CHAKWAKIYAR BABBAN GIDA
3
"Yaya kalil".kalil yaji Muryar Habib amma kuma baiji alaman mutum ba.
"Habib ina ayan yake?".
Murmushi Habib yayi"mesa kake sauri".
Se yanzu kalil ya gane cewa daga speaker Muryar Habib yake fitowa.
"Habib ina ayan?".ya kara tambayan shi.
"Zan baka ayan amma da sharaɗi". Habib ya faɗa.
"Ina jin ka".abun ya fara bawa kalil haushi amma dole ya riƙe dan karya ɓata wa Habib rai.
"Ina so inna baka ayan zaka kawo min sadiya dan in hukunta ta da abunda ta faɗa akan mama na,in kuma baka kawo ta ba Nan da awa biyar to Ni da kaina zanzo kuma abun bazeyi daɗi ba wa dukkan ku,ka yarda?".a karshe ya tambaya.
Shiru kalil yayi yana nazari tukunnan yace"eh na yarda".
"Good choice".
Se aka kunna wuta yaga ba kowa a office ɗin,wani kofa aka buɗe se ga wani da ayan suna fitowa,ayan yana riƙe da motan wasa da chocolate a hannun shi.yana kallon Kalil da gudu yaje ya rungume shi.
"Are you ok?". Kalil ya tambaya da damuwa a fuskar shi.
"Yes I'm fine".ayan yayi murmushi sannan ya kama hannun Kalil suka fara fita.
"Your time starts now".yaji Muryar Habib.
Wuce wa wurin mota sukayi sannan ya kunna motar suka wuce.
A hanya ayan se hira yake mishi akan irin wurin wasan da yaje da abubuwan da yaci amma Kalil kawai murmushi yake yana tunanin yanda ze ɗauko sadiya.
Suna iso wa Laminu ya buɗe gate suka shiga sannan ya wuce yayi parking a wurin side nashi daidai lokacin kauthar ta fita daga side nata ita da arham yana bata labari.
Kalil fita yayi daga motar ayan ma ya fita,ai kuwa arham yana kallon ayan yaje da gudu ya rungume shi yana farin cikin ganin ɗan uwan shi.
"Sadiya ki fito ga ayan ya dawo".kauthar ta faɗa da farin ciki.
Kafin kace me duk sun fito ana mamakin ganin ayan yana farin ciki.
Sadiya da sauri taje ta rungume shi tana fashe wa da kukan farin ciki.
"Ayan kana lafiya?".sadiya ta tambaya da damuwa tana dudduba jikin shi.
"Mommy I'm fine".yayi murmushi yana goge mata hawayen fuskar ta.
"Kalil a ina ka same shi?".Malik ya tambaya yana shafa kan ayan da farin ciki.
"Habib ne yace nazo na ɗauke shi".kalil ya faɗa.
"Shine baka sanar damu ba ka tafi kai kaɗai".nasir ya faɗa yana kallon Kalil.
"Past is past". shureim ya faɗa.
"Habib ya bani ayan da sharaɗi".kalil ya faɗa yana shafa kanshi irin na gajiya.
"Me ne sharaɗin?".Malik ya tambaya yana kallon Kalil.
"Yace se na kai mishi sadiya kafin nan da awa biyar ko kuma yazo da kanshi".kalil ya faɗa da takaici.
"What?, wannan ma ai rainin wayo ne".harun ya faɗa.
"Me yake nema da matata?".Malik ya tambaya.
"Yace ze hukunta ta akan rainin da tayi wa mama".kalil ya bada amsa.
"What if taje ya kashe ta?".Walid ya tambaya.
"Bazan bari haka ya faru ba,i promise". Kalil ya faɗa daidai lokacin text ya shigo wayar shi.shiga yayi ya kalla;
YOU ARE READING
chakwakiyar babban gida
Randombabban gida(2). ku biyo ni dan ganin yanda chakwakiyar babban gida ze kasan ce da dangin Jaffa. bazeyu a karanta wannan shi kaɗai ba se an karanta babban gida.