Prologue

8K 403 77
                                    

®
📖✏
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

Na sha dauka mahaifiyar kowa haka take kamun inyi hankali, sai daga baya na fahimci ni kadai nai rashin sa'a. Na sha fatan in kwanta bacci in tashi a gidan da ba nan ba, har sai da na fahimci ba komai rubutun ALKALMIN KADDARA yake iya canzuwa ba. Ta wani fannin yau burinki ya cika...ta wani fannin ke da kanki kinyi nasara wajen wargaza burin naki..."

Muryar Tasneem ta sarqe saboda sabon kukan dake shirin kwace mata.

"Tsakanin yau zuwa gobe idan aurena ya mutu kece...Idan mutuwar shi bata faru a daren yau zuwa safiyar gobe ba, makomar shi kece sila. Abba bazai yafe miki ba Umma, kaman yanda nima bazan yafe miki ba..."

"Tasneem..."

Bara'atu ta fara muryarta da duk jikinta na kyarma, maganganun Tasneem din na zauna mata a wajajen da bata san da su ba. Girgiza mata kai Tasneem take hawaye na zubar mata.

"Bana son jin komai...lokacin da na sha jiran jin kalamanki ko bayanin ki ya wuce umma. Bazan roqi komai daga gareki akan su Hamna ba...Zan tuna miki mu duka Amana ne a wajenki... Idan baki dubi Allah ba bansan me yasa kalamaina zasu canza komai ba..."

Tana karasa maganar ta sa hannu taja mayafin da ta dage lokacin da aka shigo da ita daga dakin, tana rufe fuskarta dashi lokacin da hawaye masu dumi suka zubo mata. Dan ko zama batai ba daman, wani irin zafi kirjinta yake mata yau wajen wata biyu kenan, tari Tasneem ta soma ba kakkautawa da yasa Bara'atu da sai lokacin ta samu motsi tashi da sauri ta karasa wajenta tana kamata hadi da daga mayafin dake rufe da fuskarta.

Hannuwan da Tasneem ta sa ta rufe bakinta ta dawo dasu dubanta jin lema a jikinsu, har lokacin tarin da take bai tsagaita mata ba, tsilli-tsillin jini tagani a jikin tafukan hannunta.

"Tasneem tarin jini kike..."

Bara'atu ta fada hankalinta a tashe, zame jikinta Tasneem tayi daga riqon da tai mata tana nufar hanyar kofa, dan tarin ya fara tsagaita mata. Sai dai kirjinta da yake kaman ana hura mata wuta, har numfashinta sama-sama yake saboda azaba...!

**

Ko ina na jikin ta kyarma yake, musamman zuciyarta da take dokawa har cikin kunnuwanta, kallon shi take da bayanannen tsoro a kan fuskarta. Gam yaja kofa yana kulle zuciyarshi da duk wani emotions dazai iya samun fitowa, fuskarshi babu komai akai ya sauke idanuwan shi cikin nata

"Ni da ke bamu taba wuce wani abu da ya girmi nisha di ba, bansan me nayi daya saki tunanin ko zuciyata kin isa ki hango ba balle ki samu waje a ciki, bakuma zan baki hakuri ba dan babu kuskuren da nayi, banyi komai da babu amincewar ki ba..."

Hannu Fadila ta sa tana dafe cikin ta da yake yamutsawa da sabon tashin hankali. Inalillahi wa ina ilaihi raji'un take son furtawa amman kaman an kulle mata baki, sai lokacin nauyin komai yake danne ta, abin da yake tsaye a wuyanta take son hadiyewa amman ta kasa, sau uku tana bude bakinta da niyyar magana amman babu abinda yake fitowa. Numfashi take ja ta bakinta tana fitar dashi a wahalce.

"Nawfal???"

Ta kira sunan shi cike da shakku da alamun tambayoyi da dama, muryarta can kasa, idanuwanta na kasa yarda shine tsaye a gabanta. Zuciyarta na qin aminta da abinda kunnuwanta suka ji. Nawfal bazai mata haka ba, ba zuciyarshi kawai ta iya hangowa ba, tana da yaqinin har cikinta ta shiga ta samu wajen zama.

Ganin yanayin dake fuskarta yasa Nawfal kama hannunta yana janta, mamaki ya hanata yin komai banda binshi, har yakai ta bakin kofa ya hankada ta, badon bangon da ta dafa ba, babu abinda zai hanata mummunar faduwa.

"Ko meye kike tunanin yake tsakanin mu ya zama tarihi a yau!!!"

Bakin shi kawai take ganin yana motsi, kunnuwanta sun daina jin sauran kalaman, tashin hankalin da take ciki da maganganun shi na farko sun sa komai tsaya mata cik. Girman kuskuren yarda dashi na danne ta...!!

**

Hannun shi Tariq yake kokarin kwacewa yana juyawa hadi da kallon gidan, hawaye masu dumi na zubo mishi. Sakin hannun shi Ashfaq yayi yana tallabar fuskar shi ya juyo dashi.

"Ba mu da dalilin juyawa baya Tariq, babu abinda ya rage mana, komai ya kare, ni da kai ne kawai..."

"Ta ina zamu fara? Ina zamu je? Yaya haka rayuwa take da wahala?"

Tariq ya karasa wasu sabbin hawayen na zubo mishi, da ganin su kesa zuciyar Ashfaq wani irin ciwo marar misaltuwa. Fuskar Tariq din ya tallaba da dukkan hannayen shi, a zuciyarshi ya fara jin zaman kalaman kamun ya fito dasu.

"Ban sani ba nima...babu abinda yake da tabbas, na so labarin rashin tabbacin rayuwa kawai zan baka Tariq, bawai ka tsinci kanka a cikin shi ba, zuciyar dake bugawa a kirjina kanta babu tabbacin zata kai anjima, abu daya na sani a wannan matakin, da duk numfashin da zan fitar daga yanzun zuwa na karshe zan tabbatar ko yayane taka rayuwar akwai sauqi a cikinta...zan tabbatar hawayen ka sun zuba ne badan kunci na rayuwa ba. Kana jina? Baka bukatar kowa in ina nan..."

Idanuwan shi Tariq ya kalla, a cikin su yana ganin gaskiyar alkawarin da Ashfaq yai mishi, a cikin su Yana ganin rubutun ALKALMIN KADDARAr su da yaren da yafi karfin fahimtarshi...!

*

Bazan saka muku rana ba, saboda ikon komai ba a hannuna yake ba, ba da jimawa ba complete PART 1 zai zo muku a OKADABOOKS In shaa Allah. Bazan ce ba zakuyi dana sanin saka kudin ku ku siya ba, saboda bashi bane zai zama labari mafi sarqaqiya da darussa da zakuci karo dashi ba, kaman yanda ba lallai ya samu karbuwa a wajen wasu ba, rubutuna baifi na kowa ba, sai dai daban yake da na kowa.

GET YOUR OKADABOOKS application on play store and sign up.

Allah ya bamu aron lafiya da rai cikin rayuwa mai amfani da inganci, ya karbi rayuwakan mu cikin Aminci. Amin thumma amin. Ina kaunarku saboda Allah. ♥♥♥

#TeamAK
#AnaTare
#VOI
#FWA

ALKALAMIN KADDARA. Where stories live. Discover now