Farko Da Ƙarshe.

836 22 1
                                    

HARAMTACCIYAR DUKIYA
       (Gajeren Labari)
       Mallakar:AyshaJb

Yau ma kamar ko wacce rana ina zaune a ruɓaɓɓen akurkin ɗakin da a yanzu shi ne muhallina saboda yanayin halin jinyar da nake ciki, ba yara ba hatta ga manya ƙyamatata suke yi, duk inda na gifta nuna ni ake ana zunɗeta, yawancin yara kuwa jifata suke suna kirana da. 'Mahaukaciya.' Dole a kira ni da wannan sunan domin ba ni da maraba da mahaukaciyar, na yi dauɗa saboda rashin wanka, wankin kaya ma ba a magana domin kayan da ke jikina wani irin ɗoyi na fitar hankali suke yi. Uwa uba yadda tsari halittar jikina yake a yanzu tamkar aljana domin ko ni ba na sanya kaina cikin jerin bil'adama. Wani irin  gashi masu masifar ƙarfi da ƙaikayi ne suka firfito min, ga shi a tsattsaye suke maimakon a kwance, da yawan jama'a kwatance na suke yi  da  me suffar junnu. Ajiyan zuciya na sauke a karo na barkatai jin an wullo min wani busheshshen biredi wanda ba na raba ɗayan-biyun  yarona Anwar ne domin daga shi sai mahaifiyata wacce ita ma ya zame mata dole ne ya sa take tsakura min abinci saboda surutun kishiyoyinta, hawaye ne suka ci gaba da zariya bisa kuncina sakamakon amsar kuwar da masarrafan ji na ke yi wanda ake  sake jaddada min adadin kwanakin da ya saura ga rayuwata. Nan take zuciyata ta tsinke, ina faɗin “Dama yau ce ranata ta ƙarshe. Wannan azaban da ake gana min ma kaɗai ya ishe ni, na fi buƙatar mutuwa ta fiyye da komai a yanzu. Kwana biyu rak! Ya rage min a duniyar da ke cike da ƙalubale iri-iri wadda nake da buri kafin wannan ranar na samu ganawa da ɗan'uwana kuma miji a gareni domin neman gafarar shi, ba na so na koma ga mahaliccina ba tare da na waiwayi baya na haskowa al'umma irin mummunar rayuwar da na jefa kaina cikin ta ba. Wanda ƙazamin buri tare da tuɗin duniya ya ɗibeni na afkani cikin komar da-na-sani.
     Fa’iza Hamza shi ne cikakken sunana ni marainiya ce kuma ni ce 'ya ɗaya tilo a gidanmu domin tun ina ƙarama Allah ya yi wa mahaifina rasuwa inda ya bar mata uku Ummata ita ce ta biyu, wani irin rayuwa ake a gidanmu na ba ruwan wani da ɗan'uwansa, duk da ƙasa ta rufewa mahaifina ido hakan bai hanasu zaman kishi ba, habaici da baƙar magana kuwa ya zame musu tamkar ruwan shan su. Duk maganar da za su yi Ummata ba ta ɗaga kai ta kalle su balle ta ce musu wani abu, ta mayar da hankalinta wurin neman kuɗi domin inganta rayuwata, tarbiyya daidai gwargwado na samu daga wurin Ummata.
