Mamuhgee

57 8 3
                                    

Salamu Alaikum.
Hira da Marubutan mu zango na farko tare da babbar baƙuwarmu,wanda ni Oum Mumtaz zan jagoranta a yau (Monday, Oct 9.)

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *A madadin masu sauraro,ina miki Barka da zuwa babbar baƙuwar mu!.*

Mamugee: Aslm alailkm
Barka ngd

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Ko za mu iya sanin sunan baƙuwar tamu?*

Mamugee: Maryam sani Gummi
Amma da mamuh nafi sabawa sbd shi ake Kirana dashi ko a gida.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Masha Allah
Muna miki barka da zuwa Maryam ko kuma ince Mamuhgee! Lallai yau mun yi babban kamu.

Mamugee: Yawwa thank yo.u

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *A takaice cikin kalmomi da basu haura dari biyu ba wacece Mamuh?*

Mamugee: Mamuh yar haifaffiyan zamfara ce,Inada aure da haihuwa
Nayi karatu na har matakin degree
Shine abinda kawai zan iya cewa🙏

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Masha Allah
Ubangiji Allah ya raya zuri'a yayi jagora.  *Bari mu tsunduma cikin shirin namu gadan-gadan. Shin mallama Mamuh A wace shekara ki ka fara rubutu? Wanne ne littafin ki na farko? Me yaja hankalin ki,ki ka rubuta littafin ki na farko? Daga farkon fara rubutunki kawo yanzu shin littafai nawa ki ka rubuta? Wanne ne yafi baki wahala? Wanne ne ya ɗaga darajarki a duniyar marubuta har aka san da Mamuh? Shin wanne ne yafi baki wahala?*

*Lissafo mana sunan littafan da ki ka rubuta?*

Mamugee: Yawan karance karance yaja raayina ga fara rubutu,
Na fara a 2016 a think,Littafina na farko DAIMAN,Zuwa yanxu a qalla inaga na rubuta books da zasu Kai 17 zuwa 20 ma kila,
Nafi Shan wahala a rubuta littafin Tarayya sbd abubuwan dayaxo dashi a cikinsa,Littafina na farko kusan gaskia shine ya fara dagani daga kansa Kuma gaskia alhmdlh duk littafin danayi Yana samun karbuwa sosai.

Daiman
Zuciyarmu Daya
A duniyarmu
Taura biyu
Auren raba gardama
Dacewa
Dawood
Tarayya
Eznah
Buri Daya
Kaunarmu
Min qalb
Deen marshall
Ubayd maleek
Noor Albi
Inayah
Idona nera
Zafin Kai.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Ashe dai da tsohuwar marubuciya muke tare a nan tunda ana batun shekara 7 baya kenan da fara rubutunki! Menene littafin tarayya ya kuntsa da yasa yafi baki wahala yayin rubuta sa? Me littafin Da'iman ya kuntsa a taƙaice?*

Mamugee: Labarin Tarayya labari ne na sarauta da fitintinun dake cikinta wainda suka hada da tsafi,cin Amana,buri da qwallafa Rai a kan son haihuwar 'da namiji Wanda daga karshe sarautar ta koma hannun mace.To yanayin yanda ya hada wainnan abubuwan da yawa dakuma kasancewar akan al'ada da rayuwar Ethiopia nayisa ya sakashi ban wahala gaskia. Daiman Kuma labarine na yanda wasu ke tagayyara rayuwar marayu da son zuciyarsu.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Shin wani ƙalubale ki ka taɓa fuskanta a dalilin rubutu?*

Mamugee: Qalu bale Kuma baifi irin wainda sauran marubuta ke samu ba daga masu karatu ta hanyar fadan maganganu marasa dadi da cin fuska.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Daga Fara rubutunki zuwa matakin ɗaukaka,Shin kin taɓa shiga ƙungiya? Wacce?*

Mamugee: Eh na taba har so biyu
Na taba zama real Hausa fulani writers kafin na zauna a Haske writers.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Shin labaran ki sun raja'a ne akan labarin da ya faru a gaske ko kuma ƙirƙirarren labarai ki ka fi yawan ta yi?*

Mamugee: Kusan duka na kirkira ne na gasken Basu fi guda uku ba.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *A ɓangaren karance-karance littafi,wani littafi ki ka taɓa karantawa? A marubutan mu na baya wacece take birge ki? A marubutan online wacece tafi birge ki?*
*Faɗa mana marubutan da ki ka sani guda Shida.*

Mamugee: A Baya nayi karatu sosai gaskia,Amma Ina fara rubutu na fara Denawa yanzuma Kam kwata kwata na Dena bana iyawa ko naso so bazan iya cewa ga wainda na karanta ba gaskia,A marubutan Baya sa'adatu waziri gombe da sumayya takori sune best dina.
Online writers Kuma
Zinnyta
Huguma
Billy
Rano
Xoxo.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Wai miyasa marubuta da dama suke faɗin a baya sun yi karatu amman idan suka fara rubutu yake ja da baya?

