1

9 1 0
                                    

Chakwakiyar babban gida

1

"Shikenan yanzu malam ya tafi". sadiya ta faɗa tana kuka.

Matan suna zaune a parlourn Alhaji yau sadakan bakwai na malam.

"Sadiya addu'a zaki mishi".aunty fatee ta faɗa tana rarrashin ta.

"Nifa ban gane ba,yanzu Habib ne ya kashe malam kenan?".munal tayi tagumi tana tambaya.

"Shi ya kashe shi mana tunda sunan shine a rubuce". kauthar ta faɗa da ɓacin rai.

"Ba hujja kauthar ki Dena faɗan haka".mama ta faɗa da takaici.

"Mama ai dan yaron ki ne shesa kike faɗan haka".Maryam ta faɗa da haushi.

"Ke wannan wani irin magana ne?,ai gaskiyan ta ba hujja balle ace za'a kama shi".aunty fatee ta faɗa.

"Ba wani ai da kanshi ya rubuta dan ya nuna mana shi ne amma yanzu dan yaron ta ne take kare shi".sadiya ta faɗa tana hararar su.

"Wai me yake damun kune?,da mutuwan malam zamu ji ko da suruntun ku".aunty fadila ta faɗa a fusace.

"Wallahi baku isa ba,bazan zauna Habib ya kashe min malam ba ku kuma kuna biye mishi".Maryam ta faɗa da haushi da raini.

"Maryam ki nitsu ki zauna dan Allah ku Dena irin wannan abun".maman ta ta faɗa ahankali da sanyin jiki.

"Mesa zamu nitsu,kina ji dai suna cewa wai ba Habib bane ya kashe malam bayan shi da kanshi ya rubuta sako, wallahi mama kisan yanda zakiyi ko kuma karan ki zan kai".sadiya ta gama maganan tana kallon mama dake tagumi.

"Ke sadiya ita sa'ar ki ne?!!!!".Malik da suke shigo wa da sauran mazan ya faɗa a fusace.

"Yaya Malik sune fa wai ba Habib bane ya kashe malam bayan sarai sun san shi ya kashe shi".sadiya ta tashi tana kallon shi.

"Shine zaki dinga mata magana kaman sa'ar ki".Malik ya faɗa yana kallon ta da haushi.

"Eh anyi,kuma wallahi se na samo Habib na kash--".bata gama maganan ba Mustapha ya tsinka mata mari.

"Ke baki da hankali ko?,shi sa'an kine ko sauran sa'an kine da zaki dinga faɗan Irin wannan maganan?". Mustapha ya faɗa a fusace.

"Wallahi Ni barin gidan nan zan yi,in kana so na ka bini mu tafi".sadiya ta gama maganan tana kallon Malik.

"Ke sadiya ba inda zaki je".harun ya faɗa yana kallon ta.

"Ba wanda ya isa ya hana Ni".sadiya ta faɗa tana kama hanyar kofar parlour.

Karan shigan message ne kawai kake ji a parlourn,duk suka duba wayan su.

Sakon shine kamar haka;

Ina so kowa ya zama yana babban gida,duk wanda ya tafi shi ya jawo wa kanshi.tashin hankali kuma yanzu kuka fara gani.habib❤️

"Yaya kalla abun da Habib ya tura". khairat ta faɗa tana nuna wa kalil dake kallon sakon a wayar shi shima.

"Ni me yake damun yaron nan ne". Mansur ya faɗa da haushi.

"Yanzu har Habib ya isa yace mu zauna a gida kuma mu zauna ne?".Anam ta faɗa tana kallon su.

"Sadiya ki zo nan".kalil ya faɗa yana kallon wayar shi.

Sadiya itama data karanta sakon ta dawo kusa dashi.

"Kar in kalla ƙafan kowa a waje".kalil ya faɗa yana fita daga parlourn.

"Salma ku tafi side naku". mommy ta faɗa tana sauke nunfashi na damuwa.

(Salma matar masir ne yaron su ɗaya sunan shi zahir, shekarar shi biyu).

chakwakiyar babban gida Where stories live. Discover now