Talatin da daya

34 4 4
                                    

https://chat.whatsapp.com/HWOGchc0ANFGLcqBcKeYhH

*Ko Da So*
*31*

_*Kafin mu ɗora muji ya akai akayi auren Hafsa da Muktar, ya akai Mum ta dawo tana son sa, ku biyo mu rayuwar su ta yanzu, nasan baku manta da sakin da ya mata ba, bari muji ko zai mayar da ita ko kuwa*_

_*Babbar Matsalar mu rashin comment, anya kuna bin labarin kuwa,?*_

*Cigaban Labari*

Yamma lis aka sallami Mami Hafsah wadda jikinta da jininta da ya hau ya daidaita. Ko da likitan ya sallameta zaunawa tayi a kan gadon asibitin kanta yana mugun sarawa. Ta rasa tunanin da zatayi a lokacin. Ta rasa inda ta nufa. Ance in bata daina ba jininta zai mugun hawa wanda zai jawo mata wata babbar matsalar. A ganinta babu matsalar da ta kai girman rabuwa da Mukhtar. Sai dai ba kowa bane zai gane. Har shi Mukhtar din da ya jawo musu wannan bala'in.

Ta kalli yaran yadda sukai jigum har sun gaji da tambayarta mene ya faru sunyi shiru. A hankali ta rufe idanunta wasu zafafan hawayen suka sake saukowa. Ta goge su sannan ta mike. Da farko, jiri yaso dibanta kafin tayi gaining balance dinta. Dakin take ganu tamkar ba haske. Hasken rayuwarta ya barta, taya zata ga wani haske a duniya? Ta sake takawa amma sai gashi ta kusa faduwa saboda duhun da take gani a idonta.

Abdallah ya taso ya kama hannunta. Ta kalle shi sannan ta rike hannun nasa da kyau. Da gaske bata jin zata iya yin takun farko ita kadai. Ta hadiye wani abu da ya tsaya mata a rai gami da shanye kukan da takeji ya kulle mata wuya.

Ta kalli sauran yaran cike da damuwa tace, "Muje, gidan aunty Halimah kafin Abie ya dawo." Suka gyada kansu, mutum biyu kuwa suka zuba mata ido tunda da dan wayonsu sun san ba kalau ba. In ma gidan aunty Haliman ne Abien ne yake kaisu. Ta rasa yadda zatayi ne. So take taje can saboda kar yaran su fahimci abunda yake faruwa ba don tana tunanin zuwa gidan aunty Halimah mafita ce ba.

Hawaye ya balle mata wanda a yanzu bata boye ba daga idanunsu dake kanta.

Da kyar ta tausasa zuciyarta ta dena hawaye har suka fito bakin titi domin samun abun hawa. A sannan ta tuna babu kudi a hannunta. Wata zuciyar tace kawai ta tafi gida watakila in Mukhtar din ya ganta ya sauya hukuncin da ya dauka akanta.

Tana tsaye tana tunanin ta yadda zata kira wayarsa sai ga direban gidan yazo ya faka kamar yasan jira take. Ba tare da doguwar magana ba duk suka shige cikin Sienna da aka zo daukan nasu.

Kananan suka soma surutu musamman ma da Malam Idi direba ya mika musu ledar alawa. Abdallah yayi shiru yana kallon window yayinda suke tafiya gidan.

Mami Hafsah ta jinginar da kanta a jikin kujerar ta rufe idonta wanda a ranar babu abunda yake mata dadi kamar rufe idon. So take kawai ace mafarki take. So take ta bude idonta ta ganta zaune a gefen Mukhtar tana bashi abinci a baki suna dariya. So take ya zama ba gaskiya ba. Gwara mata ma ace ta sami matsalar da take sanya ta tunanin da ba daidai ba akan ace mata yinin yau da gaske ne.

Da gaske ne Mukhtar ya sake ta.

*****

Tuki yake a hankali saboda yasan idan yayi gudu ba karamin zagi zai sha ba akan titin ko ma yaje ya jawowa kansa asara da hakkin rai. Tunda yake a rayuwarsa bai taba tsintar kansa a yanayi makamancin wannan ba ko kusa. Bai taba yanke hukuncin da ya yanke masa wani sashe na zuciyarsa ba kamar wannan. Danshin gumin da ya zubo daga goshinsa yabi da kallo yaga yadda farar shaddar da ya sanya ta kwanta a jikinsa saboda zufar tunani da tashin hankali.

Zuciyarsa ma nauyi take masa idan ya tuna kalaman da ya furta dazu. Idan ya tuna kalamai ne amma sun fi adda kaifi. Sarai yana sane da yanayin da Hafsah ta shiga. Ba zai manta kalar dimaucewar da ya gani a kwayar idaniyarta ba sai dai kawai bashi da zabi.

Ko da soWhere stories live. Discover now