Maman Maama

27 4 0
                                    

Salamu Alaikum.
HIRA DA MARUBUTAN MU zango na biyu tare da babbar baƙuwarmu, wanda ni Oum mumtaz zan jagoranta a yau (Mon,oct 16, 2023).

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: A madadin masu sauraro ina yi ma baƙuwar mu barka da zuwa, Bismillah kiyi sallama ga masu sauraro.

Maman Maama: Assalamu alaikum wa rahmatullah. Barkan ku da wannan lokacin.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Yauwa barkan mu dai! Ko za mu iya sanin sunan baƙuwar tamu?

Maman Maama: Sunana Maman Maama.

Oum Mumtaz ce🤙: A taƙaice wacece Maman maama?

Maman Maama: Maman Maama sunanta na gaskiya Nafisa, an haife ta ta kuma girma tayi karatun muhammadiyya a garin Kano, tayi karatun secondary da digiri ɗin farko a Jigawa State, digiri na biyu kuma a Kano state. A yanzu tana aiki kuma tana aure a Jigawa State, tana kuma karatu a Kano state, tana da yara uku. Nagode.

Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Madalla da Maman maama lallai keɗin ta musamman ce kuma a yau ɗin mun yi babban kamu! Bari mu tsunduma cikin shirin namu gadan-gadan. Shin Maman maama A wace shekara ki ka fara rubutu? Wanne ne littafin ki na farko? Me yaja hankalin ki,ki ka rubuta littafin ki na farko? Daga farkon fara rubutunki kawo yanzu shin littafai nawa ki ka rubuta? Wanne ne yafi baki wahala? Wanne ne ya ɗaga darajarki a duniyar marubuta har aka san da Maman maama? Shin wanne ne yafi baki wahala?*
*Lissafo mana sunan littafan da ki ka rubuta?*

Maman Maama: Okay. Da farko dai na fara rubutun novels ne a shekarar 2018, littafi na na farko kuma sunansa Maimoon. Abinda ya ja hankali na kan rubutu shine yadda naga mutane musamman mata sun mayar da hankali sosai wajen karance karancen littafan hausa, sai naga cewa rubuta littafi kamar wata hanya ce ta musamman da mutum zai yi amfani da ita dan ganin ya isar da wani sako zuwa ga mutane cikin sauki.
Daga 2018 zuwa yanzu na rubuta novels guda biyar, Maimoon, A'isha Humaira, Diyam, Tagwaye da Jidda.
Littafin da yafi bani wahala a gurin rubutu shine Tagwaye, saboda shine paid novel dina na farko, na rubuta shi cikin pressure na hakkin mutanen da yake kaina ina tsoron kar in mutu ban gama musu ba. Sannan kuma ga labarin yana da tsaho. But ut turned out to be the most epic novel ever written by me😊
Batun daga daraja zan iya cewa Maimoon, shine littafin da yafi suna kuma shine littafi na na farko, da shi aka san sunana.

Oum Mumtaz 🤙: Lallai an jima ana gwagwarmaya! Bamu kaɗan daga cikin littafin Maimoon na abin da ya ƙunsa!
Bamu kaɗan daga cikin littafin tagwaye na abin da ya ƙunsa!

Maman Maama: Littafin Maimoon an gina shine akan soyayya, yadda karfin ta yakan iya chanja komai. Babban darasin dake cikin littafin Maimoon shine "do not judge a book by it's cover" yadda muke kallon abu a lokuta da dama ba haka yake ba.
Labari ne akan yarinta Maimoon, yar masu kuɗi, yar gata, kyakkyawa mai tarbiyya da sauransu, tasha wahala akan soyayyar wani bayarabe da tayi tunanin mahaifinta ba zai yarda da haɗin su ba, daga baya kuma sai shi baban nata da kansa ya ce ta nemo shi ya aura masa ita, lokacin shi kuma ya tafi neman kuɗi dan shima yana tunanin iyayenta ba zasu aura wa talaka yar su ba. A lokacin da take tsakiya da kewar sa sai ta samu labarin har yayi aure ma, shi kuma a nasa bangaren yayi auren ne saboda ya samu labarin itama anyi mata aure dan a raba ta dashi. Wanda hakan makircin kawarta ne
Daga baya kuma sai ta hadu da wani lalataccen dan sarki wanda yayi suna a kasa baki daya akan rashin tarbiyyar sa da munanan dabiun sa, ta fara kula shi da niyyar tana so ta karanci halayyar sa dan ta rubuta wani "project" dinta na makaranta a kansa, daga baya kuma sai ta fahimci he has the purest soul data taba gani a duniya, mutumin kirki ne shi sosai, wannan yasa ta fada son sa, suka sha wahala sosai kafin iyaye su yarda, auren nasu da kuma dawowar wancan tsohon saurayin nata ne ya bude wani babban shirrin da ya chanja rayuwar mutane da dama.

Littafin tagwaye an gina shine akan banbance banbancen halayya irin ta dan Adam, yadda koda Tagwaye masu kama daya sukan zama masu banbancin halayya.

littafin tagwaye an gina shine akan rayuwar wasu yan biyu guda biyu, maza Hassan da Hussain, da mata Ruqayyah da Sumayya. Inda Allah ya bawa Hussain daukaka ta dukiya sosai tun lokacin samartakar sa, ya kuma azurtashi da auren yar sarki. Shi kuma Hassan mutum ne shi mai gudun duniya, mai takatsantsan da komai da rayuwa sai kuma Allah ya jarrabeshi da auren Ruqayyah.
Ruqayyah da Sumayya identical twins ne, ita Sumayya tana da hali kusan irin na Hassan, yayin da ita kuma Ruqayyah ta kasance mai matukar son abin duniya, mai raina iyayen su saboda talaucin su, mai dogon burin da yafi karfin tunanin mai  karatu. Sai kaddara ta haɗa ta da Hassan, ita kuma sai tayi tsammanin shine Hussain mamallakin kamfanin "H and H group of companies" wannan yasa ta yaudare shi har ya fada soyayyar ta kuma ya aure ta, sai bayan auren ne sannan ta fahimci cewa ba shine mai kuɗin ba, asali ma shi maaikaci ne a kamfanin danuwan nasa. Sai dai kuma shi din dan uwane magaji daya tilo ga mai kuɗin da Allah bai bawa haihuwa ba, wannan yasa ta kudiri aniyar ganin sai ta mallaki wannan tarin dukiyar da kullum take ta kara hauhawa, ko da kuwa zata rasa komai nata, koda kuwa zata rasa kowa nata, idan tace kowa tana nufin kowa har mijinta, yayanta, iyayenta da kuma yan'uwanta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 16, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HIRA DA MARUBUTAN MU.Where stories live. Discover now