Shimfida

5.8K 517 168
                                    

Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'adunmu. Rashin aure kan haifar da damuwa a zukatan iyaye da su kan su ya'yan amma kamar yanda addini ya koyar da mu cewa "Komai da lokacin sa" shi ma auren ya shiga sahun "komai" ɗin.

Gaggawa da kwallafa ran akan sai anyi aure ya sa da yawa daga cikin jinsinmu yin KUSKUREN da har su mutu suna nadamar sa.

Jinkiri kan sa mutane su rasa tauhidinsu na duk abin da zai faru a doron kasa ya kan faru ne a bisa ga ikon Allah, in bai so ba hakan ba zai faru ba, kuma komai rubutacce ne, kuma alkaluma sun bushe. Sai su zama su na takurawa wanda aurensu ya zo da jinkiri da kalaman "Yaushe za ki yi aure?" ko kuma "Kin ki aure ko" abin tambaya ga duk wanda ya ke ɗaukan aure a wani hanyar nuna Darajan mutum shi ne "mai ya hana musu mutuwa" don kuwa aure, haihuwa da mutuwa lokutansu rantsattse ne.

Babu abin takaici kamar a ce mace don ba ta yi aure ba, sai ma su kiran ta ki aure su zagayo suna neman ta da lalata don a ganinsu tun da ta ki aure toh mazinaciya ce. Wacce gaggawa ya dibe ta sai ta ba da kai bori ya hau don a tunanin ta hakan zai sa su aureta.

Wasu daga cikin kawayensu kuma kan ɗauki rashin aure dalilin yanke zumunci da su, saboda a ganinsu babu kaskanci kamar rashin aure ko da kuwa auren da za'a rike zai kai su ga wuta ne ba Aljannar da kowa ke yin aure don nemansa ba.

Tsabagen son aure ya sa tun yarinya na kwailar ta ake dasa mata ra'ayin duk abin da za ta yi don farin cikin wani ɗa namiji ne ba wai don kanta ko farin cikin mahallicinta ba. Sai ka ga don yarinya ta ci kwalliya ba za'a nuna mata tayi kyau don ta ji daɗi ba sai dai a nuna mata tayi kyau za ta burge wani ɗa namiji. A haka za ta taso in ba'a taki sa'a ba sai ta kai ga siyar da mutuncin ta duk don ta birge namiji.

Aure ibada ce, sunna ce mai girma amma kuma rashin sa bai rage komai na daga Darajan bawa a idon mahallicinsa, matukar mutum zai tsare kansa daga kowanne nau'i na zina, zai kasance abin so a wajen Allah har zuwa lokacin aurensa, anan Allah zai saka masa da abokin rayuwa nagari wanda zai sa a manta da kuncin jinkiri, in kuma bai da rabo zai samu babban rabo ranar gobe kiyama.

Babu jinkirin da ba Alkhairi ba, matukar an yi hakuri, in kuwa ba'a yi ba tsaf ze zama azaba...

***

Zaune take a ofishin ta na sashin kere-keren magudanar ruwa ( water resources engineering department) a bangaren kere-kere (faculty of engineering) da ke jami'ar kimiyya da fasaha ta Safiyyah Jibril  (Safiyyah jibril University of science and technology) da ke daular Qahɗanie.  

Kacokan hankalin ta na  kan  zanen Dam ɗin da jami'ar ke shirin kaddamarwa wanda musamman aka zaɓe ta cikin ma'aikatan wannan sashi na su don ta zana ta gabatar ma shugabannin makarantar don a samu a sa shi cikin kasafin shekara mai zuwa.

"Miss Fatima ki ɗauki abin sannu a hankali mana, ke ba miji ba balle a ce zai hutar miki da gajiya a gaba" faɗin wani magidanci wanda kallo ɗaya zaka masa ka san in bai yi jika da wacce ya kira da Miss Fatima ba toh tabbas zai haife ta. Aikinta ta dukufa ta cigaba da yi ba tare da ta dago kai ta kalle shi ba.