    Tun ina ƙarama na ta so da burin son karatu sai dai haƙata ba ta cimma ruwa ba, domin kuwa bayan gidan da mahaifina ya mutu ya bari wanda rabin ginin ya zube, ba mu da komai abincin da za mu ci ma da ƙyar Ummata take fafutukar nemo mana. A haka ta yi ta faɗi-tashi da taimakon 'yan'uwanta na yi firamare sai makarantar allon da nake zuwa, duk dangin mahaifina babu mai ƙarfi ɗaukar ɗawainiyata kowa na ƙoƙarin nema wa iyalansa abin da za su saka a bakin salati. Ga shi na taso da wani ƙazamin buri a rayuwata wanda kullum idan na kalli kaina cikin madubi sai in ji wani takaici ya  lulluɓe ni  kasancewata kyakkyawar da ya dace a ce na fito daga tsatson masu ƙunbar susa, sai ga shi na faɗo gidan talakawa talakan ma futuk wanda abinci ma da ƙyar ake samu. A ƙasar anguwarmu akwai wani  mutum wanda muke kiran shi Yaa Hafiz muna gaisuwar mutunci da shi wani lokaci har zama muke yi mu yi 'yar fira, yana sayar da shadduna da atamfofi. Da taimakon sa na shiga islamiyya anan na haɗu da ƙawaye 'ya'yan manya yanayin rayuwarsu ya sa kullum sai na kalli kaina  ina faɗin “Dama ni ce ake kawowa a mota me AC kamar yadda ake kawo su” Ko kayan sallah idan Ummata ta yi mun renawa nake yi domin ina ganin na fi ƙarfin zanin dubu da biyar.
   Fatima da Suhailat duk tare da su muka yi makarantar allo bayan mun kammala ba mu sake haɗuwa ba kasancewar sun yi tafiya. Na sha mamaki sosai lokacin da suka dawo na ga sauyi tattare da su yadda suke wadaƙa da kuɗi da yadda ake shige musu ana nan-nan da su sai nake ta mamakin lamarin domin suma dai kamar ni ɗin ce.
    Watarana muna cikin fira na ce. “Ni kam wani abu na ba ni mamaki yadda lokaci ɗaya za ka ga mara arziki na kuɗancewa ya fi  wani mai arzikin ma kuɗi, kamar dai ku ɗin nan, bambancin da ke tsakaninmu kwalin degree ke gareku ni kuwa ko sakandiri ban yi ba, ba aiki kuke yi ba balle in ce da albashin kuke bushasha. Bare ma albashin gwaunatin ba zai kai har ku dinga wadaƙa irin haka ba..”  Shewar da suka yi shi ya dakatar da sauran maganar da nake yi.
  “Muna da degree amma kwalin bai da amfani tun da ga shi nan ba mu samu abin yi ba. Ba mu kuma da hanyar samu kin san irin jujjuyamun da aka dinga yi a kan neman aiki kuwa? Kin san wahala da fafutukar da muka dinga yi amma babu nasara? Na ji takaici ga shi duk ƙoƙari iyayenmu sun yi suna ta murna muna da kwalin da za mu samu aiki mu tallafesu.” Mun yi hira inda anan na fuskanci irin gwagwarmayar da suka shiga na neman aiki amma babu nasara.
              Watarana ina zaune a shagon Yaa Hafiz muna fira a TV naga an hasko wasu mutane an kama su a Legas firar da ake yi da su ya ba ni mamaki sosai. Inda ake tambayarsu yadda suka kasance cikin ƙungiyar matsafa, ɗayan ya ce. “Ba ƙungiyar matsafa ba ce, ƙungiya ce da ke taimakawa ire-iren mu waɗanda suka kammala karatu babu aikin yi, sama da shekaru biyar ina zaune babu aikin yi ga shi ina da ƙannai iyayena sun ɗora burin in  samu aiki in tallafesu. Ina so in yi aure babu hali muna cikin matsi da ƙuncin rayuwa hatta abin da za mu ci da ƙyar muke samu yunwa na neman kashe mu dalilin da ya sa na shiga ƙungiyar kenan, domin ranar da na shiga aka a ba ni miliyan goma. Kodayake sai da na bayar da ɗaya daga cikin dangina.. Ina ƙoƙarin bayar da mahaifiyata shi ne aka samu aka sin da har asirina ya tonu” Babu nadama ko tsoro a muryanshi haka ya dinga ba da labari. Yayin da ɗayan ya ce.
                “Ƙungiyar ce ta nemi na ba da mahaifina ko ɗana domin idan ina son na ci gaba da samun dukiya dole na salwantar da ɗaya daga cikin su. Mutane biyu da aka ambata ina matuƙar ƙaunarsu na nemi a musanya da matata amma aka ce lallai sai jinina haka na ɗauki mahaifina wadda ya temaka ya hana cikinsa ya inganta rayuwata har na kammala karatu matsalar da na fuskanta bai wuce na neman aiki ba, domin na yi bulayi ban samu ba. Dalilin da ya sa lokacin da abokina ya yi min tayin ƙungiyar ban ƙi ba, jin ana ba da zunzurutun kuɗi ya sa na amince na shiga ƙungiyar.”
