Episode 10

1 0 0
                                    

*💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*


_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________


*_episode 10💧_*


💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

*Alhaji ɗan Ijje*

___Tun yana kan hanya ya kira number sa yasanar masa da zuwan sa, dan haka tun kan ya ƙaraso aka sanar da masu gadin gidan, bai wani tsaya ba yana zuwa suka basa hanya, ya wuce ciki, gida ne tafkeken gaske me girman gaske wanda yaci uwar na Alhaji Ɗan Ijje a girma da haɗuwa da komai, wajen gidan da cikin gidan duk cike yake da matakan tsaro sun zagaye ko ina na cikin gidan, wasu harda bindigu a hannun su irin zabga zabgan nan,

Motar sa na tsayawa a wata farfajiya, wani daga cikin masu tsaron gidan yazo da sauri ya buɗe masa ƙofa, yana fitowa wanda ya buɗe masa motar yayi yana yi masa iso yana nuna masa inda zaiyi, sai kuma wasu mutum biyu a bayan sa suna mara masa baya, saida sukayi tafiyar kamar minti 3 sannan suka ƙaraso bakin wata ƙofa me ɗan faɗi suka buɗe suka shiga wani dogon corridor suka kuma miƙewa ba wata tafiya me tsawo sannan sukayi kwana tun anyi kwanar sauran biyun suka tsaya daga gurin da ɗayan suka ƙarasa bakin wata ƙofa nocking yayi sannan ya matsa daga gurin tare da juyawa ya matsa can nesa dashi,

A hankali a ka buɗe ƙofar wata mata ce ta buɗe tare da sunkuyar da kai ƙasa tace barka da zuwa bismillah ta faɗa tana basa hanya, shiga yayi tare da yin sallama ta amsa masa, tare da barin wajen, cikin tanƙameman falon ya ƙarasa ya samu ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman royal chairs ɗin da suka gaji da kyau ya samu ya zauna, babu kowa a falon sai kan center table ɗin da aka cika da kayan marmari, shiru yayi yana ɗan bin falon da kallo duk da ba wannan ne loƙacin da ya fara shigowa falon ba, saidai kuma duk shigowa sai ka samu abun da aka sauya a cikin falon,

"Ahh wata sabon gani ashe talaka na ganinka, Mas'ud baka da kirki wallahi mutuncin ka kaɗanne"

Dariya Alhaji ɗan Ijje yake yi irin tasu ta manya ta masu kuɗi, yana jinjina halin sa da irin waɗannan maganganun nasa, shi dai a kwai sa zolaya...,

Mutumin shima fuskar sa ɗauke da murmushi a kan kyakkyawar fuskar sa ya ƙaraso inda yake zaune yana miƙa masa hannun alamar suyi musabaha da sauri Alhaji ɗan Ijje shima ya miƙe yana miƙa masa sukayi musabaha, sannan Alhaji ɗan Ijje ya koma ya zauna shima mutumin kujera ya samu ya zauna yana fuskantar sa.

Alhajin Allah kana nan abunka ka manta damu kaci mutuncin abota wallahi duk da bansan dalilin ka na juya mana baya ba,

Alhaji ɗan Ijje ya ɗan sosa kai sannan yace; "Hmm ai kune Alhazai wane mu muna gefe, siyasa ta ɓoye ku, ya shirye-shiryen zaɓe kuma?

Saida ya ɗanyi jim kamar bazai ce masa komai ba, sai kuma can yace;zaɓe alahamdulillah, tunda kai ka guje mu me zai hana yanzu ka ƙara fitowa takarar ina tunanin yanzu baza a kuma samun matsala ba kamar da, saboda ada ɗinma laifin kane amma da tuni kasan kai zaka ci amma ka juya mana baya amma......

Hannu Alhaji ɗan Ijje ya ɗaga masa tare da cewa; dan Allah mubar wannan maganar tunda de komai ya wuce, yanzun ma ɗan wani abune ya kawo ni idan zai samu fa amma ba takura idan kuma da matsala shima abarsa.

Shiru yayi kamar yanda ya buƙata amma aransa baiji daɗin hakan da yayi masa ba, ko ba komai yakai wani matsayi da shi bai kai ba duk girman abotar da ke tsakanin su bai kamata ya ɗaga masa hannu ba a loƙacin da yake magana, amma duk da haka me makon ya nuna masa ɓacin ransa saima murmushin girma irin nasu na masu kuɗi da ya sakar masa yana me ɗaukar glass cups ɗin da aka kifesu akan plate juyo dasu yayi sannan ya ɗauki flaks ɗin tea ya tsiyaya a ciki sannan ya ɗauka ya miƙa masa, ba musu ya amsa,

💧💦SU WAYE SU....!?💦💧Where stories live. Discover now