" Ankara ɗin nan ya fito da ke, kin ga yanda kwalliyar ki ke gayyata na zuwa gare ki, don Allah ki aminta da ni zan shayar da ke daɗin da ba ki taɓa tsammani ba, sannan hakan ne zai kara min mararin aurenki, wallahi ina son ki" Ya sake faɗi yana mai kai fuskansa saitin nata fuskan har suna shakan numfashin junansu.

"Au'uzu Billahi Minka" Ta ce tana mai mikewa

"Zan ba ka mamaki Prof. Ka bar ganin kai ne shugaban ɓangaren nan (Dean) Wallahi zan maka abin da ba ka taɓa zato ba, Banza tsohon Bunsuru" Ta ce tana ficewa da ga ofishin sanin da ta yi kofar jam lock ne.

"Ai ko da karfin tsiya sai na sha romonki, Ace yarinya se shegen fuska biyu, mace za ta kai shekarun ta ne ba tare da neman namiji ba, duk kuɗin da na ba ta ba zai tashi a banza ba" Ya fadi yana buga kofar da karfi.

Da kyar ta iya jan kanta zuwa gidansu da ke unguwar da ake kira Madina saboda kasancewar sa sabuwar anguwa da ya kunshi sabbin gine-gine da abubuwan kawata waje. Ba kowane dan Qahɗanie ke mallakan gida a wajen ba sai wane da wance musamman yan jinin sarauta da hamshakan yan kasuwa kamar Mahaifin Fatima Alhaji Bello Yahuza.

***

Daular Qahɗanie na tsakanin Kasar Nijeriya da Ghana  masarauta ce da fataken Larabawa su ka kafa yayin da su ke yaɗa zango in za su je kasuwanci a wannan yankin. Sannu a hankali sai ya zama duk wani wanda ya ratsa daga yankunan Sahara da arewacin Nigeria a nan su ke yada zango har sai da  zuwan wasu ayarin Karauka karkashin shugabancin Madugu Imam Jibril da ya ke yawon yaɗa musulunci a shekara na ɗari uku da hamsin bayan Hijira. 

Tun da ya yaɗa zango ya ga wajen sai ya yi ra'ayin kafa daular musulunci a wajen. Ba tare da ɓata lokaci ba yayi Shawara da ayarin sa nan su wasu su ka aminta da haka, yayin da wasu su ka ki  amincewa. Cikin shekara ɗaya aka kafa daular sannan su ka sanya masa suna Qahɗanie kasancewar su Larabawa. Sun ɗauko iyalansu sannan sun bar kofa a buɗe ga duk wani mai bukatar zama a daulan bisa ga amana. 

Kafin a ankara Hausawa sun rinjayi Larabawa masu zaman wajen saboda kasancewar sun fi Larabawa kusa da nan. A lokacin mulkin Imam Abdulhamid  Bn Jibril watau shekara ashirin bayan kafa daular ne aka fara auratayya tsakanin Hausawa da Larabawa a daular Qahɗanie, sannan a shekaran ne aka kafa makarantun boko a daulan wanda fa taimakon yayar Imam Abdulhamid Safiyyah bnt Jibril ne aka kafa su. 

Tun daga nan aka fara samun cigaba ta fuskan kimiyya da fasaha, har ma da shari'a sannan akwai yalwan ilimin addini a daulan. Bayan tsawon shekarun daulan sannu a hankali Al'adun Larabawa ya gushe da ga jikin su, yaren su da Al'adun su ya zama na Hausawa amma duk da haka ba za'a ce sak na Hausawa ne ba kamar yan Nijeriya, Cameron da Nijar da Chadi da sauransu ba... 

How do you see our shimfiɗa

How do you see our main protagonist? 

Others are yet to come

Get set for twined twists, all you have to do is to invite extra patience coz more update may b after my exams Insha'Allah. But if am opportuned I will publish one or two Insha'Allah

Invite ur family and friends,family of friends, friends of the family, friends of friends, friends of friends of friends, friends of family of friends. 

I love you and I will forever do

Vote, comment and share please  

BA GIRIN-GIRIN BA Where stories live. Discover now