        “Don kun kammala karatu babu aikin yi sai ku jefa rayuwar ku a irin wannan ƙungiyar? Ta ya ya aka yi asirin ku ya tonu? A ina reshen ƙungiyar taku yake? Wa ke shugabantar ƙungiyar?” Kallon Yaa Hafiz na yi ina tambayar shi. “Ya aka yi suka yi shuru?” Dariya ya yi tare da kashe TV yana faɗin. “Ai ba za su iya furta wata kalma bayan wanda suka faɗa ba, wannan kalaman da su ka yi ma za su amshi sakamako daga ƙungiyar, a doka  irin ta wannan ƙungiyar ba a ƙyale duk masu son buɗe sirinta. Ba su da wayo, domin ba za su kai labari ba,  ni ko za a kashe ni ba zan faɗi yadda aka yi na shiga ƙungiya ba.
   Matsala ya dame ka ba dole ka nema wa kanka mafita ba, shuwagabanni sun yi kane-kane a dukiyarmu in ka kai kuka babu me share maka hawaye ya rayuwarmu ba za ta gurɓace ba? Ki dubi yadda muke da matasa  daga mata har mazan duk an yi karatu amma babu aikin yi wani ma in ka je neman aiki a yi ta juya ka a ce yau a ce gobe daga haka za a shashantar da kai, ga tsadar rayuwar da muke fuskanta pure water wannan ƙwaya ɗaya naira talatin yake, kayan hatsi kuwa ya fi komai tsada, al'umma na cikin damuwa maimakon abubuwa su sauko kullum sai gaba-gaba take”
  Bayan na dawo gida na ga Ummata zaune jugun tambayarta na yi abin da ke faruwa nan take sanar min da rasuwar babar Fatima, bayan rasuwar na ga Fatima da wani danƙareren  mota wanda ake ya yi, arziki kuwa ya ci uban na da. 
  Na shiga komar mamaki nan na fara tunanin ta ina suke samun waɗannan manyan kuɗaɗen haka? Ban yi ƙasa a gwiwa ba na nufi wurin Yaa Hafiz ina tambayar shi ko yana da labarin inda suke samun kuɗi, domin a halin yanzu ni ma ina cikin buƙata ga bikina da Yaya Sudais (Ɗan wajen ƙanin mahaifina) Ya gabato dangin mahaifina sun yi min kayan gado, wanda ba wani abin a zo a gani ba ne har kunyar kallon kayan nake ji. Ummata ta tsinta mi 'yan kwanukan samiru  duk na rena kayan abin takaici ma a ɗaki ciki ɗaya za mu zauna.
   “Yaa Hafiz ko ka san sana'ar da su Fatima suke yi suke samun wannan kuɗaɗe haka? Idan ka sani ka sanar da ni domin ni ma ina buƙata ko ma mene ne zan yi..”
   “Ba za ki iya ba!”
Amsar da ya ba ni kenan tun ban ƙara sa maganar ba, tare da faɗin. “Ki yi haƙuri kawai ki je ki zauna a ɗakin mijinki..”
