Page 4-5

81 4 0
                                    

💖GIDAN AUNTY💖

        ( A heart touching love story)

           By  Aysha galadima

                 ( mss Lee)

PAID BOOK

    BOOK 1 📕

Bismillahirrahmanir rahim......

Free page 4 and 5🦋

Bugun kofar da akai da Karfine ya katsemusu hirarsu, TAHEER ne ya mike da Niyar bude kofar amma oumma ta tsayar dashi, "dawo taheer bari na bude" fita oummansu tayi suma mimmikewa sukai tare da bin bayanta. Yan gidan ne cike taf a wajan kowa sai faman zabga masu Harara suke , mazan gidan kuwa duk Wanda yaga taheera sai ya kara kallanta sai mafan satar kallanta suke sabamin matan dake harararta.

"Munafukan Allah muna furcin me kuke kullawa, bayan kunsan akwai ayyuka a gabanku, shine dan muna furci da kinibibi kuka shige daki dake da 'ya'yan ki masu kama da tattabaru" cewar wata da tafi kowa za'kewa a cikin su. Zuba wa sarautar Allah ido taheer da taheera sukai wai sune tattabaru hmm . Hakurin da suka ji oumma na bayarwa ne yasa suka maida hankalinsu kanta ," kuyi hakuri Dije bansan akwai ragowar aiki ba shiyasa".

Matar da aka kira da dije ce ta Dallawa oumma harara " kyaji da munafurcin ki, inba munafurciba ba me kuke kullawa a daki ko sallan karuwancin da kika saba kike koya musu" baki taheer ya bude daniyar yin magana amma kallan da yaga oumma tayi masane ya hanashi hakan , sun kuyar da kanshi yayi yana taunar lebensa. Wata daga cikin mutanan gidan ce ta soma magana itama " kinsan dangin Matsiyata ba abunda suka iya sai tsiya in ba karuwanci take koya musu ba me suke yi a dakin", nan da nan mutanan gidan suka fara musu gori da hantara , suna ci musu mutunci , kowa nagidan da abunda yake fada a kansu, kaka ta bawace kawai bata wajan . TAHEE da tunda aka fadi kalmar karuwanci idanuwanta Suka faru da ha waye ga wani irin ja da sukai, ba abunda ke mata yawa sai kalmar karuwanci ko magan ganun da mutanan gidan suke bata ji, wata gigitacciyar kara ta saki da ya firgita kowa dake wajan hatta taheer da ke kusa da ita, hannunta ya so kamawa amma ta hankadashi , daya bayan daya ta soma bin mutanan gidan da tun lokacin da ta saki ihu sukai shiru da kallo, ba Wanda ne tsure ba da irin kallan da take musu, ida nuwanta ne suka sauka a kan dije dake faman zare idanuwa , a guje tayi ganta , suna ganin hakan kowa na gidan ya Watse dan ba karamun firgitasu tayi ba daga mazan har matan. Wani murmushi taheer ya saki daman yasan za Arina, a zuciyarsa sai faman Allah shikara yake musu. Dije dake kokarin shiga daki tahee ta cafko, riko tayi mata ba na wasa ba , Innalillahi wa inna ilaihi rajiuna Dije take ta faman fadi , fuskar ta tuni ta jike da gumi sai faman zare ido take , jama'a ku kawo mun a gaji shikenan ni fatalwa ta kamani, kukai kawai Dije take majina duk ta bata mata fuska. Ita kanta oumma Dije ta bata dariya kuma ta bata tausayi dan Tasan kome zatayi yanxu TAHEE bazata hakura un tayi mata ta Karfi kuma rashin lapiyar tane zea tashi. Taheer ma dake gefe sai faman kunshe dariyarsa yayi ganin yadda Dije ke faman fadin fatalwa ta kamata. Kallan d tahee tayi mata ne ya sata kunshe bakinta "nayi shiru , Wlh nayi shiru" , tana gama fatar hakan ta rike bakinta gam hawaye na fita, Kwale idanuwan ta TAHEE tayi a kanta , take a wajan Dije ta saki futsari dariyar da taheer yake rikewane ta fito wajan dan ba karamun dariya ta basu ba. Baki TAHEE ta bude da nufin cizonta, lokaci daya kuma ta zube a wajan. Tana faduwa kuwa Dije ta arta a guje duk da kibarta a haka ta ke kudin tana tsine TAHEE a zuciyarta.

Daukarta taheer yayi shi da oumma suka nufi daki da ita," maza dakkomun maganinta " cewar oumma , be dade ba ya fito dauke da roba a hannunta, ruwan adduar dake ciki oumma ta iba ta dan shash shafa mata a jikinta da fuskarta, nannauyar ajiyar zuciya ta saki , nun fashinanta na Daidai ta .

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now