Mamugee: Kana zama marubuci Wani labarin kana fara karantawa zaka funskaci inda ya dosa saika ji Kuma to meya rage💔😂😂nawa thought din kenan fa.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Da wannan ma saboda kusan duk tunanin mu akan abu guda yake sakamakon muna rayuwa a nahiya guda.  *Wace shawara za ki iya baima tsofi har ma da sababbin marubuta?*

Mamugee: Suyi hakuri su Ara karfin zuciya daga abubuwan da zasu fuskanta.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Wace shawara za ki iya baima marubuta ƴan uwanki masu rubutun batsa da suke sawa ana ma dukkan marubutan yanzu kallon kamar duka haka muke?*

Mamugee: Allah ya shiryasu kawai harma damu gabaki daya.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Wani uzuri za ki baima fans ɗin ki na idan sun ajiye miki saƙo basa samun attention ɗin ki a dai-dai lokacin da suka fi buƙata sai daga baya a lokacin da suka fidda tsammani?*

Mamugee: Uzuria shine yawanci bana kashe data koyaushe a kunne take sai idan ba caji ne so shiyasa ana Turo Sako yake shigowa sai a dauka kaga sakon baka bude bana bayan Kuma gaskia bama lallai wayar na hannuna bane may be tana aje Ina can gurin Wani aikin so saina nutsu nake bin chats su ringa uzuri please abubuwan da yawa.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Wani abinci Mamuh Tafi so?*
*A abin sha fa?*
*Wace kalar sutura ki ka fi yawan amfani da shi?*

Mamugee: Inason abinci mara nauyi sbd inada kiba inason ragewa😂😂
Drink Kuma any drink dayake da lemon. Sutura Kuma dogayen riga.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Wani albishir ki ke da shi zuwa ga masoyanki masu bibiyan labaran ki?*

Mamugee: Suci gaba da bibiya bazasu Dana saniba.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Kafin kiyi sallama da masu bibiyarmu! Ki faɗa mana sunayen kafofin ki na sada zumunta ta yanda masoyanki za su iya tuntuɓar ki kai tsaye?*
Wattpad,Facebook,Arewabook,IG,Twitter,Tiktok?

Mamugee: Wattpad: Mamuhgee,
Facebook: maryamgumi,
Arewabooks: Mamuhgee,
IG: mamuhgummy
Bana Twitter
TikTok mamuhgummy.

Oum Mumtaz ce🤙: *Shin masoya za su iya kallon hoton Mamuh saboda kada wata rana tazo ta wuce ba tare da sun san cewa ita bace?*

Mamugee:

Oum Mumtaz ce🤙:  Masha Allah so beautiful! *Shin kina ɗaya daga cikin mutanen da in aka musu ba daidai ba suke fitowa social Media wajen maida martani?*

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.


Oum Mumtaz ce🤙:  Masha Allah so beautiful! *Shin kina ɗaya daga cikin mutanen da in aka musu ba daidai ba suke fitowa social Media wajen maida martani?*

Mamugee: Banayi Bantaba ba.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Masha Allah! Duka-duka a nan muka kawo karshen hirar mu tare da babbar baƙuwar mu! Fatan Allah ya maida ke gida lafiya ya kuma sake sawa mu samu damar sake gayyatar ki,ki amsa ƙira.*

Mamugee: Amin ya Allah ngd.

End!

Za ku iya comments akan abin da ya shige muku duhu wanda idan har da naji tambayoyi masu ma'ana zan sake gayyato muku ita domin kuji amsoshin tambayoyin ku! Ko kuma ku faɗi sunan marubuciyar da ku ke son ayi hira da ita next insha Allah za mu naimo ta saboda farin cikin ku.

*Ku kasance tare da ni Fatima Adamu Fate, wacce aka fi sani da OUM MUMTAZ,domin ganin da wace marubuciya za mu tara a gaba da yardar Allah!*

*Domin neman ƙarin bayani ko kuma bayar da shawara ku tuntuɓe Ni a kan lamba ta,ta WhatsApp banda kira!  09061794195*

Bissalam!

HIRA DA MARUBUTAN MU.Where stories live. Discover now