21 : CETO

1.2K 215 113
                                    

shamuSYY accept my condolence please, Allah jikan ummah ya sada ta da rahma. Sisters pls pray for her mum.

Ku kara hakuri da er boko, kuma zance na Allah am a lazy type, ga abubuwa da dama a gaba na. Ur prayers needed.

😍😘😘😘😘😘

Ganin yanda ɗakin ke tsare ya so ya ba shi tsoro, jikin wani lungu ya maqale a tsorace. 

'Kasan ba'a banza na ɗora ka akan karati da tokwando ba sai don ka san yanda zaka kwaci kanka, kuma musamman daga Kasar China na hayo su toh kar ka bani kunya ko a bayan ido na, ko bayan kasa ya rufe ido na' kalaman don Clemenza ya faɗo masa a rai take wasu kwarin guiwa da bai san da su ba suka taso masa tun daga tafin kafarsa. Hakan ya sa ya tuna da ajiyar da ke jikin wondonsa na ciki. Rabuwarsa da direban taxi ya saka ta a wandon kafin ya ajiye sauran kayansu a wani kogon bishiya.

Bindiga ce, Don ya masa kyautar sa da zai baro, tana iya harbin abin da ke da tsawon mile ɗari in dai an seta shi da kyau. Sannan ba ta da kara, tana ɗaukan harsashi sannan tana ɗaukan nakiya duka biyu Don ya cika masa shi ya ce iya taimakon da zai iya masa yanzu kenan.

'Ka san mafi yawan yan ta'adda bindiga kawai ce karfin su, ba su da karfin yin faɗa da jikkunan su, saboda haka a duk sanda ka haɗu da su nema hanyar raba su da bindigogin su Shike nan ka ci nasara matakin farko a kansu' cewar yogn Chen mai koyar da shi karate. Yana tuna hakan ya daidaita bindigar sa ga mutanen da ke zaune a bakin kofar kowannensu ya sakar musu harsashi, kafin su ankare da zuwan halsashin kowannensu ya samu isowar nashi cikin kirji. Tim su ka faɗi nan sauran da ke tsaye a gefe su ka yi sauri don barin wajen domin kuwa labarin shocking din Adjetey ya is ko su, a wata majiyar ma cewa ake ya suma an fice da shi daga fada don samun magani.

"Aljanu ne a fadan, ka san mu a kasarmu aljanu na taimakawa masarauta" cewar ɗaya daga cikinsu da ya fito daga yankin arewacin Nijeriya, ta yana gizo ya hadu da wani dan ismaalie a hankali daga abota su ka janye shi zuwa ga ta'addanci. 

Kalamansa ya sa da yawansu tsorata, har su ka juya sai wasu karfafa daga yankin Kasar ibo sa su ka ɗauki aniyar ganin wannan aljani. AbdulHaleem na ganin tahowarsu ya sake sakin harsashi  wanda bai sauka a ko ina ba sai cikin cikin ɗaya da ga ciki, take ya sheme a kasa. Dayan na ganin haka ya tsaya cak, ya gudu ko ya tsaya. Hakan ya sa AbdulHaleem fitowa ya dunkare shi ba tare da tsoro ko shakka ba. 

Daga idon da yayi ya ga AbdulHaleem take zawo ya nemi kucce masa, don kuwa tabbas wannan ne hoton da ke zagaye da falon Alhamzie da sunan ɗan sarki da su ka kashe, kenan Aljanun ma Fatalwa ne, bai dawo daga duniyar tunani ba yaji saukar naushi a fuskar sa don sai da kumatun ya lotse, wani sabon naushin ne ya sauka nan ya fara kuka wiwiwiw faɗi yake

"ka yi min rai in fita, ba zan sake dawowa ba" karamar wukar da Mr Chen ya bashi ya zaro daga in da ya aje ya so ka ma mutumin a cinya. Wukar na shiga cinyar sa yana sakin ihu, hakan ya sa AbdulHaleem ya sakar masa kuma. Faɗin da yayi yana gurnanin azaba, AbdulHaleem ya dunfari ɗakin, buɗewa ke da wuya ya iske yan ta'adda uku suna mashaa da wasu tsofaffi, ma'aikata a fada. Take ya tsorata kada Ace mutanen nan sun yi da iyayensa.

"Kai ma dauki ɗaya, yanzu muka fara don mu sha romon dukkansu kafin a tada mu" daya ya faɗi ba tare da ya juyo ba ganin  irin tsorata da matan su ka yi ganin AbdulHaleem. 

Bindigogin da su ka ajiye ya kwashe ya damka ma mahaifiyarsa kana ya jawo mai maganar cikinsu ya daɓa masa wuka a mazakutarsa, ya yasar da shi gefe. 

Sauran ba su ankara ba sai da yayi ma na biyun wanda shi sakin ihu yayi da ya ji azaban. Ba kamar na farko ba da ya kasa motsi saboda tsananin azaba. Ihun na biyun ya sa na uku tashi a firgice yana lalubo bindigar sa ganin babu ya Mike yana mazurai.

"wanene kai, don kazan kazan ka har zaka shigo nan, ka kawo kanka ajalinka" yace yana fiffiga kamar zai iya wani abin. Isa gareshi AbdulHaleem yayi bai masa wani gargadi ba ya soka masa wukar a cinya, azaban da ya ji ya sa ya nemi guduwa amma kafan ya hana hakan ya sa ya janye jiki gefe. Bin sa yayi ya masa abin da yayi ma sauran nan shi ma ya bi saura wajen jin azaba da zubar jini.

Sake waya yayi zuwa hedkwatar sojin Qahɗaanie inda aka tabbatar masa da zuwan jirgi mai saukar angulu a inda ya bada umurni. Nan ya jagora ci matan da ke ɗakin zuwa kofar yamma in da jirgi ke jiran su. Sai da ya tabbatar da tashin su sannan yayi yunkurin komawa don ya fuskanci sauran da ke gaban gidan. 

'malam ga matar ka ga ya'ya kada ka yi yunkurin raba su da gatansu' wani sashi na zuciyar sa ya ankarar da shi amma ya cije ya dage.  Saman gini ya nufa, yana tafe yana Hasbunallahu wa ni'imal wakeel don ya san bai da wani gata sai na mai duka. Ko da ya isa nan ya samu an ajiye na'urar harsashi da in aka saki zai yi kaca-kaca da wanda aka harbawa. 

"Duk wanda baya fatan mahaifiyarsa ta yi sabon naquda ya sallama kansa, masarauta za ta yanta shi cike da kyatuttuka da aikin yi" ya faɗi ta lasifika din da ke makale da wannan tankin. Wasu maballai ya latsa take harsashi ya sauka a kan wasu yan ta'adda ya na kallon yanda su ka tarwatse. Babu shiri su ka fara gudu don tsira da ransu suna hayewa kan hillux hillux din da ke harabar wajen suna guduwa. Ganin haka ya sa AbdulHaleem ya sake sakin harsashi nan wasu suka kara zubewa, don burin sa ya rage yawan yan ta'addan. 

'ina mai martaba' shine tambayar da ta hana masa latsa botirin a karo na bakwai nan ya juya da sauri zuwa ga hanyar da zai sada shi ga cikin majalisa 

BA GIRIN-GIRIN BA Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon