritis?" Girgiza kai tayi "Nifa abinci ne kadai ban iya ci sai dizziness, kuma da ae banyi it started recently" kallonta yayi for some seconds, danshi symptoms in pregnancy ta lissafo masa "You will go through some tests" da toh ta amsa ta fita tayi ma Ummi bayani sama-sama, dan tace batajin haushi tayi karya "Toh koh malaria ne?" Ummi ta tambaye ta "Barin yi test in dai" ta fada sannan ta wuce ta zuwa hospital lab, saida ta gama komai and finally the result is sent to Shareef kafin ta koma masa luckily ba patient "Ilhaam you might find this weird, but when last did you see your period?" Kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kai "Wannan month in dai ban gani ba tukun, but may be it was delayed due to-" kafin ta karasa ya tsaidata "Due to what?" Girgiza kai tayi alamun bata sani ba "I am sorry, the result is out" kallonsa tayi sai kuma tayi saurin rike ciki jin hanyan da maganan sa ya dauka "It can't be, tell me am not carrying Aameer's baby" kawae tasa ihu "I am sorry, but yes" ji tayi komai ya tsaya mata "Ilhaam calm down" tace "I shan't" cikeda masifa kaman shi ya mata laifi "Anwaar shouldn't know about this, na shiga uku" haquri ya fara bata ganin yanda take kuka "Ilhaam duk wannan ba abun tashin hankali bane, barin samu Ummi" yana fada ya tashi, kallon mamaki take masa wai ba abun tashi hankali ba, dole yace haka ae tunda su maza Allah ya sa musu rashin tausayi, tana zaune tana kukanta ya dawo "Mey kace mata?" Tayi saurin tambaya "I told her you were having a shock trauma dalilin maganan auren data miki and test in ya nuna komai negative ba malaria ma" ya mata bayani "Meyasa baka fada mata gaskia ba?" Ta tambaya "Actually auren ki was just 2 weeks Ilhaam, koh an fada mata zata gane-" sai kuma yayi shiru "Shifa abokin ka yanzu auren Teemerh zaiyi, the saddest thing yanzu ni bama matan sa bane" shima kansa Shareef Ilhaam ta basa tausayi amma how can he stop the marriage? "Shareef ever since that incident-" sai kuma tayi shiru, tama rasa ya zata masa bayani "Meya faru?" Ya tambaya "Ina mafarki wasu iri" ta fada ah takaice "Ilhaam kinsa abun ah ranki ne, just keep calm ki tuna even the last time was a mistake, hakan bazai sake faruwa ba da yardan Allah. Aameer is a good someone and you know that better than me koh?" Shiru tayi kawae dan yanda Shareef yayi maganan makes her want to believe him "I will rebook your meeting with Dr. Zahra-therapist" yayi assuring nata "Thank you Shareef" ta amsa ah hankali "Ilhaam don't worry komai zaizo da sauki, yanzu kije kar taga kin dade" dakai ta amsa "Ka gaishe da Zoya"... "Ku ae baku zumunci daga ke har shi Anwaar" murmushin dole tayi tace "Zance Anwaar ya kawo ni" yace "In ma baku zo ba mu zamu zo ae" hawayen da taji na kokarin saukowa ne yasa ta tashi ta fita, ya yanke shawaran bazai fadawa Anwaar ba sai ya dawo tunda gobe zai dawo kar hankalin sa shima ya tashi
YOU ARE READING
💖💫RUDANI💖💫
FantasyANWAAR, AAMEER, AAMEEN, AHMAD, TEEMERH, XEENERH, ASHPHERT ILHAAM.