*CIKIN DA BA'ASO*
(unwanted pregnancy)
*@HUMAIRAH B MELODY*
_*Dedicated to my group members Wato MELODY NOVEL GROUP😘 Tnx for the love and care*_👏🏻
66-70
Meye wannan tafadi tareda tunanin abunda zai sanar da ita
“Mash Pills ne na hana daukan ciki saboda mu more amarcinmu koh kinfiso yau kidau ciki gobe kifara laulayi?”
Mashahura ta gyada kai alaman ah ah wata irin murmushi yayi cikin ransa yace
Haka nakeson mace mai saurin fahimta ba irin Atee ba itama Nasan rashin ilimi ne kawai ke damunta, glass cup ya dauko da ruwan EVA ya bata pills din guda biyu Wanda basaina gayawa mai karatu irinsa ba haka MD fauzi yadinga yiwa Mash hudubar shedan akan daukan ciki harta fara dauka.
Akwana a tashi wajen Allah MASH tayi kwana bakwai cikin na takwas Atee ta amsa girki cikin ikon Allah Atee ta maida komai ga Allah saidai tadauki aniyan cewa ciki kam saita dauka don su bakwai iyayenta suka Haifa Pills kuma batasha, A dinning ta shirya komai na abinchi akaci aka sha Mash sai santi takeyi dare nayi Atee tayiwa BB kamal shinfida a gadonsa Sannan ta shirya cikin gaya nagani na fade Atee dai in takaitawa mai karatu tazama sisi Lagos wani ya ganta zaice yar jami'a ce, A Daren sunyi wani Abu wai lalata kowa ya nuna irin kewar Dan uwansa dayake Abun ba'a magana bayan sunyi komai sun kammala MD fauzi ya dauko same pills din dayaba Mash yaba Atee cikin rashin fahimta tace
“meye wannan? Look MD nifa baxan dauka ba shan pills Nada matukar hatsari baxan sha ba ciki ai bakaina farau ba kuma wayace maka ciki koda yaushe yake shiga mace? Look MD fauzi nifa wannan Abun shizaisa komai zai faru yafaru koh ka mance cewa shaye shayen magunguna yana haifar da mummunar illah Ga lafiyar bil adama? Koh ka manta cewa yana lalata hanyoyin jini da jijiya koh ka manta cewa pills yana iya kawo MATSALA ma Al'adar mace? Koh ina kake lokacin da pills ya lalatawa dubban mata mahaifa? Kana ina Cancer yake kashe mata? Look badaniba indai akan wannan ne zan iya hakura da Tarayya dakai na aure shine kawai mafita akan daukan ciki daga haihuwa daya”
Wani gigitaccen mari ya sakarwa Atee abunda bai taba gigin yimata ba ya nunata da yatsa yace
“Ki sani saikin fiskanci hukunci mai tsanani acikin gidannan don aurenki nakeyi yaxama dole kibi umurnina matukar Nike aurenki Sannan haihuwa nace ta isa haka tarbiyansu ma aikine kazo ka Haifa yayan suzama ba nagari ya kashi I will not take it any longer kisani duk Idan kika sake naga ciki a jikinki ina maiyi miki albishir da cewa saidai kisan yadda zakiyi dashi tunda ke bakida hankali Gashi Idan kikaso kisha Idan bakiso ba ki watsar”
Duk wainar da ake toyawa Mash tana labe tanaji duniya tayi mata sugar sai tsalle takeyi daki takoma don taji tafiya bakin gado ta zauna tace
Lallai nasamu dama in taka Atee tunda na lura batabin umurnin MD fauzi Niko inhar rashin daukan *CIKIN DA BA'ASO* Ne baxan tana daukaba muci love dinmu son rai.Sallama ne ya katse mata tunani cikin sauri tazo
“Sweet lafya naga ranka a bace? Meye ke damunka?
Namiji babu sirri tuni ya yayimo komai yasanar da ita sannan koh breakfast baiyiba ya fita
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Atee tazama Abun tausayi ta rame ta kanjame saboda masifar MASH da MD kowani kashi aka kwaso itace tunda MD yaga alaman ciki a jikin Atee yasa mata karan tsana koh inda take baya zuwa sai hantara da kyara aikin gidan dukya dawo hannunta hatta wankinsu ita keyi an maidata bola bola, wani Abun ma sai kayi kuka
Mash ce tafe cikin isa da kasaita tasamu Atee zaune tana bawa BB kamal abinci wani tsawa ta dakawa Atee tace
“Ke maza ki tashi ki wanke mun zanin gado kafin rana ta fadi saboda jiya nayi ambaliya Dayawa haka mijinki yi maxa banason bata lokaci”
Atee taji wani bakinciki har cikin ranta ta dago kai tace
“Karki damu zan wanke bari ingama ba BB abinchi bacci ya tashi gashi yunwa yakeji ”Ai mash tuni tasa kafa ta haure Abinchin tace “Har bawa BB abinchi yafi wankina tashi kin wani aje ciki a gaba cikin da ba'a maraba dashi”Atee saboda karfin imani takasa cewa uffan Sannan takasa kuka BB kuwa yana bude baki yace
“Umma abinchi zube Aunty muguwa”Atee tuni ta kwashe da dariya daidaida mash ta juya Atee tace “Allah sarki duniya Yaro kenan wai shima yasan Wanda baiyi masa daidai ba kai BB kamal yau kasa zuciyata tayi fari kal Nasan cewa yarona jarumine”.Comment dinku da like shine karin karfin gwiwa na........

ESTÁS LEYENDO
CIKIN DA BA'ASO(Unwanted pregnancy)
Ficción GeneralAn interesting story which no one will afford to missed join pls MD fauzi and his two wifes fighting over Pregnancy wat a pity Atika his first wife hv become a rag of mess bcos she refuse to be aborting their unborn babies while Mashahura become the...