BISMILLAHI RAHMANIRRAHIM
💔
Zauna yake ya rike kansa da yake sara masa kamar zai fashe saboda wani zafi da yake ji daga kan sa har cikin kirjinsa.
Yama rasa wana irin tunani zaiyi ga rashin matarsa dan har yanzu bai daina jin mutuwar ta ba kusan wata uku kenan ta tafi ta bar masa twins din da ta haifa, ta rasu a wajan haihuwarsu , yanzu kuma ace yayi aure kuma a rasa wacce za a ce ya aura sai .....Kasa Kiran sunanta yayi yadda yaji kamar an buga masa guduma dan sauke nunfashinsa yayi tare da kwanta wa akan gadon da yake zaune a dakinsa ya rintse idonsa .
Jiyayi ya tsani kansa dan gani yake Shi ya jawo rasuwata dan bai mata at adalci ba, he look at himself as a selfish man ,
" oh Allah forgive me , I never wish this to happen , pls forgive me..."
Wani zafi kirjinsa yake masa zai so ace ko hawaye ne ya zubo masa ko zai samu saukin abun da yakeji a kirjinsa.**********
Kuka take sosai har jikinta na rawa kamar ranta zai fita .shike nan ta rasa yaruwarta bazata sake ganinta ba , ta yadda da zancan bahaushe da yake cewa mutuwa mai raba da da mahaifi , masoyi, d'anuwa , amini yau kam tagani akanta ,mutuwar ta dauki wani part na rayuwarta dan tasan tayi rashin yar'uwa da bazata ta ba samun wani da zai to she mata idan ta rasa ba amma tasan lokacin tane yazo kuma duk mai rai mamaci ne kowa lokacin sa yake jira.
Amma ta rasa me yasa ba a sabo da ita . Ta daga kanta tana goge hawayen da yaki tsayawa ta kalli twins din da ta bari wani kukan ne ya sake kubuce mata. Suma yanzu sun zama marayu sun rasa mahaifiyarsu.Wani abune yazo ya tsaya mata a wuya data kasa hadiyeshi tana nunfashi taji shima kamar an rike mata Shi dafe kirjinta yi tana kokarin abunda ya tsaya ya sauka amma ina kuma shaketa yake ta sake wani irin kuka ta fara innanillahi....... can taji ta hadiyeshi, ta kwanta a wajan tana sauke nunfashi a hankali tare da gaggarowar wani hawayen .
Tasan bata yiwa yaran nan adalcin rabasu da mahaifiyarsu ba " me yasa batayi hakuri ta zauna a inda take ba komai zai sameta da yafi ye mata abunda yake shirin faruwa da ita.
Taya zata kalli yaruwarta lokacin da itama lokacin yazo, tace ta auri mijin da take so, ta zama me son kanta kenan da wani ido zata iya kalleta "
Kuka take yi mai ratsa zuciya " ki yafe min twin wallahi nafison ganinki a gaba na da wannan auran ,Ya Arabi na kine ke ka dai pls don't miss understand me I never wish this to happen ".