Chakwakiyar babban gida
2
"Wayyo Allah ayan nawa".sadiya ta faɗi a ƙasa tana ihu.
"Bari mu kira su yaya a faɗa musu ko yana makarantar".Amina ta faɗa tana cire wayar ta.
"Habib ne ya ɗauka min yaro".sadiya ta faɗa tana kuka.
"Taya kika sani?".Anam ta tambaya.
Miƙa wa Anam wayar ta tayi inda ta karanta sakon da habib ya tura mata.zaro ido Anam tayi"innalilahi wa innailaihi raji un yanzu ya zamuyi?".
Sauran ma duk duba text ɗin sukayi ai kuwa duk suka rikice dan basu san me ze faru da ayan ba.
Anam kiran kalil tayi a waya ta sanar dashi,bai daɗe ba ya dawo babban gida daidai lokacin Malik da Jamil ma suka dawo.
"Muga text ɗin".Malik ya faɗa a fusace kamar wanda inka mishi magana ze mare ka.sadiya miƙa Mishi wayar ta tayi se ya buɗe ya gani, wani wurgi yayi da wayar a ƙasa.
"Ni Habib zeyi wasa hankali na!!".Malik ya faɗa a fusace kamar me hauka.
"Malik calm down bari na kira shi".kalil ya faɗa yana kiran Habib a waya.chan se ya ɗauka.
"Yaya kalil".habib ya faɗa da Muryar shi na izza.
"Habib ina ayan yake?". kalil ya tambaya da haushi a Muryar shi.
"Gashi nan a wuri na wai shi baze dawo ba". Habib ya faɗa ta cikin wayar.
"Ka dawo dashi ko in kai ƙaran ka!!".Malik ya faɗa a fusace.
Dariya me sauti Habib yayi sannan yace"ka ta ɓa ganin ɗan babban gida a prison ne?,ko ka manta girman dangin Jaffa ne balle ma Ni da nake lawyer,ai yanzu nafi karfin ku yaya Malik,Ni zan faɗa abu kuma dole ku bi".
"Habib danallah ka dawo min da yaro".sadiya ta faɗa tana kuka.
"Sadiya wannan punishment naki ne na raina mama da kikayi,ayan kuma se ranan da naga daman dawo dashi ze dawo". Habib ya faɗa sannan ya katse wayar.
"Na shiga uku Ni sadiya, Dan Allah yaya ku taimaka min da yaro na". sadiya ta fashe da sabon kuka,Kana ganin ta zaka tausaya mata.
Kalil da haushi ya wuce side nashi, Malik ya ɗaga matar shi suka shiga side nasu.
"Nifa abunnan ya fara bani tsoro".Anam ta faɗa tana kallon Raisa.
"Ka da muma dai ya ɗauke yaran mu".Salma ta faɗa ba damuwa a fuskar ta ko kaɗan.
"Addu'a kawai zamuyi tayi komai ze wuce".Anam taja hannun yaran ta suka wuce cikin side nasu.
Anam tana shiga ta shirya yaran ta sannan suka zauna cin abinci banda kalil dan ta kasa zuwa ɗakin shi ta kira shi dan tasan yau yana jin haushi sosai.
"Aunty Nam Nam wanda ya bamu chocolate yace wai shi uncle namu ne".aslam ya faɗa yana sa abinci a bakin shi.
Murmushi tayi wanda bai je har zuciya ba tace"eh uncle naku ne amma in kun kara kallon shi karku je wurin shi".
"Mami why?".islam ta tura baki tana tambayan ta.
"Nothing".Anam ta sauke nunfashi na takaici dan batasan ma taya zata faɗa musu Habib ze iya cutar dasu ba.
Sanda suka gama cin abinci Anam ta shirya wurin sannan ta tura su side na Farida dan a wurin suke karatu.
Ahankali ta tura kofan ɗakin shi ta shiga.a kwance ta same shi yana kallon sama,kana kallon shi zaka san da damuwa a fuskar shi.
"Yaya".ta zauna a kusa dashi.
"Umm".ya lumshe ido yana jan hannun ta kan chest nashi.
"Yaya stop worrying yourself".ta kwanta akan kirjinshi tana lumshe ido itama.
YOU ARE READING
chakwakiyar babban gida
De Todobabban gida(2). ku biyo ni dan ganin yanda chakwakiyar babban gida ze kasan ce da dangin Jaffa. bazeyu a karanta wannan shi kaɗai ba se an karanta babban gida.