💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
( A heart touching love story)
By mss Lee 💖
PAID BOOK
MAI SON AI MAI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581
BOOK 1 📕
Free page 9 🦋
********
Suna zaune tun safe basu fito ba, oumma ta dafa musu ragowar taliyar jiya sukaji ana faman buga kofar da karfi kamar za a karya," maryam bazaku fito bane kuna ji ina magana", tsaya wa duk sukai daga cin abincin da suke jin muryar kaka tabawa, cikin damuwa oumma ta fito bayan ta yiwa su tahee kashedin karsu fito, a tsats tsaye tagansu ko wannan su , kaka ta bawa sai faman zaginsu take , "inna ina kwana", bata bari ta karasa ba kaka ta bawa ta katseta"ban kwana ba , nace miki ban kwana ba , wallahi maryam kiji tsoran Allah , yanxu daman bakin cikin nace zan aurawa waccan yar taki me kama da aljanu tanimu shine zaku bi dare keda ban ka daddun 'ya'yan ki ku fasa mun randa, kunsan tsawan shekarun randa ta da zaku tashi ku fasa mun" bata bari oumma tayi magana ba ta dora " toh wallahi bari kiji,ko kina so ko ba kyaso aure kamar ya d'aurune dan ba fashi, itama munafukan da suka 'ki futowa dani suke magana, ku fito ka aiki can kutashi kuyi, uban me ya hanaku yin aiki ma yau" sun kuyar da Kai oumma tayi kafun ta fara bata hakuri"kiyi hakuri inna, bamusan Wanda ya fasa miki randa ba" bata karasa ba Dije da bakin ta ya kun bura cikin haushi ta fara"toh karya za ai muku , in baku ba uwan wane ze fasa mata randa, yan bakinciki , shiyasa nace muku zuwan mutanen nan ba alkairi bane "ta kara sa da juyawa tana kallan mutanan gidan. "Hindu ce ta kalli inna ta bawa " inna shiyasa ai jiya nace kawai kisa tanimu ya turo ba sai an jira bintalo ba, dan wannan bakin halin nasu ma waya sani ko sunbi wajan boka " ta karasa tana hararar oumma da ta sun kuyar da Kai har ynxu fuskarta tana a yadda take.
A daki kuwa jin yadda suke zagin oumman nasu yasa tahee fashe wa da kuka , sosai take kukan bakin ciki akan abunda suke musu, ita ba Auran ne ya dameta ba suje su aura mata duk Wanda suka ga dama amma bazata kuma lamunta da cin mutuncin da suke wa oumma ba, sosai shima taheer ransa ya baci. Kara fashewa da kuka tahee tayi jin kaka tabawa nacewa auwalu ya kirawo mata tanimu asa musu rana , sosai sukai musu tatas ko hakurin da oumma take bayarwa basu saurara ba suka bar wajan , Dije sai faman d'ingishi take dan tayi alwashin sai ta ruguza farin cikin su , dan tasan bokan da oumma ta ke bine yasa ayi mata haka (nace uhmmmmm Dije jikin ki be gaya miki ba kenan🤭).
Farin macijin dake la'be tun dasu ya kurawa tahee ido ganin yadda take kuka shima sai launin idanuwansa suka canza daga baki zuwa ja ,sai ya silale ya fita baki d'aya daga dakin ganin oumma na kokarin shigowa.
➰➰➰➰➰➰➰➰
DADA
zaune take cikin wasu lallausan kujera jikinta sanye da wasu fararan cotton din kaya , sosai kayan sukaiwa jikin tsufanta kyau,a center din gabanta wani dan madaidaicin glass jug ne cike da fura, sai faman tashi kamshin furar da yaji damu yake, kallan Aunty dake gefe a zauna tayi tare da gyara zamanta , inajinki Amina , cikin inda inda Hajiya Amina ta soma magana " wai dada naga yan matan gidan duk sun tasa ne , shiyasa nake ganin me zai hana ayi Auran dangi, ko King ne a aura amsa amrah, naga kamar suna kyaunar junansu", sosai dada ta zuba mata idanuwa kafun ta soma magana "amma dai haroon kike magana akai ko, ke yanxu Amina bazaki dena wannan halin naki ba , shi sadaukin Yaushe kike ganinsa har yace miki suna Kaunar juna", kin kina ta soma tama kasa magana " saurin da katar da ita dada tayi"bana san irin haka , inda shi sadaukin ne yace yanasan yar taki da babu abunda zai Hana Aki aura masa , amma tunda be fada ba kar nasake Jin wannan batu, zaki iya tafiya", sosai ran hajiya Amina ya baci da magan maganun dada , dan tabbas tasan da hajiya kilishi ce ko uwar king din da babu abunda zai hana tayi naam da zancen, daman ta dad'e da sanin cewa dada ba kaunarsu take ba , amma fili sai ta saki murmushin nan nata "tuba nake dada , ban fada da wata manufa ba, na barki lapiya", itama dadan jinjina mata kai tayi "akiyaye ",itama aunty mikewa tayi tana fadin "insha Allahu", tare da kama hanyar fita daga falon, bin bayanta da kallo dada tayi kafun ta girgiza kanta tacigaba da sabgar gabanta.