Episode 2

1 0 0
                                    

*💦SU WAYE SU...!?💦*
          *_(Who are they...!?)_*

              
     _💦Story and writing💦_
                         💎
          *🌬️Yaya Azeema😎*
   ______________________________
                      
               
                   *_episode 2💧_*

                         
             💧💦محمدالرسوالله..!💦💧

Bissmillah.....✍️

"Duk wannan budurin da suke babu wanda yasan meke faruwa da ƴan cikin motar domin zufa tagama wanke musu jiki gaba ɗayan su, duk da sanyin AC dake cikin motar hakan bai hana gumi fita daga jikin su ba, kowanne su yayi ƙuru da ido yayin da gaban su ke dukan dari ɗari, sun tsorata matuƙa kowa acikin tashin hankali yake, dan basu san ma ta ina zasu fara yi musu bayani ba.

'Wata ce tace; "JANNAT...! "wai jiran me muke tunda bazai buɗe ba mu ai sai mu buɗe sa tunda jan ajin nasa yaƙi ƙarewa, nasan yana kallon mu yayi mana shiru, tayi maganar tana kallon glass ɗin motar da take tunanin yana gurin wataƙil ma ita yake kallo.

"Hmmm kema aikin san halin BILAL yanzu hakama wannan abun da muke duk a banza baisan muna yiba, ya nan yana baccin da yasab...

Tun kan takai ƙarshen maganar tata, yarinyar da tayi magana ɗazu tace; "Ni nasan ma UNCLE baya cikin motar nan dan jikina yabani wataƙil ma yana waccen motar. ta nuna motar bayan ta, duk bin gun sukayi da kallo, Amma babu wanda yabar wajen.

Wacce aka kira da Jannat tace "Bari kuga tana faɗar haka tasa hannu ta buɗe motar, wayam suka gani babu kowa abayan motar,

A kusan tare wasu suka ce Kashhh...!! Suna me dafe goshin su cike da rashin jin daɗin rashin ganin sa, ashe duk wannan abun da sukayi daman baya ciki,

Yarinyar ce ta kuma cewa "You see what I'm saying... Tayi maganar cike da ɗan iyaye harda taɓe baki tana yi musu nuni da hannu ta.

Ta gefen tace ta ɗan dungurar mata kai tare da cewa "MUBEENA iyayi ai ba faɗar kice tasa hakan ba,

Bata kulataba tayi ga ta nufi wajen wata motar, tunkan ta ƙarasa ma aka buɗe motar, tsayawa tayi tana jiran taga me fitowar...

Sauran ma duk maida hankalin su sukayi ga wajen motar.

Ɗaya daga cikin Bodyguard ɗin sane ya fito daga motar ciki da ƙarfin hali, dan yadade zaman bazai musu ba shiyasa suka yanke shawarar gwanda kawai sugaya musu ayita ta ƙare,

Yanzu ma de ba haka suka so ba, dan ba wanda suke son gani ba suka gani.

'Yana fitowa sauran ma duk suka shiga fiffitowa har suka gama fitowa gaba ɗayan su.

Cike da ƙaguwa Mubeena tace "UNCLE BILAL...! ta kira sunan sa tana jiran taji ta inda zai amsa.

Gaba ɗayan su suka haɗu a waje ɗaya kallo ɗaya zakayi musu ka fahimci ba ƙalau suke ba.

Wata mata ce ta ƙaraso gurin su cikin tsuke fuska take binsu da kallo kafin daga bisani tace "Where is Bilal...!?  Tayi maganar tare da ƙara canza yanayin ta, dan jikin ta yabata Bilal baya cikin ko wacce mota musamman da taga yanayin fuskokin su ya sauya tasan something is wrong,

Gaba ɗayan su shiru suka yi tare da sinnar da kansu ƙasa, babu wanda ya iya furta komai saboda sunfi kowa sanin wacece ita.

Cikin ɗaga musu murya sama tana me daka musu tsawa tace; "Ku bani amsa. Nace ina Bilal? Me yasa kukayi shiru Answer me. I said where is Bilal? Why are you silent? Ina yake..!?? maganar take ko tsayawa batayi cikin fara hassala tana tsare su da manyan idanunwan ta dara dara tubarkallah.,

💧💦SU WAYE SU....!?💦💧Where stories live. Discover now