14.

192 34 20
                                    

14.

AMMAY YUJIBUL MUDƊARRA IZA DA'AHU WA YAKSHIFUS SU'A
(Shin ba shi ba ne yake karɓawa mai buƙata idan ya kira shi, kuma ya yaye masa cuta....)
                -Ayar Ƙur'ani

Gaba ɗaya lulluɓe ta ya yi kamar kazar da ke son kare 'yan tsakinta daga ruwan sama, hakan ya taimaka masa wajen isar da saƙonsa. Ba zai ce ya taɓa alfahari da surarsa kamar lokacin ba. Yadda abin ya zo wa Zinatu a bazata haka ƙwaƙwalwarta ta tafi yajin aikin wucin gadi, so take ta ji yadda ake ji in hakan na faruwa amma ƙwaƙwalwarta ta ƙi ba ta wannan haɗin kan. Kai tsaye ba za ta ce ga taƙamaiman yanayin da take ciki ba, wani tsoro da firgici ke neman rufe ta, ga kuma wani abu, wani sabon yanayi mai wuyar fassarawa, hakan ya sanya ta runtse idanunta gami da ƙara takurewa jikinshi, ta bar shi da yin kiɗa da rawarshi. Abu ɗaya da za ta iya ƙararwa, ko ma me yake mata jikinta ba ya so ya daina, amma zuciyarta na mata kururuwar dakatar da shi, to amma ta yaya?

Kamar wadda aka tsikara Rauda ta saki kuka mai ƙarfi, hakan ya sa Sharhabilu miƙewa ba shiri yana gyara jikinsa, shi ya yi ƙarfin halin ɗaukar ta, dan Zinatu na daga kwance inda ya bar ta ido a rufe. Minti biyu ya ɗauka yana ƙare mata kallo, zaninta da ya yaye yana bayyana hasken katararta, ya durƙusa ya sa hannu ya rufe mata kamar wanda ke tsoron kar wani ya gane masa ita a wannan yanayin bayan shi. Murmushi ya saki yana jin wata irin annashuwa yayin da yake jijjiga Rauda a hankali saman kafaɗarsa, yadda yake jin kansa kamar mai yawo a saman gajimare, murmushinsa ya ƙi tsayuwar. Ya fara rerawa Rauda waƙar tawai da yake yawan ji Yaya na rerawa jikokin gidan idan tana rainon su.

"Ina uwar 'yar nan ne,
Ta tafi rafi,
Ta ɗebo ruwa,
Ta dawo gida,
Ta ba ta mama,
ta sha ta ƙoshi.

Rera waƙar yake cike da annashuwa, sam ya manta da kiran Momma da tashin hankalin da yake ciki, kawai jin sa ya ke daga shi sai Zinatu ne kawai a doron ƙasa, sai kuma 'yar jaririyarsu Rauda.

Ita ma Zinatu da ke kwance ido rufe jin ta take lulluɓe da shauƙi, yanayin yadda ƙirjinta ke bugawa, tana jin Sharhabilu na ratsa ta, wani shauƙi da ba za ta iya faɗin ko na mene ne ba, ta dai san ba soyayya ba ce dan ba ma zai yiwu ba, to ta ina ma hakan zai zama soyayya? Ta haɗa mishi karin kumallo duk safiya ko ta zaman taɗin da suke yi na 'yan mintoci? Ko kuma wannan wutar shauƙin da ke kunnuwa duk san da ya raɓe ta?

Haka ta dinga zantawa da zuciyarta har ta ji shi ya ajiye Rauda ya fita, sai a lokacin ta tariyo abin da ya wakana, sai samun kanta ta yi da murmushi tare da jan alhamdu lillah!

***
Sai da ya sanya haƙarƙarinsa a kan gado sannan ya tuna da kalaman Momma, ko da me za ta zo da shi? Shiru ya yi cike da damuwa, ya saƙa ya kwance har bacci ɓarawo ya yi awon gaba da shi.

Washegari bai faɗawa kowa zuwansu ba, tafiya ce miƙaƙƙa daga Bauci zuwa Kaduna, ya san in sun yi sauri ne su iso da La'asar, hakan ya sanya ana ƙarfe uku ya kashe wayoyinsa ya fice daga gidan ba tare da ya yi sallama da kowa ba, shi tsoron sa kar son rai ya sanya Momma kifar da tulun mutuncinta a idon waɗanda suke ganin ta da mutunci da ƙima.

Yadda bai faɗawa kowa zancen zuwan ba ya sanya mutan gidan bayyana mamakin ganin su.

"wai sai baki faɗa musu zuwanmu ba" Alhaji Mamuda cikin ɓacin rai, sai da ya tambayeta kuma ta faɗi masa sun san har da dalilin zuwansu.

Kallon shi ta yi sannan ta kau da kai gefe. Ranshi ya ƙara ɓaci amma ya dake. Ƙarar da wayarta ta yi ne  ya sa ta ɗaukar wayar da fita waje. Bayan ta gama amsa wayar ta shigo fuskarta cike annuri, sai ta ce masa
"Alhaji har sun iso, bari na shigo da su." Tana gama maganar ta fita cikin sauri, ta bar Alaramma, da su Yaya cike da wasiwasin ko su waye. "Wasu ne suka ga hoton 'yar wajen su Sharhabilu, sun ce danginta ne."

"Alhamdu lillah!" Gwaggo da Inna suka faɗi a tare, fuskarsu na bayyana farin cikin da suke ƙoƙarin danne shi a zuci.

"Amma sai kuka yi shiru Alhaji." Faɗin Alaramma, zuciyarsa na karyewa.

WA'ADI Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang