10

119 34 6
                                    

WAMA BIKUM MIN NI'MATIN FAMINALLAH
(Kuma dukkan abin da ke gare ku na daga ni'ima, to daga Allah yake)
                _Ayar Ƙur'ani

Aliyu bai taɓa sanin Yaya ta iya irin soyayyar uwa da ɗa irin wadda can da suke gani a finafinan indiya ba sai yau, kawai sai ganin Yaya ya yi a matsayin "Mother India", wasan kwaikwayon da tsabagen kallonsa sai da suka haddace dukkansa. Kafin a yi wani abu za su ruɗe kowa na sowar "yanzu za ai kaza! yanzu za ai kaza!"

Sallamar Alaramma ne ya sa duk suka kalli ƙofar shigowa ɗakin. Tunda Zinatu ta tashi za ta iya rantsuwa wannan ne karo na uku da ta taɓa ganin Alaramma ya taka ɗakinsu, tun ƙuruciyarta, 'yammatancinta, ba ma ita ba, har zamanin yayyunta har aka zo lokacinta, kuma ban da wannan, duk sauran ma dan ita ne, lokacin da take jinya.

Takowa ya yi har inda take duƙunƙune jikin Yaya, yakai hannu ya taɓa kanta sannan ya ce.

"Zinatu kin ga wa'adi ko?"

Yadda Alaramma ya ga ta tsare shi da ido fuskarta na bayyana tsoro da ruɗu ya sanya shi jin matsanancin tausayinta ya dabaibaye shi.

“To mene abin kuka kuma?" Ya ce yana share mata hawayen da ke zubo mata.

"Babana don Allah ka warware auren nan ba na son shi!"

"Me ya sa ba kya son shi?” Ya ce mata cikin nutsuwa yana kallon ta cikin ido.

"Baba ya min yaro, Sannan ni ba ma irin mijin da nake so ba ne." Ta ce kanta tsaye, babu ko ɗar cikin muryarta.

Murmushi Alaramma ya yi yana mai girgiza kanshi, Aliyu kuwa baki ya saki yana mai ji kamar ya kamata ya yi ta duka dan takaici. Har zai yi magana Yaya ta riga shi.

"Ke kin taɓa kallon kanki a madubi? Ko kin taɓa zama kin tambayi kanki me ya sa kika gagara samun mashinshini? Duk ma ba wannan ba, an ce miki ita mace na da zaɓi ne da ya wuce nagartacce,.wanda zai zame mata garu mai ƙarko. Faɗa min cikin 'yan'uwanki in akwai wanda ya kai shi nagarta?" Duka wannan maganar Yaya ta yi ta ne cikin hasala da ƙufula, bayan ta zame jikinta daga nata.

"Yaya ban da zancen wanda ya kai shi, ko ni na fi shi ai." Aliyu da ke gefe ya yi caraf ya tsoma baki. Saukar ranƙwashi da ya ji ya sa shi kallon Alaramma. Hanya ya nuna masa da yatsa ya fice daga ɗakin.

"In ban da abin ki Zinatu, kina tunanin za ki yi haƙuri ki tsare kanki, ba wai kuma kin yi gaggawar zaɓi ba kuma Allah ya ba ki wanda ba shi kike buƙata ba? Ai shi Allah ba ya saɓa alƙawari kuma ya yi ma mai haƙuri alƙawura da dama. Ki ƙaddara wannan ne sakamakon da ya tanadar miki na haƙuri da tsare kanki da kika yi. Ga mahaifiyarki nan sheda, ban taɓa amsar sadaki mai yawan naki ba, ƙarin daraja ba da sulalla ko takardar kuɗin Nijeriya ba, da dalar Amurka fa! Godiya ce kawai ai ke yanzu da za ki ma Allah, ba wai ina fifita kuɗi ba ne, amma haka Allah ke al'amrinsa, wanda ake ganin bai isa ya kai ba se Allah ya sa ya kai har ma ya wuce.”

"Ai da ka bar ta, wai tsaya ma, ni da ubanki an ce miki zaɓi aka ba mu? Amma da yake mun san ibada za mu yi, a tafiyar soyayyar ta zo, mai tsafta da inganci fiye da wanda kuke iƙirarin yi  a yanzu. Wallahi na sake jin bakinki se na saɓa miki, shashasha wacce ba ta san kyautar Allah ba!" Yaya ta sunkumi Rauda ta fice ta bar Alaramma na ci gaba da ba ta baki da nasiha a kan tarin girman da ya hau kanta.

"Da za ka taimaka min ni dai da ka warware auren nan Babana" Zinatu ta ce cikin kuka. Har cikin ranta ba ta son auren da aka ƙaƙaba mata, ita gaba ɗaya ma ba ta ma shiryawa kowane irin aure ba.

"Ko da wasa na ji labarin ba ki sauke haƙƙoƙin da Allah ya ɗaura miki na matar aure ba sai na yi matukar saɓa miki, kin ji ni ko!" Ya faɗa a kausashe, sannan ya fita ya bar ta tana kuka.

