chapter 3🌼

18 3 0
                                    

Kano, Nigeria
12:11pm
......

                         Yarima nurain pov

  Kano is a little bit sunny. Furzar da iska me dumi nayi tareda kallon hanya, Kano akwai mutane. Muryar dogari naji Yana cewa "yarima ankusa karasawa masarauta". Gyada masa Kai nayi tareda kallon wayata dake Kara. Kamar kullum, karawa nayi a kunne tareda cewa "barka da rana giwar sarki". Dariya tayi tace "gidanku yarima, I hope ka iso lafiya". Dan murmushi nayi da na jima banyiba nace "alhamdulillah Mami". Haka muka karasa magana harta katse.

Bamu jima ba sai gamu a masarauta. Bayan an gama parking motocin, na shiga sashina ba tareda na shiga wajan Mami ba ko Mai martaba. Tura kofar nayi a hankali tareda shiga. The parlor is neat and tidy, abu Daya ne na kalla naga baiyimun ba, air conditioner da ba'a kunna ba.

Rungumeni naji anyi ta baya, da sauri na Kalli Wanda ya rungumeni. Arfat is crazy sometimes. Playful punch na Kai masa Yana kaucewa. Kamo hannuna yayi yace "yayaa...shine ko kira?". Girgiza Kai nayi nace "meyasa zan kira?, Wani abu kakeso?". Gyada Kai yayi tareda cewa "yaya, kasan inason addu'a fah kasani".

Tsaki nayi nace "arfat kana abu kamar ba Dan shekara 28 ba, ni matsa ka bani wuri, am so exhausted". Dariya yayi yace "naji, bari na hadama ruwan wanka". Dariya ya bani nace "dama Kai ke hadamun ruwan wanka?, Yaushe ka fara kenan". Dariya yayi sosai Sannan yace "toh yaya enough for the joke, Mami tana kiranka fah".

Kallonsa nayi cikeda mamaki nace "tun yaushe take kirana?". Sosa Kai yayi yace "umm...umm...tundaa..na shigo nan". Gyada Kai nayi, Allah ya shirye arfat, har yau da sauran hankali a tare dashi.

Tashi nayi na nufi daki bayan na huta na wasu mintuna, na fada toilet Dan watsa ruwa.

***----***

Sannu yarima "cewar Mami". Kallon arfat nayi nace "Mami be fadamun ba Saida ya gama shirmansa". Kallonsa tayi tace "ai na sani, dama munyi waya ne da kakarku tace Ina kake, so shine fa na aikashi ya kiraka". Nasreen ce ta fito tareda ihuu. Kallonta nayi nace "oh, dama kina nan?, Ina makarantar?".

Mami ce tace "wato yarima Kai komai baka saniba a gidan nan". Girgiza Kai nayi tareda cewa "ba haka baneba Mami, kawai dai kinsan bana shiga abunda babu ruwana".

Wayar da tayi Kara ce ta katse mana hira. Mami ce ta daga, harta gama wayar hankalina na Kan waya. Salatin da Mami tayi ne yasani dagowa, a hankali ta ajiye wayar tace "yasalaam! Me fadimatou ta aikata haka?". Arfat ne yace "Mami meya faru?". Nasreen ma dake zaune tana waya tace "Mami laifi tayi neh?".

Duk bata basu answer ba saida na riko hannunta nace "what's wrong Mami?". A hankali tace "fadimatou tayi laifi ne a school, please yarima jeka kaji mene I got a call from the HOD".

Hello lovelies 🌼
How are you doing?
We are still going on "haduwata dakai "...
Don't forget to follow, comment, vote and share
Much love🥀

  Yours_ rosewithhanany 🤍

HADUWATA DAKAI Where stories live. Discover now