Salamu Alaikum.
HIRA DA MARUBUTAN MU zango na biyu tare da babbar baƙuwarmu, wanda ni Oum mumtaz zan jagoranta a yau (Tue,oct 10, 2023).Oum Mumtaz Ce🤙🏼: A madadin masu sauraro ina yi ma baƙuwar mu barka da zuwa, Bismillah kiyi sallama ga masu sauraro.
Nana Haleema: Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuh.
Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Wa alaikassalam.
Barka da zuwa baƙuwar mu.Nana Haleema: Barka dai ina godiya.
Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Ko za mu iya sanin sunan baƙuwar tamu?
Nana Haleema: Suna na Haleema Khabir wacce aka fi sani da Nana haleema.
Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Ah! Lalle yau mun yi babban kamu! Munji matuƙar daɗin kasancewa tare da ke Nana Haleema! A taƙaice, cikin kalmomin da basu haura ɗari biyu ba wacece Nana Haleema?
Nana Haleema: Nana Haleema dai haifaffiyar garin kano ce tayi karatun primary da secondary a kano. Na kammala diploma health technology ina aiki da primary health care sannan ina business na siyar da abinci a social media. A yanzu kuma na ina gab da shiga makarantar koyar da aikin unguwar zoma wato midwifery.
Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Masha Allah mallama Haleema lallai kice yau tare muke da hamshaƙiya da ta ƙware a fannin girke-girke! Kuma likita sannan kuma marubuciya!
Nana Haleema: Tabbas kuwa😅
Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Shin ta tayaya mallama Haleema take tafiyantar da tafiya wurin aiki! Sana'ar abinci ga kuma rubutun Littafi! Shin babu abu ɗaya da yake shiga lokacin ɗaya?
Nana Haleema: Gaskiya babu na tsara komai ne dan ganin ban shiga hakkin ko wanne ba. Bana yin abinci yawanci sai weekend ko kuma in ina off a wajan aiki. Shi kuma typing nafi yin sa a duk sanda na samu lokaci koda a wajan aiki ne indai na samu free time na zauna zanyi rubutu dan baya bani wahala gaskiya.
Oum Mumtaz Ce🤙🏼: *Madalla da Haleema lallai keɗin ta musamman ce! Bari mu tsunduma cikin shirin namu gadan-gadan. Shin Nana Haleema A wace shekara ki ka fara rubutu? Wanne ne littafin ki na farko? Me yaja hankalin ki,ki ka rubuta littafin ki na farko? Daga farkon fara rubutunki kawo yanzu shin littafai nawa ki ka rubuta? Wanne ne yafi baki wahala? Wanne ne ya ɗaga darajarki a duniyar marubuta har aka san da Nana Haleema? Shin wanne ne yafi baki wahala?*
*Lissafo mana sunan littafan da ki ka rubuta?*Nana Haleema: To na fara rubutu a shekarar 2017 zuwa 2018. Karance-karance na labaran Marubuta shine ya bani sha'awa ya kuma saka min shaukin son rubutu ba tare dana shiryawa hakan ba. Tun kafin labaran online ina karanta littafan takarda na tsoffin marubuta sosai. Littafina na farko sunan sa BAN AIKATA BA. daga farko zuwa yanzu na rubuta labaran goma sha uku kenan ina kan rubuta na sha hud'u.
Gaskiya wanda yafi bani wahala kwantan b'auna ne wanda nake yi yanzu, ban tab'a labarin sarauta ba sai a kansa, kin san labaran sarauta kuma sai ka tsananta bincike kar kaje kayi wani abun ba daidai ba duk da nasan abubuwa da dama na sarauta dan muna da sarauta a gidan mu. Sannan ban taba labari mai yawan sa ba shiyasa nake jin wahaalr rubuta shi.
Wanda ya saka aka sanni Saudala ne labarin barkwanci da ban dariya ni kaina in na tuna ina dariya sosai yayi farin jini a zamanin sa sosai. Sai kuma Mugun nufi ya kawo min masoya wanda ban san adadin su ba.Ban aikata ba
Saudala
Rayuwar fateema
Yancin mata
Dukiyar marayu
Masoya uku
Zuciya ce
Makaho ne
Sirrin zuci
Muwaffaq
Kasaitar so
Zanen zabuwa
Mugun nufi
Kwantan b'auna.Oum Mumtaz Ce🤙🏼: Lalle muna tare da tsohuwar hannu a tunda ana maganar shekara 5 zuwa 6 ana fafatawa!
Nana Haleema: Tun muna jarirai😂😂
YOU ARE READING
HIRA DA MARUBUTAN MU.
FanfictionShiri ne da zai baima makaranta damar zaben ko wacce marubuciya da suke son ayi hira da su,a manjahar Wattpad tare da ni Fatima Adamu Fate (Oum Mumtaz) Domin ganin da wace marubuciya za mu fara hirar tamu sai kuyi following ɗina sannan kuyi comments...