Ko tsakar gida ba ta fita ba, wani zazzaɓi ta ji ya saukar mata, haka dai ta ƙudundune a gado bayan ta sallaci La'asar. Kiran sallar Magariba ne ya sa ta tashi.

Tana raka'a ta biyu ta jii sallamar Sharhabilu daga bakin ƙofa, ya sanyo kai cikin ɗakin ya samu gefen gado ya zauna. Yadda ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi da ta ji muryarsa ya sa ta tsawaita ruku'u ba shiri, sai da ta ji ƙafafunta na neman gagara ɗaukarta sannan ta ɗago ta tafi sujjada. A sujjadar ma daɗewa ta yi, ta ƙi ɗagowa, zuciyarta na buga mata da sauri, so kawai take ya fice ya bar ta, ko ta ɗago daga sujjadar da yanzu ba tasbihin da take a cikinta. Ta ma rasa me take ji, shin tsoronsa ne ko kunyarsa take? Ta rasa ma ya zata ɗaga ido ta kalle shi a matsayin mijinta, wanda ya aure ta. Sharhabilu, wai Sharhabilu shi ne mijinta.

***
Shki kuwa Sharhabilu tunda ya shigo ya ga tana salla sai ya nemi guri gefen gadonta ya zauna. Tunda aka ɗaura auren yake jin sa ɗan gata wajen Allah, sadaka kawai ya ke badawa, yana kiran iyayensa a waya yana musu godiya, kamar yanda ya kira su ya nemi amincewarsu a ƙurarren lokaci.

Sai a karshe ne ya kira mahaifiyarsu, tana ɗagawa kuwa cikin zumuɗi ya ce, “an ɗaura min auren Momma!"

Farincikin da Hajiya Zulai ta jiyo a muryarsa ne ya janyo wani tuƙuƙin ɓacin rai tun daga ƙasan ranta.

"Da tsohuwa ko? To wallahi de an ci baya", ta fada kai tsaye, bai kai ga ba ta amsa ba ya ji muryan Alhaji Mamuda bayan ya karɓe wayar daga hannunta.

"My boy is now a groom" Ya faɗa yana dariya, wai yarona ya angwance. Hakan ya sanya hankalin Sharhabilu ya ɗan  kwanta. Bayan sun gaisa Alhaji Mamuda ya sa albarka a auren sosai. ”Kar ka wani damu kanka, haka suke, ba a musu gwaninta. Anyway, welcome to the club ka ji." Alhaji ya faɗa yana mai ƙara kwantar da hankalinsa. Amma duk da sun yi sallama zancen Momma na ta yawo masa a kai, a lokacin ne ya ƙuduri ya shiga ɗakin Zinatu.

Yana zaune yana aikin kallon bayanta ita kuma tana sujudar da bai san ranar ƙarewarta ba, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi, tunani kala-kala ne cunkushe a ranshi. So kawai yake ya rungumo ta ta baya ya shaƙi ƙamshin gashinta da  ƙasan wuyanta, ya ji ko zai yi daidai da wanda hancinsa ke auno masa a duk lokacin da mafarkinsa ya kai ga hakan. To amma salla take, duk da yanzu ita ɗin halalinsa ce, amma sai yake ji sam hakan bai kamata ba. Yana ƙoƙarin tashi ya fita ne ya ga ta ɗago daga sujjadar, ya yi wata ajiyar zuciya gami da murmushi sannan ya dada gyara zama.

Sai da tau lokacinta son rai kafin Zinatu ta juyo ta fuskance shi, sarai ya san ta san da zamanshi a ɗakin, ya san ta san ita yake zaman jira, to amma bai wani damu ba, idan da sabo ai ya saba, haka rayuwarsu ta taso cikin tsama da rashin jituwa, to amma shi ya san tun a wancan lokacin so ne ke ɗawainiya da shi, son ta. Ita kuma wataƙila kishi ne na ya yi mata tarayya da uwa, to amma bai taɓa damuwa ba, Shi dai ya san yana son ta, faƙat!

Ko da Zinatu ta juyo suka yi ido huɗu, sai kawai ta ji ta daburce, gaba ɗaya sai ta rasa wane yanayi take ciki. Karo na farko a rayuwarta, sai ta ji Sharhabilu ya yi mata kwarjini, wani irin kwarjini da ko da ya kira sunanta sai harshenta ya yi mata nauyin amsawa, kamar an sa kwaɗo an datse shi. Sai kawai ta bi shi da idanu, idan harshe ya rasa kalmominsa, an ce idanunu ne ke furtawa.

Sai dai abin da Zinatu ba ta sani ba, daradaran idanunta masu ɗauke da ruwan ƙwalla da cakuɗin tausayi da fargaba a cikinsu gaba ɗaya su  rikita angonta da ke zaune gefen gado yana duban ta. Sharhabilu. Bai san lokacin da ya taso daga inda yake zaune ba ya janyo ta jikinshi ya rungumo ta tsam.

Zinatu sai kawai jin ta ta yi kewaye jikinshi, jikin Sharhabilu.

WA'ADI Where stories live. Discover now