Episode 5

1 0 0
                                    

*💦SU WAYE SU...!?💦*
          *_(Who are they...!?)_*

              
     _💦Story and writing💦_
                         💎
          *🌬️Yaya Azeema😎*
   ______________________________
                      
               
                   *_episode 5💧_*

                         
             💧💦محمدالرسوالله...!💦💧

Bissmillah.....✍️

 
       *News*

  "A yau ranar Laraba an tashi da ɓatan ɗan gidan commission of police na jahar Kano KHAMIS ADAM IBRAHIM akan hanyar dawowar sa gida akayi kidnapping ɗin sa, to bincike kuma ya nuna ana zargin wasu ƴan mata da suka shigo garin bayan fafatawar da sukayi da ƴan sanda akan ɗan gidan Alhaji Ɗan Ijje da suka sace shi, bayan kamasu kuma suka ƙi yarda a kama su har sukayi nasara tserewa ƴan sanda aka rasa inda suke tode yanzu ga hoton ƴan mata kamar yanda kuke gani yanzu dai hukuma tana neman su ido rufe ga duk wanda ya gansu sai yayi saurin sanar da hukuma domin.........,

Ɗif tvn ta ɗauke sakamakon kashewar da aunty Babba tayi, tare da jan tsaki,

"Tabb babbar magana.. meye mafita?

"Mu miƙa kanmu...

Dukan su zuba mata ido sukayi cike da mamakin faɗar hakan.

"Beenish kinsan kwa me kika ce?

"Eh, Aunty Babba, ina ganin kamar hakan shine mafita, tayi maganar cikin sanyin murya,

Zee ce tace "Beenish baza'ayi hakan ba, wannan maganar bata taso ba kefe kike ƙarfafa mana gwiwa bai kamata wannan abun yasa ki fara karaya ba tun yanzu, idan muka miƙa kanmu bazasu taɓa yarda bamu bane saboda duk wata alama da zatasa a gane mune munriga da mun nunata, dan haka bazai yiyu mu nuna kanmu tun yanzu ba,

"Nima dai abun da nagani kenan idan mukayi haka zamu iya jefa kanmu cikin cakwakiya, suna da kuɗi duk yanda zasuyi su ɗora mana laifin zasu iya bazamu taɓa kare kanmu ba ko abun da mukayiwa ƴan sandan da kuma ɗauke sa da mukayi tun farko dole sai sun hukunta mu akan hakan....

Maganar ki gaskiya ce "Ameela, ko an ajiye maganar kidnapping bamu bane, amma dukan nasu shima laifi ne da kuma ɗauke shin da mukayi tun farko mun wahalar dasu, dan haka baza su barmu ba hakannan, cewar Babyn baby,

  "Barazana tace "yanzu de ai babu wanda yaga fuskar mu, dan haka mafita itace zamu dena fita da motar mu sannan dole mu ringa ƙoƙarin rarraba kanmu kar mu ringa yawan nuna guri ɗaya muke,kar agane kanmu a haɗe yake, idan mun fita mu ringa raba hanya, ko ya kuka gani?

'Hummm to kusan hakanne mafitar amma kuma fitar muma ɗaiɗai kuwa zata yiyu kuna ganin babu matsala,

"To in bahaka ba ya zamuyi gwanda mu fara gwada hakan zuwa wani loƙaci kafin mu samowa kanmu mafita....

Nan dai sukai ta tattaunawa kowa yana kawo tasa shawara har suka tsaya a matsaya ɗaya, wajen ƙarfe goma duk suka tafi suka kwanta, kowa yana ƙara saƙa wasu abubuwan aransa,

            ***********************

     *Waye Alhaji Ɗan Ijje..?*

'"Alhaji Ɗan Ijje, Babban mutum ne dan a ƙalla shekarun sa zasu iya kaiwa hamsin, mugun me kuɗi ne kuɗin sa har sun kai yawan dash kansa baisan adadin su ba, saidai kuma abun tambayar ga sauran mutane ƴan gari babu wanda yasan tsayayyiyar sana'ar saidai ya kasance mutum me yawan shiga wasu ƙasashen wataƙil a can yake gudanar da kasuwan cin sa shiyasa babu wanda yasan me yakeyi da har yatara maƙudan kuɗaɗen nan haka, Alhaji Ɗan Ijje ta wani fanni yana da kirki ya iya zama da mutane idan yaso kuma idan kabishi sau da ƙafa sannan yanaso yaga kowa yana jin tsoron sa, saidai yana da son kuɗi matuƙa sannan yana da son yara akan ƴaƴan sa baiƙi yasa a kashe mutum bama baya so a taɓama masa ƴaƴa, ya ɗaure musu gindi kowa yana abun da yaga dama acikin garin babu wanda ya isa ya takasu shiyasa suma suka taso basu da mutunci ko kaɗan, daga masu bin mata sai ɗan shaye shaye dan wasuma acikin su idan suka bushi iska sai subar ƙasar ma gaba ɗaya sai su shafe watanni kafin su dawo gida, acikin su kuma babu wanda yake sana'a makaranta ma kuma sai sunga dama suke zuwanta, yana da mata uku, Sabeena, Khattume da Jannat, yana da yara guda biyar, Shuraim, Bilal, Ma'aruf sai mata guda biyu Abeeda da Hafsa,  Sabeena itace mahaifiyar Bilal da Shuraim, sauran kuma ƴayan Khattume ne matanne manya sai autanta Ma'aruf, ita kuma Jannat bata da ɗa ko ɗaya, shiyasa bayan rasuwarsa Sabeena sai ya auri Jannat to ita ta riƙe Shuraim da Bilal tun suna yara, dan ko da suka taso ma babu wanda yasan ba itace ta haife su ba, saidaga baya suka sani,

💧💦SU WAYE SU....!?💦💧Where stories live. Discover now