Bayero university Kano,
11:43amHanan pov
Tsaki nayi tareda gyara zamana Kan wani cement chair dake waje. Yau kwana biyu kenan da fara zuwana BUK. Ga rana da akeyi. Tafiyar wani naji, da sauri na juya saboda akwaini da tsoro. Wata ce da baxata fini ba, fara ce tana da dan tsawo. Murmushi tayi tareda zama kusa dani.
Mikomun hannu tayi tace "hii". Murmushi nayi nima tareda Mika mata hannu "salamu alayki". Amsawa Tayi da "wa'alaykis Salam".
Haka har nasan sunanta wato Fatima elbasheer lamido, ita yar sarkin Kano ce. To Amma mamakina shine metakeyi a wannan school din?Muryarta ce ta katseni da cewa "so hanan a wani unguwa kike?".
Amsawa mata nayi da "kinsan tarauni?". Gyada Kai tayi tareda cewa "eh mana, sosai mah kuwa".***
Second lecture muka shiga tareda ita. Fatima tazama tamkar yar uwa a wajena. Mun Saba da ita sosai saboda halinmu yazo kusan Daya. Akwai wata rana Muna zaune a hall, saiga wata bahijja da ake cewa a class dinmu ta karaso wajanmu. Kallona tayi tace "sannu". Kai kawai na daga mata Sannan ta Kalli Fatima tace "sannu yar sarkin kano".
Hankali tashe Fatima ta kalleni tace "waya fada Miki?". Wani irin murmushi tayi tace "wako zai fadamun, baga wayata ba". Saida ta gama ta mike ta tafi.
Haka dai wannan bahijjan ta dinka takurawa Fatima har takaiga wata rana, Muna zaune ta Fadi wani abu aikuwa sunsha dambe. Ban taba ganin fushin Fatima ba sai ranar.
Abunku da freshers sai gasu a office din HOD. Ranar dai hankali tashe muka koma gida...Next day...
12:22pmMammah ce ta kalleni tace "banganeba hanan, shi Ahmad din mene aibunsa?". Shiru nayi Ina nazari, ya ahmad yanada kirki ba laifi, Amma banida ra'ayinsa gaskiya.
A hankali nace "gaskiya mammah I don't really like him, banida ra'ayinsa neh". Gyada Kai tayi tace "haka ne, ba'a forcing mutum akan abunda baya ra'ayinsa gaskiya, to Amma wa kikeda shi?. Dariya nayi nace "tukunna dai mammah, you should wait for the Khair inshaa Allah 🤍"....Yo!
Hi salam-alaykum everyone!
How's your day?
I hope you are doing good.
It's the second chappy after all, I hope you enjoy itt..
Can't wait for the vote, comments and sharings
Much love 💕😘Yours_rosewithhanany
YOU ARE READING
HADUWATA DAKAI
RomanceMeet the prince charming handsome man yarima nurain elbasheer lamido, first born of the king of Kano State A story of two souls coming together through his sister Cute lady of 19 hanan Ahmad Zayd....