“Na gaji da baƙin talaucin nan! Ni ma ina da buri, ina so a dinga nuna ni kamar yadda ake nuna su, kowa zancen su yake lokaci ɗaya sun shahara in so samu ne ina so nawa shaharar  da ɗaukakar ya danne nasu, ina so ko’ina na gifta a ambaci sunana”
Dariya kawai ya yi tare da faɗin “Kamar dai yadda na ce a baya ba za ki iya ba” Haka na dawo gida ina saƙe-saƙe cikin raina. Har aka yi bikina irin gudumawar da suka ba ni ne ya sake hura min wutar son samun dukiya fiyye da nasu, tun da aka gama hidimar bikina ban samu na haɗu da Yaa Hafiz ba, domin yaya Sudais irin mazan nan ne masu kulle, yana ƙoƙari daidai gwargwado sai dai kullum idanuna na tukunyar maƙotana ganin irin cimar da suke girkawa, duk abin da zai kawo sai na goranta mishi  tare da yaɓa mishi baƙar magana ina nuna gazawar shi. Wani lokaci yakan yi murmushi ya ce. “Fa’iza kenan! Ki bar hangen nesa, a hakan da kike wallahi wani yana neman abun da kika raina bai samu ba” Wani lokaci kuwa sai dai ya yi murmushi ya ce. “Allah ya shirya ki” A haka har na samu juna biyu  bayan na haifi Anwar na zo wankan gida na samu wata ɗaya da kwanaki kafin na fita zuwa shagon Yaa Hafiz. Ina cikin kallon hotuna a wayarshi na ga wasu zobuna da saraƙuna sai wasu baƙaƙen kaya. Kallon shi na yi tare da faɗin. “Dama kaima kana da naka ƙungiyar shi ne ko a saka ni? Mene ne dokokin domin ina son shiga?”
“Kina da aure ba lallai ki iya tsallake ƙasar nan zuwa ƙasar Afghanistan ba, dokokin suna da tsauri..”
Dafe ƙirji na yi ina faɗin. “Har Afghanistan ake zuwa? Ni kam ban san yadda zan yi da yaya ya bar ni na je ba.”
“Akwai yadda za a yi muddin kina so da gaske zan faɗa miki abubuwan da za ki yi wadda zai sa ki samu ƙarfi har ya ba ki damar zuwa inda kike so..” Da sauri na tari numfashinsa wurin faɗin. “Dan Allah sanar da ni.” A ranar bai faɗa min ba, ya ce na je sai na yaye Anwar, aikuwa ina yaye shi na dawo nan ya ce in saya kwakwa wanda ba a fasa ba, sha biyun dare zan yi amfani da shi inda zan fasa kwakwar in yi amfani da ruwan bayan na gama  sai in zuba su cikin ruwan da zan yi wanka da shi, akwai wani gishirin da ya ɗiba min shi ma cikin ruwan wankan zan zuba wanda ya ce min dubu hamsin ake sayansa a can ƙasar.  Ya ba ni wasu kalmomi masu wuyar haddacewa wanda da ƙyar ya dinga maimaita min ina faɗa har na haddace kalaman, sannan zan samu ƙasa mai laushi wanda zan ɗora tafin kafana a kai sai wani barkono da ya ɗiɓa min, shi kuma a baki na zan saka ina taunawa bayan na tsaya kan ƙasar sai in dinga jero buƙatuna, wannan sai ɗaya da rabi na dare zan yi.  Abubuwa da yawa ya faɗa min, haka na dawo gida na yi duk abubuwan da ya faɗa min, da sassafe na ɗauki wayar yaya Sudais na kira shi ina sanar da shi na yi duk abin da ya ce in yi. Murmushi ya yi yana faɗin. “Shugaban ƙungiya ya sanar min ki jira zuwan baƙon mu ƙarfe biyun dare zai zo karki firgita in za ki kwanta yau kar ki yi addu'a idan ya zo ki sanar da shi duk wasu abubuwan da kike buƙata a duniyarnan” Ajiye wayar na yi ina tunanin ta ya ya zan ga wani mutum? Wunin ranar haka na yi shi cikin tunani har dare ya yi Allah ya sa ma yaya ya yi  tafiya zuwa kasuwar ƙauye, ina cikin barci na fara ganin wani duhu-duhu can kamar wacce aka farkar da ni na buɗe ido, nan naga wani shirgegen ƙaton mutum baƙin ƙirin da rusheshen ciki, daurewa na yi saboda tsoro ina amsa tambayoyin da yake min tare da sanar da shi abubuwa da nake son samu a rayuwa, na buƙaci ɗaukaka, farin jini, tare da tarin dukiyar da babu iyaka, na ƙara da faɗin. “Ina so kuma duk abin da na buƙata daga mutane a aikata min shi, ina buƙatar ƙarfi da ƙwarjini.”
