BANI BACE

201 18 0
                                    

*BANI BACE

INNOCENT MARA LAIFI





*ELOQUENCE WRITER'S ASSOCIATION





Basira Sabo Nadabo





Wattpad
@
Basira_Nadabo











HML bro Yusuf Auwal


Wannan shafin naku ne jinie na 'yan uwa na rabin zuciyata, Hussain (ɗan hajiya), Maman Yasmien, DJ, Shu'aib (soja mazan fama), *Aunty Aisha Mom Nana(my second mom)*, da duk members ɗina da suke _Family Group namu wannan naku ne jinie na_. Onelurv❤





Dedicated To Ramalurv








9/08/2017





SHAFI NA ASHIRIN DA HUĎU



Alkali ya kara maimaitawa kotu nason ganin barrister Sulaiman Shu'aib a gaban ta


S.Man na gani tare da wasu mutane sojoji a bayan su daga ganin su kasan sun shiga hannun mazaje domin sun jimgu sun sha wuya fuskar shi harta canja kamar ba S.Man ɗinda nasani ɗan gayu da kwalliya ba lallai soja soja ne basa ɗaukan wargi, suka tsaya a gurin daya dace su tsaya


Ta taka zuwa gaban su tace kotu zata so jin sunayen ku, ko kunfi son na faɗa da kaina ne don muna gaban alkali mai karamci da adalci ne inhar baku bane a kotu zata sakeku ku tafi abinku amma fa sai kun faɗa gaskiyar lamarin akan abinda ya faru da waccen baiwar Allah ɗin

Na farkon yace sunana garba amma da garus akafi sanina dashi


Na biyu yace ni sunana mati,

Mati shine asalin sunan ka baka da sunan yanka ne


A'ah ina dashi toh amma na manta da sunan tun ina yaro abokaina suke kirana da mati shine ya ɓatar da asalin sunana sai inna koma gida zan kara tambayan mamata don ta tuna min

Kotun ta ɗauki dariya


Alkali ya buga guduma, kotun tayi tsit

No barshi kawai basai kaje ka tambaya ba malam mati


Ta tsaya a gaban S.Man tace malam kaifa ko baka da sunane ko kaima saika koma gida an tuna maka ne


Yayi mata kallon kaskanci sannan yace sunana barrister Sulaiman Shu'aib


Barrister baka karasa ba kace kaine lauya me kare mai kara kuma nayi mata zagon kasa saboda abinda duniya, barrister me Ysriema yayi maka kasa ka aka kashe shi ba tare da yayi maka laifin komai ba saboda wani mugun burinka tare da mummunar bukatar ka


Ni ban kashe shiba to me zaisa na kashe shi

Saboda yana son abinda kake so kuma tare da mummunar bukatar ka

Ta taka zuwa gabana tace Wahiedat ko zaki iya shaida wani fuska acikin fuskokin nan tare da nuna su


Na tsaya shuru ina kallon su ɗaya daga cikin sune tun shigowar su naga kamar nasan fuskar amma na manta inda nasan shi, na nutsu cikin tunani na sai can na ɗago tare da cewa wallahi shine, gashi nan, shine na farkon nan Allah kuwa shine musabbabin shiga na wannan halin wallahi shine na fashe da kuka

Yi shuru kiyi mana bayani, shine wa kiyi magana mana duk nan kin samu a duhu, Wahiedat shine wa

Naja hanci sannan nace shine wanda yazo ta bayan Yariema ya soka masa wuka nima gurin kare wani sarar da yakawo wa Yariema na tare shine ya yanke ni a hannun, na faɗa tare da nuna musu hannun

Kina nufin garus shine ya kashe Yariema Abbas?

Eh wallahi shine ya kashe shi, bazan taɓa mantawa da fuskarsa ba duk daya rufe ta amma gurin dana tare wukar abin fuskarsa ta fita shine yasa naga fuskarsa

Garus me yasa ka kashe Yariema me Yariema yayi maka da baka kaunar ganinsa a doron duniya, eh da kai nake magana

Nima sani akayi na kashe shi, bayin kaina bane


Waye ya saka ka kashe Yariema, kuma saboda me yace ka kashe shi

Yayi shuru kuma bashi da halamar magana

Waye ya saka ka kashe Yariema kayi magana ko maganar taka zata kuɓutar da kai domin kana gaban alkali mai adalci ne babu wanda zai danne maka hakkin ka, kayi magana garus waye ya saka kashe Yariema

Unhm ammnm, wallahi sani akayi

Eh to waye ya saka, sunan mutumin kawai zaka faɗa shikenaɓ ka kuɓuta daga wannan ɗaurin, ka kwantar da hankalinka garus



*Eloquence Writer 's Association



Karamar Su Babban Suce Ni Wato 'Yar Mutan Kd Ce

Basira Sabo Nadabo


Wattpad
@
Basira_Nadabo

BANI BACE Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt