chapter 4

4 1 0
                                    

Kano, Nigeria
1:21pm
****

  A hankali na tako daga mota zuwa gaban office din HOD din BUK. Ganin idanu sunaso sumun yawa yasa nayi saurin shiga Kai tsaye.

Dagowa yayi tareda kallona, daga bisani yace "sannu, please come over". Karasawa nayi na zauna Kan Daya daga cikin kujerun office din.

Fadimatou dake durkushe itada wata, probably wadda sukayi fadan sai wani kauda Kai sukeyi. Mutumin ne ya katseni da cewa "Good day sir". Gyada Kai nayi nace "same prof.auwal, mene ya faru?".

A hankali ya fadomun yadda abun ya faru Sannan nace "professor ni a gidanmu ba'a fada, bansan Ina ta koya ba... depending on her status..koda yake, I will deal with her".

Prof ne yace "ah haba yallabai ai ba saeka hukunta ta ba, ai batada laifi, kawai dai ayi fadan Kar a sake maimaita irin haka tunda dai naga daga babban gida ta fito".  Karamun tsaki nayi nace "ba wannan ne matsala ba, Saka Mami cikin damuwa da tayi, I hope that won't repeat itself, you get it?".

Da sauri ta gyada Kai Sannan na Kalli Dayar yarinyar nace "uhm Kinga". Dagowa tayi ba tareda ta kalleni ba nace "kinason rama dukan da tayi Miki ne?ko kuma kudi kikeso?". Amsawa tayi da "no ba saena rama ba, ya wuce ai".

Harna gano inda ta dosa, na karbi acct number dinta na tura mata 500k tareda cewa "I hope bazan Kara Jin haka ta faru ba". Da murna ta fita office din aka gama case din.

~~~°°°~~~

                             Hanan pov

Tashin hankali Babu irin Wanda ban shiga ba. Fadimatou tana chan cikin wani hali. Fitowata kenan daga lecture saboda su suna wajan HOD.

Zarya kawai nake a kofar office din ban aune ba naji nayi karo da wani abu. Its probably not a human being right?

But am wrong, mutum ne sosai ma. Saida kaina ya gama juyawa Sannan na matsa ya wuce. Tunanina kawai wani irin mutum ne wannan??

Ana haka sai ga fadimatou ta fito tana hade rai. Rungumeta nayi nace "oh what a complicated dayy". Bayan nayi releasing dinta ta kalleni tace "hanany wai ni yaya zai watsawa kasa a ido".

  Ban gane inda ta dosa ba, Dan haka nace "ban gane ba". Furzar da iska tayi tace "he gave out 500 thousand naira to that filthy....". Katseta nayi da cewa "noo don't!, Karki zageta, aniyarta ta bita okay, remember what comes around goes around".

  Murmushi tayi tace "har Kinsa hankali na ya kwanta, but I was just fuming inside dazu, harda cewa ko zata rama dukan". Dariya nayi nace "kaiii haba dai, meyasa babban yaya yake haka ne".

Tabe Baki tayi tace "saisa nafi gane ya arfat yazo, Amma Mami ta turomun wannan mutumin gashi ya gama tabamun rai ya tafi ai".

.....

Haka dai har muka shiga lecture din karshe aka fito kowa ya fara hanyar fita. Fadimatou ce tace " hanany yau Dan Allah ki bari mu tafi tare, kinsan na Dade Ina pleading".

Ni kawai a rayuwata ban taba sha'awar wani ko wata kawata su ragemun hanya ba, gidanmu ba'a so ma gaba Daya saisa baya cikin tsarina.

Haka dai har saeda na yadda na bita suka ajiye har kofar gida. Zuciya ta sai bugun tara-tara take saboda ban Saba ba. A haka dai muka rabu bayan munyi sallama na wuce gida......



Hii lovelies 🌼
It seems like am having low viewers, comment, votes and followers...
Though I won't get tired of making an update for the available people to view and recommend 🤍
Much love
Don't for to vote, comments and share

Yours hanany

HADUWATA DAKAI Where stories live. Discover now