Sha uku

32 1 0
                                    

*Ko da so.....*
_*in kin Karanta ki yi sharing please*_

*13*
"Aifa dole kaya su dinga koɗewa, haba ace sawa ɗaya sai an wanke kaya, su kaya ba wani na azo a gani ba" Inna da ta fito daga ɗaki riƙe da ɗan likidiri ta ce da Muktar wanda ke ta faman cuɗa kaya, ɗagowa ya yi yana murmushi daga sunkuyen wankin, "ai Inna kayan ne sam basa mun daɗi in nasu su da ɗauka ko yaya maiƙon jikina ya taɓa kayan na fiso kan in kuma sawa in wanke"

Murmushi inna ta yi, "ai iyawa ne bakai ba, in ka dawo ka cire kayan sai ka baza su a inuwa su sha iska kafin ka mayar adaka"

Murmushi ya yi ba tare da yace komai ba, inna tasan halin abin ta, tunda ya yi  murmushin nan cewa bazai yi bane kawai ba zai ba anma bazai yi yadda ta ce ɗin ba, kwafa ta yi "ai shikenan kayan ka" ta faɗa kafin ta yi zaure har ta kai ta tsaya ni na shiga gidan Harira in ka gama kan kaje in da zaka ka daure ka shigo ka duba Malam ɗazu Fiddausi da ta shigo siyan taliya take cemun jinin nasa ya yi tsanani"
"Tom shikenan a masa sannu kanin zo" Inna bata ce komai ba ta fice daga gidan tabarshi yana shanya.

Sai da ya gama komai sannan ya fito, yana ƙoƙarin ɗaure ƙofar gidan da wayar kebir yaji muryar juwairiyya na faɗin yaya kar ka kulle, sakin ƙofar ya yi tare da juyawa Juwairiyyar ya gani ɗauke da katuwar Kula tare da Hajara wadda ke sanye da uniform ɗauke itama da ƙatuwar kular kamar kullum in ta taso saga makaranta sai ta fara zuwa ta ɗauko kula inda Juwairiyya ko Ummi ke zama da abinci kafim ta tawo gida, bai ce musu komai ba ya tsallaka kwatar da ta raba tsakiyar layin nasu ya shiga gidan su Harira da sallamar sa.

daga zaure suka haɗa ido da Bahayura wadda ke gefen tabarmar da su Inna ke kai tana gurza kuɓewa murmushi ta  sakar masa, lah yaya shigo mana ta faɗa lokacin da ta jawo turmi miƙo masa ta yi zauna daga bakin zauren ya zauna dan tsakar gidan ya tushe, a nutse ya gaida su ya musu ya mai jiki kafin Bahayura ta gai she da shi, "yaya ya aikin?, Jiya nazo ai baka nan"

"Aiki Alhamdulillah, eh jiya naje lesson da nakewa yara da na dawo na biya ta majalisar mu sai dare na shiga gida"

" Haba nifa in ce har gidan su Yaya Salisu naje bakanan"

Murmushi ya yi  " towo Allah yasa ba bashin ki naci na manta da shi ba" sai da kowa ya yi dariya kafin Umman su Bahayuran ta ce " ai ko bashin ne ta ƙyaleka ka sarara.

Aje kuɓewar ta yi kafin ta miƙe ta mika hannu saman kusa da jakun kunan su ke rataye daga ɗan inda rufi ya zubo, takardu ta ciro " ka gani Badawi ne ya kawo min tana nufin saurayin ta wai form ne na school of hygiene, ya sai mun to daga ni har shi muna tsoron mu cike ba dai dai ba" cike da annashuwa ya amsa " amma Badawi ba ƙaramin kyautawa ya yi ba gaskiya miko biro in cike miki yanzu in ya so ko gobe sai in miƙa miki in jiyo mai da me zakuyi."

"Anma yaya da ka kyautamin walllahi don ni yace in kai da kaina gashi na kashe kuɗin motar da yaban."

Tsaf ya cike mata kafin ya mike "bari in leƙa in gaida malam ɗin," sosai ya tausayawa yadda Malam ke jin jiki, a kasalance ya bar gidan kasancewar yau lahadi ranar da suke ɗaukan karatu yasa da ya fito daga gidan littattafan sa ya ɗauka kafin ya wuce masallaci.

Ko da ya dawo dakyar ya samu bacci ya yi awon gaba da shi sabida tunane tunane haka kawai ya rasa mai yasa da ya zauna sai Hafsa da ƴar hirar rakin su mara tsayi ke dawo masa wani zubin takaicin kan sa ya kamashi wani zubun ya saki murmushi, bai san mai yake ji kan yarinyar ba kuma zai iya cewa maine ba yasan dai ba sabo bane ba kuma so bane cikin tunanin da son gano mai ne ya samu bacci ya yi gaba dashi.

Washe gari da wur wuri kamar kulluum ya shirya bayan ya cika gidan da ruwa, fitowar da ya yi daga kama ruwa ya tarar an zuba masa abincin karin sa yau a langane har ya ɗauka ba tare da dubawa sai kuma ya buɗe kosai da faanke ne, "an gama toya wainar nan kuwa?" ya tamaba.

Ko da soWhere stories live. Discover now