1

312 49 6
                                    

Dedicated to Zeenatu Muhammad Lawal of blessed memories....

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

WA'ADI
✍🏾SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

                1.

"LIKULLI AJALIN KITAB."
                      _Ayar Ƙur'ani

Zaune take gaban madubi ta yi ƙuri tana wa kanta kallon ƙurilla, so take kawai ta hango makusarta, dan dai ta san fuska ita ce farkon abin da ke ɗaukar hankalin mai duba, mutum gaba ɗaya a fuskarshi yake, dan ma su iya magana ma kan ce "kyawawa ba sa kwantai". Hakan ya sanya ta ƙurawa hasken fatarta ido, hasken da ta taso tana ji ana koɗawa, so take ta gano inda hasken ya dusashe ko ya munana amma ta kasa ganewa, hakan ya sanya ta sauke idanunta a cikin takwarorinsu da ke cikin gilashin madubin, suna nan dai da girmansu cikin zubi mai kyau da ƙawayenta kan kira da 'golden eyes'. Tun da suke faɗa mata kawo yanzu da take nazarin su ba za ta ce ga wani gwal a cikinsu ba, amma dai ta aminta suna da kyau.

To ta yiwu ko hancinta ne dalilin, dan dai bai da tsawo ko tsinin da zai kamanta ta da matan Indiya, amma kuma ya ƙawata zagayayyiyar fuskarta da ɗan mitsilin bakinta, da laɓɓanta masu ɗan tudu kaɗan, hakan har ya sanya ta cikin kyawawa.

“Ko zan yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, Zinatu kina da kyau!" Ta samu kanta da faɗin ta cikin mudubinta hakan. Hakan ya sa ta ɗauki audugar da take shafa hoda da ita ta barbaɗawa fuskarta, ta ɗan taje gashin girarta da burushi, ta ɗakko ta kwalli ta zizarawa idanunta, duk da ita ba wata ma'abociyar sanya kwalli ba ce, amma tana ji yau ya cancanta ta sanya, ko ba komai tana yawan ji ana cewa yana ƙara fito da kyawun mace. Sai da ta gamsu cewa komai ya yi daidai a fuskarta sannan ta yinƙura ta miƙe, har a lokacin zuciyarta cike da tambayar (ko tuhumar ) wai har sai yaushe?!

Lefen ƙanwarta za a kawo, tun safe suke hidimar ɗaurawa da saukewa dan a fita kunyar matan da za su kawo lefen. Tun da ta miƙe assalatu take hidima, ita ce wannan ita ce wancan, ba ita ta zauna ba sai yanzu kusan sha biyun rana da ta yi wanka, shi ma da ƙyar ta zame jiki saboda ganin lokaci zai ƙurace idan ta biye ta aikace-aikacen, tana kammala gyara fuskarta ta fito dan ta ƙara tabbatar da komai ya tafi daidai.

“Mom, zan ci donot dan Allah, kin ga sun hana ni." Faɗin yaron da ba zai wuce shekaru takwas ba, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci kamannin da suke yi da ita, sai dai shi baƙi ne. Sabir ke nan ɗan gidan Yaya Ahijo, koyaushe yana maƙale da ita, ta zame masa ƙaramar uwa, komai nashi yana wajenta.

"A'a! Babana, zo mu je mu ga in ba su rufe ba." Ta ce tana mai kamo hannunsa, har sun wuce ƙofar wani ɗaki ta ji an ambaci sunanta, hakan ya sa ta ja ta ta tsaya dan ta tantance kiran ta ake ko a'a.

“E wallahi Jummai, shekarar da Zinatu ta kammala karatun sakandire shekarar aka haifi Sadiya, kun ga ga shi har auren Sadiyar ya tashi ta bar ta." Muryar gwaggonsu ce, baƙin ciki da nadamar tsayawa ne ya daki zuciyarta yayin da ta sa ƙafa ta bar wajene cikin sauri cike da ƙunar zuci.

Ɗaki ta koma, ranta a cunkushe, har ta manta donot ɗin da za ta ba yaro Sabir. In da za ta samu damar yin tambaya kuma ta tabbatar da za ta samu amsa da tambaya za ta yi shin wane laifi ta yi wa Allah da ta ke kwasar jarrabawa haka? Amma sai dai ina! Babu halin yin tambayar, tuna tambayar ma wata siga ce ta saɓo hakan ya sanya ta saurin fara yin istigfari, ba wai dan zuciyarta ta saduda da son neman tambayar ba, sai dan hakan ne kaɗai abin da aka gina rayuwarta a kai.

“Wanda Allah ke so shi yake jarabta." Ta tuna zancen yayansu wata rana da ta same shi da zancen ya nema mata miji a cikin abokansa.

“Zinatu ki gode ma Allah, mu da aka yi aurenmu da yarinta, yanzu mazajenmu wayau kawai suke mana." Ta tuna aminiyarta, lokacin da ta zo mata da ƙorafin mijinta ya cinye mata kuɗinta na gado.
To me ya fi buƙatar ruhi? Ai ko feɗe mata fata miji zai yi, ita kam tana so ta gan ta da wanda za ta kalla har ta nuna ta ce mijinta ne.

WA'ADI Where stories live. Discover now