2 months leapDa sauri ta sauko kasancewan tasan ta bata masa lokaci zasu iya tafiya tsaf su barta dan mutunci bai ishi Anwaar ba "Ina kwana" ta gaida Anwaar dake shan coffee "Lafiya lau" ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya ajiye cup in ya tashi dan ya gama, tana ganin ya tashi tayi saurin binsa sukayi waje "Ina Ilhaam?" Ya tambaya dan ya zaci ta fito fa, ware hanu tayi alamun bata sani ba "Sh*t" ya furta sannan ya koma, tana kokarin saukowa hakan yasa bai karasa ba ya jirata "Na bata lokaci koh?" Ta tambaya dan kar yayi fada "No, yanzu zamu tafi, good morning" ya fada da murmushi, amsawa tayi da same expression sannan sukayi waje, basu tsaya koh ina ba sai gidan Ummi "Hop out" ya daka musu tsawa ganin dukkan su kowa na zaune suna jiran queen's treatment, as usaual an rigasu zuwa dan shi Aameer koh wani irin sauri akayi sai an samesa dan bayisan shiririta koh kadan, Aameen na gefe yana waya "Taqaballahu minna wa min kum" Aameer ya fada ganin sun karaso "Eid Mubarak" Ilhaam ta fada da alamun gaisuwa nan aka fara gaisuwa "Malam Abdallah is sending his greetings" Aameen ya sanar dasu bayan ya gama "Guys, why not make some time to go and visit him and the other Malams?" Aameer ya kawo shawara "I am having a busy week" Aameen yayi complain "Toh some other time" kawae aka tsaya a haka sannan su Anwaar karasa palon da suka san zasu samu Ummi dan sune suka zo yanzu, ita dai Teemerh sai wani bata rai take, dan kap dangin Anwaar bata shiri dasu sosai gwanda ma mazan "Ina kwana Ummi" Ilhaam ta fada da murmushi "Lafiya lau Aya, anyi sallah lafiya?" , "Lafiya lau Alhamdulillah, ina kwana" Anwaar ya amsa "Lafiya lau, Allah ya maimaita mana", "Amiin, Amiin" duk suka amsa "Ina kwana" Teemerh finally ta fada "Lafiya lau Fatima, ya sallah?" Tace "Alhamdulillah Ummi"... "Masha'Allah" Anwaar yace "Ummi zamu koma" ya fada yana shafa gashin kansa "Daga zuwa sai tafiya kuma, ba yini za'ayi ba?" Yace "Eh Ummi, ita Ilhaam zata zauna anan, Fatima kuma wai zata gida" ya mata bayani "Toh Baa Adamu yakai ta mana" da toh ta amsa sannan ta tashi ta fita "Kira mun sauran" tayi maganan tana kallon Ilhaam hakan yasa ta tashi ta fita "Ya zaman matan naka?" Shiru yadan yi kafin yace "Lafiya dai Ummi"... "Ban gane lafiya dai ba? Anwaar ban fa ce kayi aure dan ka kuntata wa 'yata ba, yarinya duk tabi ta rame kaman mey damuwa?" Shifa yasan kawae fadan Ummi ya tashi ne, banda haka ae azumi aka gama dole taga change wajen Ilhaam "Ina magana kamun shiru" ta fada ganin bai amsa ba "Ummi Ilhaam tana lafiya, kawae dai tasa damuwan haihuwa aranta ne" ya mata bayani "Aya ma dai da shiririta, haihuwa ae na Allah ne, yaushe ma tayi auren toh" shima dai abunda ya ganin kenan, amma yasan sarai fa she's not going to conceive, she met Shareef at the hospital where he does some scanning and more, kuma ya tabbatar masa Ilhaam can't conceive amma shi bai damu ba dan Allah ke badawa, kuma shi Allah ba ruwan sa da binciken Doctor. Teemerh fita tayi ta musu sallama "Guys ni zan wuce gida, ayi hidima lafiya" Teemerh take fadawa su Aameer "Toh Teemerh, ba yini zakiyi anan ba kenan" Aameen ya amsata "Eh wlh, dake kasan akwae bikin da zamu cikin week in nan shine Mummy tace naje mu shirya abubuwan, amma nima inasan zama" ta masa karya dan ah zahirin gaskia basan zama take ba "Munapuka" Ashphert ta fada kasa-kasa, Aameer kadai ya jita dake shine kusa da ita "Princess, ba kyau zagin wani" yayi whispering "Wai Ummi na neman ku" Ilhaam da fitowanta kenan ta miqa sakon Ummi, Xeenerh ce ta fara tashi nan Teemerh kuma ta fice, palon Ummin duk sukayi, Anwaar na zaune yanda ta barsa, nan duk suka samu waje suka zauna "Toh maganan sadaka ne dama, tunda Allah yasa shekara ya zago muna cikin rayyayu, banji wanin ku yayi magana akai ba"... "Eh Ummi, dake cikin azumi an cire zakka shiyasa da-" tun kafin ya rufe baki ta tsaidasa "Zakka ae ya zama dole ku cire shi Babana" jin hakan yasa Aameer yin shiru da maganan nasa "Akwae malaman ku ah Maiduguri, akwae marasa karfi ma, kuma ba Maiduguri kadai ba akwae different states da mutane ke bukata"... "Hakane Ummi, yanda aka saba za'ayi koh za'a kara?" Anwaar yayi tambayan cikin nutsuwa "Za'a kara, zanyi magana wasu Mahfouz sai susan abunda ya dace a kara, jiya sunzo gaisuwan sallah na manta banyi maganan ba"... "Toh Allah ya taimaka mana" Aameen ya fada cikin ladabi "Amiin, zaku iya tafiya ke kuma Aya ki tsaya" kallon Ummi Ashphert tayi sannan back to Ilhaam, Allah yasa ba wani laifin zata bata ba, fita duk sukayi suka bar mata Ilhaam kaman yanda tace "Aya" ta kirata hakan yasa ta kalleta "Kin tabbata Anwaar bayi miki wani abu?" Kallon ta tayi, in ma yana mata wani abun mey zatayi "Ba abunda yake mun" ta amsa in a low pitch kaman wanda aka sa dole magana, jin haka Ummi ta yarda da maganan Anwaar kan haihu Ilhaam ke damuwa "Kin dai san Allah ke bada haihuwa koh?" Tunda taji haka tasan this is Anwaar's doing, shiru ta mata bata amsa ba dan ita yanzu no one will convince her, ae Ashphert in her second month ta samu ciki, Xeenerh kuma makaranta zata koma shiyasa batayi ciki ba, ita ba karatu ba haihuwa ae bazai yiyu ba "Ina magana kinyi shiru" tace "Nasani" girgiza kai Ummi tayi jin amsan da Ilhaam ta bata
YOU ARE READING
💖💫RUDANI💖💫
FantasyANWAAR, AAMEER, AAMEEN, AHMAD, TEEMERH, XEENERH, ASHPHERT ILHAAM.