Washegari na nufi wurin Yaa Hafiz nan yake sanar min da komai ya yi na je na fara shirin tafiya komai na ce yanzu babu mai dakatar da ni, haka kuwa aka yi, domin kuwa ina cewa yaya Sudais zan yi tafiya ya kasa dakatar da ni sai ma fatan alkairi haka ma Ummata ba ta dakatar da ni ba, nan wurinta na bar Anwar wadda a yanzu yake cikin shekara biyu da rabi, washegari muka nufi abuja a can ya gama cuku-cuku ban taɓa shiga jirgi ba sai a wannan ranar bayan mun isa  wata baƙar  mota ce ya ɗauke mu ina shiga motar na ji hantar cikina na kaɗawa domin kuwa wani irin kuka motar ke yi kamar inji, nutsewa motar yake yi a ƙasa sosai, cike da tsoro na kalli Yaa Hafiz sai dai ban ga alamar tsoro tattare da shi ba, haɗiye maganar na yi har muka isa can ƙarƙashin ƙasa wani irin gini me tsawon gaske muka shiga tun a hanya na fara cin karo da  mutane wanda da yawa Hausawa ne harda fuskokin da na sani na manyan mutane wanda ake hasko su a TV. Babban ɗakin taron muka shiga nan aka amshe ni ana min maraba da zuwa tare da gabatar min da wani ruwa a ƙwariya haka na kafa kai na shanye aka ƙara ba ni wani baƙin ruwa mai ratsin ja a ciki, shi ma na shanye tun daga wannan lokaci na ji tamkar an wanke min wasu abubuwan daga masarrafan da ke auna tunanina, mutumin da ke zaune riƙe da sanda me tsawon gaske ya shiga jero min dokokin su masu wuyar ɗauka, amma da ke sheɗan ya riga da ya buga min gangan a ka, ban damu ba haka na amince da duk wasu sharuɗan su. Sati biyu sannan muka ɗauko hayar dawowa bayan na saya wayar da ake ya yi na buɗe asusun ajiyar kuɗi inda aka cika mini banki na da miliyoyin kuɗaɗe. A danƙareren gidan da na saya na sauka bayan mun yi sallama da Yaa Hafiz,  kamar yadda na tafi babu wanda ya tambayi ina zan je, haka ma dukiyar da na samu tare da gida babu wanda ya tambayi ina na samo wannan dukiyar duk da na lura lokuta da dama Ummata na son min magana sai dai da zaran na kalleta ba ta iya cewa komai haka ma yaya Sudais duk ƙoƙarin da na yi wurin ba shi tallafin kuɗi domin ya ja jari ya ƙi amsa, lokacin ya ja sosai wanda a dokar ƙungiyarmu duk wata akwai sadaukarwan da muke yi na dabba. Kuma muna kai ziyara domin tattaunawa a kan yadda muke gudanar da dukiyarmu, ɗaukakar da na yi cikin al'umma ya take nasu kamar yadda na buƙaci komai haka komai ya zo min cikin sauƙi, ina juya rayuwa yadda na ke so, domin na samu duniya na yi yawon ƙasashen duniya sosai babu inda ban taka ƙafata ba illa ƙasa ɗaya jal! Ƙasar da kowane Musulmi ke da burin zuwa sai dai ni ko kusa ban taɓa kawo ƙasar a zuciyata ba, hasali ma na manta da wannan ƙasar.
  An shafe fiyye da shekara ina gudanar da rayuwata cikin jin daɗi domin ban cika zaman Nigeria ba, na mayar da hankali kan yawon buɗe ido da sayayyar kayan ƙyale-ƙyale na saya gida fiyye da biyar mota kuwa sai wanda na zaɓa nake hawa direba ya jani koda na samu juna biyu take shugaban ƙungiyar mu ya ɓukata jin zan samu ƙarin ninkin dukiya ya sa na amince haka na sadaukar da ɗan tayin cikina. Ina tsaka da hutawa a falo na ji ƙarar fashewar abu da gudu na tashi nan naga Anwar ne cikin ɗakin da nake ganawa da shugaban ƙungiyar mu, ya fasa min kayan masu muhimmanci da amfani, cikin tsananin tashin na ja shi zuwa waje ina mishi faɗa ya rage ɓarna ina shiga ɗakin na samu kira daga shugabar ƙungiyar mu a kan lallai in zo a kwai taron gaggawa.
