CHAKWAKIYAR BABBAN GIDA
5
Duk suka juya a tsorace suna kallon ta inda karan ya tafi.
Alhaji Aliyu ne aka harɓa a kafaɗa.baba dake kusa dashi ya zabura amma bai tashi ba.
"Wayyo Allah alhaji na!!".raisa ta sake ihu tana kallon Alhaji Aliyu da yanzu yake kwance akan cinyar baba yana riƙe hannun shi da ciwo sosai a fuskar shi.
"Zaku bamu shi ko se mun kara wa wani".ɗaya daga cikin su ya faɗa.
"Ke munal dan ubanki ki basu yaron nan".aunty zainab ta faɗa a fusace.
"Wallahi bazan iya ba yaro na ne fa".munal ta faɗa tana kara kamkame Hafiz da yanzu yake kuka dan karan bindiga.
"Ok mu wannan ba matsalar mu bane,muna da enough bullet da ze hallaka ku gabaɗaya".ɗaya daga cikin su ya faɗa yana wasa da bindigan hannun shi.
"Kuyi hakuri zamu baku".mama ta faɗa tana kallon munal akan ta basu yaron.
"Wallahi se de ku kash--". Munal bata ƙarasa maganar ba suka ji wani harɓi.
"Wayyo hannu na!!".walid yayi ihu yana riƙe hannun shi da aka harɓa.
Mama ce ta tashi ta janye Hafiz daga jikin munal ta miƙa musu tana cewa"ga yaron dan Allah ku fita mana daga gida".
Jan shi sukayi yana ta ihu yana kiran maman shi amma a haka suka fita dashi.munal kuka take kamar wanda akayi wa albishir na mutuwa.
"Fatma ku tashi ku duba su". daddy ya faɗa yana ɗaga alhaji Aliyu dake nunfashi dakyar.
"Aliyu karka rufe ido".baba ya faɗa da damuwa.
Fatma da Anam da sauri suka je kawo abubuwan aiki,Raisa kam se kuka take.
Umma taje kan Walid dan itama nurse ce a baya,su Anam kuma suka je kan Alhaji Aliyu.
"Ba alluran Anaesthesia".Fatma ta faɗa a tsorace.
"Fatma time yana tafiya kawai muyi a haka".Anam ta faɗa tana barga rigan shi.
"Anam akwai matsala fa,ko mun cire bamu da kayan aiki kuma ciwon ze iya jawo mishi Matsala". Fatma ta faɗa.
"Muyi abu ɗaya kawai".Anam ta faɗa.
"Daddy ku riƙe shi".Fatma ta faɗa.
Riƙe shi sukayi sosai.
Se ihu yake kamar ana cire ranshi,duk tausayin shi sukayi dan abun akwai tausaya wa.
An samu an cire bullet ɗin lafiya amma kawai se nunfashin shi ya ɗauke.
Anam zabura tayi zuciyar ta yana buga wa dan tsoro.
Anam danna kirjinshi ta fara(CPR)a tsorace amma baya nunfashi.
Fatma riƙe hannun ta tayi tana cewa"Anam ya rasu".
Anam komawa baya tayi ta wani fashe da kuka me bada tausayi.
Ai kuwa tuni babban gida ya cika da kuka da salati.
Walid kam an samu an cire mishi amma shima yana cikin azaba.
(Bayan sati ɗaya).
"Munal wallahi bazan taɓa yafe Miki ba kawai kinsa Alhaji na ya rasu akan yaron ki".Raisa ta faɗa tana kuka.zaune suke a filin babban gida suna zaman makokin Alhaji Aliyu.
"Ke Raisa kiyi wa mutane shiru".Fatma dake gefen Anam ta faɗa.
"Mesa zan yi shiru bayan kowa yasan laifin tane,kinsa an kashe min mahaifi sannan kika sa min miji jinya, wallahi kema zaki gani".Raisa ta faɗa.
YOU ARE READING
chakwakiyar babban gida
Randombabban gida(2). ku biyo ni dan ganin yanda chakwakiyar babban gida ze kasan ce da dangin Jaffa. bazeyu a karanta wannan shi kaɗai ba se an karanta babban gida.