Hameed da mummy ,da Hisham Na zaune ah parlor.
Hameed Na kwanche da kansa Akan kafar mummyn sa Yana Bata labari Wani aiki da yayi ah Sudan.
Ahakan ya Hada Ido da Mimi tayi masa matukar kyau ,ya Mantar da kanshi Wani duniya.
Maganar ta be yasa Shi dawo hayachin sa.
"Sannun ku da hutawa mum"
Ita da Farhana suka fada lokachi daya."Thanks,Ina zaku "ya Hameed ya amsa kamin mummy.
"Saloon"farhana tayi kokarin kare su da sauri domin ta san idan har ta bar mimi ,yau asirin su zai tonu.
"Mummy,sun gaya miki ne" ya kalla mummy yana mai tambayarta.
"Eh sun tambayeni bayan breakfast,za zu dawo yanzu aii wanke gashi ne kawai"mummy takare su,
suka ji wani irin farinchiki."Ku jira ni bari na dauko car key dina" ya fada yana mikewa ko kallan su bai yi ba ya fiche ya nufi part dinsa.
mimi kam kamar ta matse wuyar shi,farhana kuma zama tayi kusa da mummy tana tura bakin ta.
"Haba mummy,mun girma fa ,we can go out on our own"
"Sai ki fada wa yayan naku pisararriya"mummy ta dauke remote har dariya ya kusa kubuche mata,ta kalle mimi yardatayi shiru ah tsaye.
ya hameed ya sako wani maroon jallabiya, da ya mugun karbe shi,sai kuma shekin kamshin da yakeyi.
" mummy sai mun dawo"ya fada yana manna mata kiss ah goshin ta.
"Allah ya kiyaye ,sai kun dawo ko" tafada tana musu addua gabadaya.
Da sauri mummy ta pashe da dariya
"Nasan ba wani saloon za suje,nikam nagode da Allah ya hada mun su da hameed"
bayan ta fada hakan,ta tashi domin zuwa kitchen tayi musu lunch kamin su dawo.☆☆☆☆☆☆
Duk da basu yi niyar zuwa sallon ba,haka suka hakura suka je aka yi musu afani da kayan sallon din aka wanke musu.Ameerah ,mai saloon din tayi mamakin yarda basu zo da hair kit dinsu ba.
haka ya hameed ya jira su har suka gama,
Mimi che ah front sit da suke komawa, ta wani murtuke fuskar ta duk mind dinta baya nan.
tana tunanin wani karya zata yi wa muhsin,da basu samu zuwa lunch dashi ba.Sai wani satan kallon ta ya hameed yakeyi don gaskiya tayi matukar kyau da atamphan jikinta ,musamman ma bayan da aka gyara mata gashin ta ya kara haska kyakyyawar fuskar ta.
Assalamualaikum!
karku manta kumana liking,commenting .muna nan ah instagram as books_bynajaatu
you can follow us.Muhsin yana ruwa 😂
so waye ne shi?
ya hameed is too strict😩😂©najaatuzubairu.
YOU ARE READING
MATAR CAPTAIN.
Romance"Mimi haka Allah ya kaddara za mu mutu mu barki....kiyi hakuri ki yafe Mana kuskuran mu,Allah ya baki miji nagari dauta, da zuri'a dayyiba,naso Naga mun aurar dake Amman lokachin mu yakare ah duniya,Mimi ki karba kaddarar ki ko tayaya ta zo Miki dom...