“Muna buƙatar jini ba na dabba ba, na mutum kuma shaƙiƙin ki..”
A razane na ce “Me..!” Wani tsawar da ya da ka min ya sa ni yin shuru gabaɗaya na gigice jin abin da ake buƙata “Akwai gaɓar da ba ki da zaɓi, don haka a wannan gaɓar an ba ki zaɓi cikin biyu Uban ko Ɗan?” Ina wani irin kuka na ce “Sudais!” Ina faɗin haka suka kwashe da dariya koda na dawo gida na rasa sukuni sai kallon yaya Sudais nake ina jin damuwa sosai a raina “Ya ya dai? Akwai wani abu ne?” Cewar yaya Sudais girgiza masa kai na yi alamar babu.  Cikin dare wani irin ciwo ya kwantar da shi ga shi babu halin na temaka mishi haka ina ji ina gani ya dinga murƙususu kwana biyar yana kwance zuwa lokacin na fita sha'aninsa domin wasu mahaukatan kuɗin da na yi arba da su ya goge min ɗan burbushin tausayinsa da nake ji. 'Yan'uwa da suka fahimci halin da yake ciki ne suka ɗauke shi zuwa gidan magani ba tare da na sani ba. Ɗakin sirri na kuwa ina kaffa-kaffa da shi kasancewar Anwar ɓarna ne da shi muddin ya shiga ɗakin sai na fuskanci tashin hankali. Watarana ina cikin wanka na ji motsin Ummata tana ta kiran Anwar cikin gaggawa na kammala na fito can na isko su cikin ɗakin sirri na. “Umma! Me kuke yi ciki? Wayyo na shiga uku..” Da gudu na ƙarasa ganin Anwar kwance yana shure-shure jini na fita mishi ta ido. “Ya isa haka ku barmin yaro bai san komai ba dan Allah kar ku yi mishi komai..” Gani na yi Ummata ita ma ta zube ƙasa wani irin ihu na saka na koma kanta “Ita ma ta ga komai dole su ɗin nan muna buƙatar su...”
“A'a kar mu yi haka da ku! Kun buƙaci mijina na ba ku ba zai yiwu cikin gajeren lokaci ku ɗauke min farinciki na ba..”
“Ha!ha!!ha!!! Farinciki nawa muka ba ki? Kina iya ƙirga adadin dukiyar da kike da shi a yanzu? Ai mun sanar da ke tun farko muma muna da tamu buƙatar kuma dole a yi mana su, tun farkon zuwan ki mun faɗa miki sharuɗanmu kika ce za ki iya dole a ba mu jini don ba mu samu wancan jinin ba. Kin kai matsayin da kema za ki sadaukar mana da komai tun da dai mun ba ki duk wasu abubuwan da kika buƙata..”
Juyowar da zan yi sai ga yaya Sudais a tsaye ya harɗe hannuwanshi a ƙirji miƙewa na yi ina nuna shi “Kina mamaki ko? To ban mutu ba, kuma ki sani muddin wani abu ya samu ɗana..” Ƙwafa ya yi tare da ɗaukar Anwar sannan ya dawo ya ɗauki Ummata gabaɗaya na kasa ƙwaƙƙwarar motsi suna fita na tsinci kaina a ɗakin taron ƙungiyar mu. “Mijinki ɗan tauri ne, ba mu da ikon taɓa shi bare mu taɓa ɗan sa, dan ya jawo mana asarar da sai an zubar da jini.. Ki bamu Mahaifiyarki...”
Haɗa hannuwa na yi ina faɗin “A'a dan Allah ku bar mun Ummata kar ku taɓa ta..”
