page 19-45

4.8K 95 2
                                    

[11/16, 7:56 PM] Faty Afreen🌷: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀
      🎀🎀🎀🎀
            🎈🎈
               🎈
*MIJIN YARINYA*
               🎈
            🎈🎈
      🎀🎀🎀🎀
🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*2nd* November 2017©

       
     *19*

🎀🎈"Sannu da zuwa cewar khaleesat "

     Amsawa irfan yayi batare daya kalleta ba fuskarsa cike da fara'a ya shiga daki khaleesat tabi bayansa...

     Kaya kawai ya cire suka fitoh Palo dinning suka nufa suka zauna khaleesat tasa masa abincin...

     Yakai cokali daya kenan ummi ta fitoh daga kitchen dauke da plate din soyayyan dankali da juice a hanunta ..tafiya take tana canja salon tafiyar tata binta da kallo irfan yayi...

   "Ummi ba magana ne?"

   "Ohhh banmasan kadawo ba sannu da zuwa"

    Yauwa yace yakaracin abincin harar juna kawai sukeyi ita da khaleesat..Zama ummi tayi tana cin abincin ta..

   "Ummi ba tayi ne?"

     Juyowa ummi tayi sanda ta tabbatar khaleesat na kallonsu tukun na tayi qasa da muryar tana  fadin

    "Kazo kaci ai har dakai na fada ma"

    Murmushi yayi ya miqe

   "Baby baka cinye abincin bafa"

    Bece da khaleesat komai ba ya juya nufi gun ummi sanda ya zauna tukunna ummi ta kalli khaleesat da gefen ido tana murmushin mugunta..

    "Ko na baka abaki ne?"

     Eh ya cemata dan haka ta dibo ta basa abaki rufe ido yayi yana fadin

    "Wow dadi"

    Juya wa tayi tana kallon khaleesat...wacce ta buga tsaki ta miqe ta nufi daki irfan ma ya bata da kallo sanda ta shige tukun irfan ya juyo ya kalli ummi

    "Ummi meyasa kike gudu na bakyason kulani?bakya kula dani?"

   Dagowa ummi tayi ta kallesa gabadaya yasa jikinta yayi sanyi..miqewa tayi zata bar wurin ya riqo hanunta..

    "Meyasa zaki tafi ki tsaya ki fadamin"

    Shiru tayi daga bisani tasoma fadin
.  

    "Kasakeni"

   Saketa yayi ta shige daki shiko ya dauki indomie din ya cigaba da ci yana murmushi shikadai...

    Itako shiga tayi daki tadinga kuka..magana da irfan sa jikinta yake yayi sanyi ji take sabon son shi na shigarta ji take kamar bazata iya rama abinda yayi mata ba ga kishin khaleesat da kullun qaruwa yake dik da tasan cewar ynxu khaleesat itace matar irfan amma bazata iya jurewa ba...

    Tana kukan ne har bacci ya dauketa

*Washe gari*

 
     "Abba ummi bata son min magana gudu nama takeyi bansan meyasa ba"

   Acewar irfan dake zaune kusa da dad shiru dad yaya daga bisani ya soma fadin..

   "Kayi hakuri irfan kaje ka bata hakuri Ku shirya shine kawai"

    "Toh dad ni zan wuce gida"

   "Toh Agaidamin dasu Allah ya muku albarka ya qara hada kanku"

MIJIN YARINYAWhere stories live. Discover now