page 16-18

3.4K 92 3
                                    

[11/14, 2:57 PM] Real Afreen ce💋: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀
      🎀🎀🎀🎀
            🎈🎈
               🎈
*MIJIN YARINYA*
               🎈
            🎈🎈
      🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*2nd* November 2017©

       
     *16*

🎀🎈Washe gari suka shirya zuwa gombe tinda sasassafe suka dau...

   "Innah kiyi hakuri ki bamu Ummi "

    "Dannan bawai naqi bane..yaronan naku bason ummi yake ba shi meyasa bezo biko ba?se Ku"

    "Bashi da lafiya ne" acewar dad shiru inna tayi tana fadin ynxu ya kakeso ayi?

    "Inna Aron ummi za'a bamu tazauna da irfan tadinga taimakawa ya tuno abubuwan sa na baya"

   Tabe baki innah tayi daga bisani tace su bari ummi ta fitoh daga wanka...

   Ba'afi yan mintina ba ta fitoh sadda ta gama shiryawa kafin ta fitoh ta same su gabadayansu kallonta sukayi dantadan rame cike sa fara'a ta gaisasu suka amsa..

    "Watoh ummi kin taho kin barni ko dama guduwa kikayi"

    Acewar mum dariya ummi tayi

    "A'ah ai zan dawo mum kodan makaranta"

    Murmushi mum tayi tana fadin aiseki shirya mu tafi"

    Innah ce tasoma fadin

    "Kunce yau zaku koma kumata bayanin abinda ke tafe daku"

   Gaban ummi  ne ya fadi ta kalli mum tana fadin.
 
    "Mum meyafaru"

  Mum din ma kallon dad tayi kafin yayi gyaran murya yana fadin

    "Ummi dan Alfarma mukazo nema agunki dik da mun San abinda irfan ya miki be kyauta ba"

   Gaban ummi ne ya fadi kanta na qasa kunyar dad takeji amma bataso takoma

   saboda irfan ba taso karatunta ne ze maidata...

     "Ummi kiyi hakuri nasan ynxu bakyason irfan ba aurensa zakayi ba zama kawai zakiyi amatsayin matarsa ki taimaka hankalinsa ya dawo kuma maganar karatunki zaki cigaba dayinsa"

    Jimmm ummi tayi tana jin nauyin dad sosai ba yadda ta iya saidai ta amsa da toh   

Dadi sosai dad yaji..innah kuwa bata so hakan ba mum ma bataso ba..

    "Jeki tayata hada kayan mu tafi"

   Dad ya fada yana kallon mum..innah da mum ne suka miqe suka bita daki dad ko godiya ya dinga ma innah ya fice daga bisani...

     "Idan kikaje so nake ki juyamin shi ba yana miki kallon yarinya ba..ki basa wahala kuma kisani ke ba matarsa bace ynxu"

   Acewar mum..innah ma qarawa tayi da..

   "Umimi ta ki qoda min shi yadda ze gane shayi ba ruwa bane"

   Itadai ummi gyada musu kai kawai takeyi..suna gama hada kayan suka kama hanya...

     Dad ko qin yarda yayi mum ta wuce da ummi gida sedai amaidata gun irfan din har seya warware tukun na...

    Ba yadda mum ta iya saidai ta yarda..shiko dad burinsa kawai in ummi ta koma yasan yadda za'ati sa sake musu sabon daurin aure...

      Suna isa gida da sallamarsu khaleesat na zaune tana ganin su ta washare haqora tana musu sannu da zuwa dad ne kawai ya amsa mata mum ko aranta tana fadin

MIJIN YARINYAWhere stories live. Discover now