“Za ki fanshe ta!..” Cikin ihu da hargagi na ce “Ban mori duniyar ba, ta ya ya zan sadaukar da kaina ba fa zai yuwu ba!” Sandar da ke hannun shugabanmu ne yai wani irin haske a fuskata take kaina yai wani irin juyawa “Kin gama morar duniyarnan! Ki je don kanki duk wasu abubuwa kin rasa su komai zai shafe tamkar ba a yi ba! Ba a jayayya da mu wannan doka ce, za ki fara ganin sakamako. Tun yanzu ki fara ƙirga kwanakin da suka saura a rayuwar ki..”
    Cikin zafin rai na fara mayar musu da martani.
“Ai ba ku kuka saka min numfashin ba da za ku cire min, dukiyata, ɗaukakata, duk babu inda za su je domin ni ma na hidimta...”
   Shaƙe min wuya aka yi tare da wullo ni filin farfajiyar gidana da komai ya shafe komai ya koma yashi, hatta sauran gidajen sun rushe tare da shafe komai shagunan da nake kasuwanci ma ya yi gobara wani irin ihu na saka tare da yin zaman 'yan bori a tsakiyar hanya, misalin ƙarfe biyun dare na fara jin wani irin fitinannen ƙaiƙayi ina jin jikina tamkar ƙaya-ƙaya. Tun daga wannan lokaci na fara fuskanta azaba daga ƙungiyar mu, yawo nake a bola tamkar zararriya ina sushe-sushe yara da manya suna jifata tare da kirana da mahaukaciya. Sati guda ina bulayi kafin dangin mahaifina suka ɗauke ni zuwa wurin mahaifiyata faɗa suka yi mata sosai sannan suka ɗora da nasiha suna ba ta haƙuri a kan lallai ta kula da ni tun da ita Uwa ce koma me na yi mata bai kamata ta watsar da ni ba, Allah ma ya taƙaita da abin ya tsaya iya kaina domin tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan duka. A wani tsohon kichin ɗin da aka daina girki Ummata ta saka ni, tun daga wannan lokacin ban sake saka ta cikin idanuna ba sai dai in abinci za ta ba ni shi ne zata buɗe ƙofa ta turo min da ƙafa sau da yawa ta kan tsaya inda nake tana faɗin. “Kwaɗayi mabuɗin wahala, kina 'yar talaka ki ɗauki ƙazamin buri ki saka wa ranki yau wa gari ya waya? Ina dukiyar suke? Ina ɗaukakar? Duk sun shafe tamkar ba a yi ba, Allah ya gani na yi duk ƙoƙarin da ya dace a matsayina na Uwa. Duk masu zagina a kan ina ƙyamatar ki sai Allah ya saka min..  “Umma dan Allah ki zo gareni Umma za su kashe ni. Anwar ka ce wa Abban ka ya yafe ni.. Ko so ɗaya Umma ki ce masa ya zo wallahi zan yi haƙuri da talauci na, zan zauna...” Dakatar da ni Umma ta yi da faɗin. “A wannan ɗoyin da kike yi ne Sudais zai zauna da ke? Ai tun tuni ya sallamawa duniya ke, takardar ki na ajiye”
Na yi kuka sosai ina kuma tur da rayuwa irin tawa, babu mai raɓar inda nake Anwar kaɗai ke zuwa shi ma Ummata ta hanashi sai dai in ya je makaranta abin da ya ci ya rage sai ya jefo min. So biyu ina fita zuwa wurin Yaa Hafiz sai dai kafin in ƙara sa nake dawowa saboda yadda yara suke harbina suna watsa min ƙasa, ihu na saka da ƙarfi jin an figi sauran gashin kaina miƙewa na yi ina girgiza kai da kiran sunan Ummata sai dai ko ƙafarta ban gani ba, haka na gama kiraye-kirayen sunan mutanen gidanmu babu wanda ya zo inda nake yayin da nake kallon yadda za a gurfanar da ni ga dodon tsafi wani irin wuƙa mai kaifi da tsini a aka zaro take na saka wani hargitsattsen kuka ina jin da ma ban zo duniyar ba.

Ƙarshen labarin kenan.

08062715485

HARAMTACCIYAR DUKIYAWhere stories live. Discover now