30

7.6K 718 263
                                    

Zuciyarshi na dokawa ya shiga gida. Ateefa ya gani ta fito daga hanyar kitchen. Dan ware idanuwa yayi yana kallon ta.

"Ba aiki nayi ba. Na shiga na duba ne kawai. Ko shima an hana?"

Ta bukata tana tsare shi da idanuwan ta. Kunyarta yake ji. Kunyar abinda yai mata yake ji. Girgiza mata kai yayi yana rasa ta inda zai fara magana.

Ganin tayi tsaye yasa shi takawa ya karasa inda take tsaye. Idanuwan ta sun kumbura sun canza kala. Wani abu yai tsaye a zuciyarshi yana mishi ciwo, bai sake jin daci a makoshin shi ba saida yaga yatsun shi kwance a kan kuncin ta.

Kallonshi take tana ganin yanda marin a fuskarta yake amman shi yake nuna yana jin ciwon abin, dakyar ya iya daga hannunshi yakai wajen yana shafawa da yatsun shi.

Yana ganin yanda ta runtsa idanuwanta da alamar zafin hakan take ji. Matsawa ya sake yi sosai, iskar bakinshi da taji yana hura mata a wajen ne yasata bude idanuwanta.

Kaman zaiyi kuka yace.

"Kiyi hakuri Tee... Inda zan koma baya in goge danayi. Banda kirki nasani... Ban kyauta ba... Kunyarki nake ji wallahi. Dan Allah kiyi hakuri..."

Ya karasa maganar yana tsugunnawa da shirin kai gwiwarshi kasa. Da sauri ateefa ta rigashi kaiwa tana fadin.

"Me kakeyi haka? Dan Allah ka tashi...!"

Girgiza mata kai yayi yana karasa kaiwa kan gwiwoyin shi hadi da sadda kanshi kasa. Ko a addini ba'a ce ya daga hannunshi akan ta ba dan ta fada mishi maganganun da sukai mishi zafi.

Laifine babba daba a wajenta kawai ya tsaya ba, ba ita kadai ya taba ba harda addininshi.

"Dan Allah ka tashi..."

Ateefa ta fadi tana dora hannuwanta kan damtsen nashi hannuwan tana kokarin mikar dashi. Ko motsi baiyi ba.

"Zan tashi inkin hakura... In kince kin yafemun..."

"Na hakura... Na yafe maka"

Ta fadi da sauri, dagowa yayi yana nazarin fuskarta kamun yace

"Ban yarda ba..."

Tsayawa tayi tana kallonshi, gabaki daya yasa ta jin kunyar itama. Labeeb ne a kan gwiwarshi yana bata hakuri bayan itama ta mishi laifi. Matsawa tayi sosai batare data tashi ba tana tallabar fuskar shi cikin hannuwanta.

Sumbatar shi tayi abinda tun kamun rigimarsu rabonta dayi. Sannan ta janye fuskarta.

"Na hakura..."

Sauke numfashi yayi yana dandana man lebenta dake kan nashi labban kamun ya mike yana rankwafowa ya kamata ya mikar, janta yai jikinshi yana rungumeta.

Sosai ta zagaya hannuwanta a kugunshi tana rike shi sosai itama.

"Kayi hakuri... Na fadi abinda bai kamata ba... Ina tsoron rasaka... Bazan iya rasaka ba El-labeeb. Dan Allah karka barni..."

Ta karasa muryarta na rawa saboda kukan da ta soma. Kara riketa yayi yana rocking dinsu a hankali.

"Shhhh... Wayace miki zan iya barinki? Waya fada miki zaki rasani? Daga randa na sauke idanuwana akanki nasan bazan iya barinki kije ko ina ba Tee. Ina sonki sosai... Kar wani abu yasa ki kokwanto kana haka..."

Labeeb ya fadi yana kamo hannunta daya dake kan kugunshi hadi da turashi ta tsakanin su zuwa kan kirjinshi inda zuciyarshi ke bugawa kaman zata fito.

"Kiji me take cewa in maganganuna basa miki tasiri... Kiji yanda zuciyata take bugawa akan hannunki..."

Shiru ateefa tayi tana maida numfashi, tayi luf a jikinshi. Sonshi na kara rufe ta. Sun jima a haka kamun ya dago ta daga jikinshi yana jan hannunta suka karasa cikin falon suka zauna kan kujera suna fuskantar juna.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now