A short story

89 17 18
                                    

By Bara'atu Yahaya Garba

Rayuwa cike take da taraɗaɗɗi, na juya gabas da yamma, kudu da arewa a tsakiyar farfajiyar gidan namu amma babu koh mutum ɗaya da zai taimake ni a halin da nake cike. Na kusan rabin awa kwance amma koh leƙe babu wanda ya leƙo ni.

Gashi dai nayi abunda zuciyata ta ayyana mun amma kuma ƙaiƙai ya koma kan masheƙiya kamar yanda reshe ya juye da mujiya. Hawaye ne keta zirya a kumatuna amma kuma na kasa ƙwaƙwaran motsi ballantana har nayi yunƙurin goge hawayen.

Koda na goge hawayen ba lallai ne na iya goge abunda ya faru ba saboda abunda ya faru tamkar rubutu ne da aka karta a jikin dutse wanda har abada bazai taɓa gogewa ba.

Wane irin baƙin fenti nayi ma kaina? Wace irin rayuwa na jefa kaina? A wannan lokacin nayi dana sani. Sai dai kuma kash! Bakin alkalami ya riga ya bushe, dana sani kuma ƙeya ce.

Nayi kuka kamar raina zai fita harna hakura na share hawayena saboda babu mai lallashi. Na fitar da ran wani zai sake kula ni acikin mutan gidan namu sai ga mahaifiyata ta fito ta ajiye mun kofin ruwa da kuma kwanon abinci, bata ce mun uffan ba ta koma ɗakinta. Koh bakomai uwa uwace.

A halin da nake ciki bana jin zan iya cin abinci. Abinci baya gabana, neman yafiya shi ya kamace ni. Nayi dana sanin rashin bin maganar mahaifina. Yakan ce "Nana, kar Allah ya baki ikon cutar da wani koda ta lafazin baki ne." Sai gashi cutarwar da nayi ba iya lafazin baki ya tsaya ba. Kaico!

Baƙin ciki, Ƙyashi, Hassada, Jin Zafi! Ya jefa ni ga halaka. Na fara tiryo munanan abubuwan dana aikata.

Ni ce ta farko acikin yara uku da iyayena suka haifa. Sunan Iya, Kakata naci wato Nana Faɗimatu. Gabaki ɗayanmu 'yanmata ne Allah ya azurta ma iyayenmu. Mahaifiyarmu tasha matukar wahala wurin dangin miji akan cewa bata haifi Magaji ba sai dai dayake Umma mutum ce mai tawakkali shiyasa ta toshe kunnuwanta.

Iyayen da kan nuna alkunya akan yaran fari amma ni sam iyayena sun jani a jiki, gata bakin gwargwado na samu. Umma tayi matukar jajircewa akan tarbiyar mu. Baba kullum burin shi ya kyautata ma iyalinshi.

Ina da shekaru Ashirin, Zeenatu mai bina nada shekaru sha takwas a yayin da autarmu Aziza keda shekaru sha shidda, Allah yayi wa Mahaifinmu rasuwa. Dattijon kirki wanda har ya koma ga Allah kullum addu'arshi bata wuce Allah ya bamu mazaje nagari ba.

Ba karamar fafutika Umma tasha ba bayan rasuwar Mahaifinmu wurin tarbiya da kuma ciyar damu, ta rike sana'arta hannu bibbiyu.

Abun mamakin bai wuce yanda samari ke tururuwa akan ƙannena ba amma ni tun bayan Lawan mai shayi daya taɓa nuna yana sona lokacin ina aji huɗu na sakandire na mashi tas ban sake samun wani ya nuna yana sona ba, lamarin dai kamar anyi ruwa an ɗauke.

Umma bata tsaya sanya ba, ta aurar da Zeenatu saboda takai munzalin auren. A lokacin ji nayi kamar na haɗiyi zuciya saboda baƙin ciki. 'Yan uwanmu da suka zo biki nata kara rura mun wuta cikin zuciya. Sai faɗi suke "Nana ba mashinshini." Bazan iya misilta tashin hankalin dana shiga ba a wannan lokacin.

Sau biyu ina zana jarabawar Jamb amma Allah bai nufa zanci ba. A lokacin da Umma ta bani shawarar fara difiloma, ji nayi kamar an buga mun guduma a kaina, kamar saukar aradu haka naji maganar Umma acikin kunnuwana.

Ya Umma zatace na fara Difiloma bayan ga Zeenatu chan tana digiri har zata shiga aji biyu a jami'a, uwa uba kuma tana zaune lafiya gidan miji. Haka nayi kunnen uwar sheggu da shawarar da Umma ta bani. Na dinga ayyanawa a raina wannan ai gurguwar shawara ce.

Ban sake shiga tashin hankali ba saida naga autarmu Aziza taci jamb ga kuma shirye shiryen bikinta anayi. Babu yanda banyi ba dan in hure mata kunne amma taƙi saurarena. Ranar da aka miƙa Aziza gidan miji, kasa bacci nayi. Sai tufka da warwara nake yi.

Hana wani hana kaiWhere stories live. Discover now