AKAN SO(1) 1-20

1.6K 58 4
                                    

[9/15, 7:34 AM] Real Afreen ce💋: 🍓🍓🍓🍓🍓
      🍇🍇🍇
              🍡
   ~*AKAN SO*~

              Na

    *Faty Afreen*
           _(Real Afreen ce)_

~Bismillahir rahmanir rahim~

GODIYA

     _Godiya ta tabbata ga Allah ma daukakin sarki daya bani ikon rubuta wannan littafi..Allah yasa yanda na fara a sa'a nagama a lafiya_

GAISUWA

    _Gaisuwa ta mussaman zuwa ga IYAYEN NA da kuma yan uwana inna musu fatan alheri duniya da lahira..Haka zalika gaisu ga masoyana kuma inna muku fatan alheri_

Littafin Marubuciyr

_Bayan wuya_
_Denishra_
_Sanadin camera_
_Nida sojana_
_Yan biyu ne_
_yan ajiye shida_
_Yar gata_
_Ashe kishiyatace_
_Rikicin Babban gida_
_*Akan So*_

TUKWICI

    _Wannan Littafin tukwici ne gareka Ibrahim Luv(😍) Nagode sosai Allah ya bar kauna_

GARGADI'

      Banyarda kowa ya juyamin labarina ba ko amin editing dinsa ba kuma banyarda asamun littafina a doc. ba innagama zansa dakaina👌

TSOKACI

     _Wannan labarin qagaggene banyi sa domin kowa ba sauran nishadantar,fadakar da mosoyana banyi shi dan wani ko wata ba..dan Allah dik wa da Allah yasa lbrn yazo daya da shi toh ya ma Afreen Afuwa_

  
     *Shout out to all mu fans*💋

        Book 1

        *🍡1-5*


🍇🍓Zaune Fatimah take kan kujerar dake palon su 1 seater tana kallon film Ibrahim na  zaune kan 2seater din dake kallon kujerar da fatimah ke zaune..Haka ma mama da Ummy da hanifa suna zaune dik kallon film din suke harda dan autansu Nasir dake kusa da mama film din series suke kallo (Twist of faith)..

    Ibrahim da fatimah ko hankalinsu kadan ne kekan kallon da akeyi suna Satan kallon junansu

   "Anty faty kalla Pragya ta gane su tanu fa"

  Acewar Ummy

   Eh kawai fatimah tace mata..Harar junansu kawai sukeyi suna kallon...

    Misalin Karfe goma baba yashigo da sallama dik gaidasa sukayi baba ya kalli Ibrahim yana fadin

    "Ibrahim har ynxu kanan Ashe"

    "Eh baba amma nakusa tafiya"

  "Toh madallah"
Acewar baba

    Shigewa baba yayi dakinsa Mama tamiqe zata bisa Ibrahim yasoma fadin

    "Mama nixan wuce saidai safe"

    Amsawa tayi da

   "toh ka agaidamin da umman taka sai goben inji dai ka qoshi ko?"

   Eh ya amsa dashi yana kallon fatimah da gefen ido yana murmushi

     Sallama sukayi da mama ta nufi kitchen ta debo ma baba kayan Abincin sa kafin tashige..

   Miqewa ibrahim yayi yana cema su ummy da hanifa da Nasir seda safe Nasir ne ya ruqo hanunsa yana fadin

   "Seda safe ya ibrahim ka kawomin sweet gobe"

   Toh yace Nasir ya miqe da gudu yabi bayan mum..

AKAN SO (1)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora